← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 114

Sashe 99

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ham, kak, na fada masa ko na bari ya gani?
11/14/21, 12:54 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
6
Washe gari
Tun karfe bakwai suka nufi asibiti daga masalaci tare da Pah da Hanja
Sun jima a zaune a kusa da ita sunna tofa mata adu'ar neman sauki a wajen Allah
A hankali Pah ke shafa gababn goshinta da ya yi fes da shi a sanyaye yana mai yi mata dadadan kalamai da nunin cewa ta jure, ta daure, kar ta saka, kar ta manta sunna nan , sunna da bukatarta
Hanja kuwa hannunta yake rike da shi mai jone da wata na'urar shima
A sanyaye ya ce" Mah, ganninki a wannan yannayi na kashe dukan kuzarin jikina, Mah yau zan fuskantace ta, ban san yaya zata dauka ba, da ace kina nan ifannuwanki biyu da rai da lafia da kin tare min ita koda ta zo baude min, plz ki motsa ko yayane ta yada zan samu kwarin gwuiwar fuskantarta ki motsa ki nunan kin san ina nan, ki motsa Mah..........."
A hankali Pah ya lumshe idannuwansa cike da tausayin yaron nasa,
Wani tausayinsa ya kara shigarsa na Idan ya ji ta tafi yaya zai dauki abin?
Sai dai baya tunanin karamin rigima zata saka Hanja gane matsala ne bibiyar mata da yake, ba wai a adininsa kadai ba, harta matar da yake so idan mai adini ce zata ji kishinsa
A hankali ya juyar da kansa yana aro dukan jarumtar da yake da ita dan yaki da tausayin yaron nasa da fadawa kansa cewa idan har ya jure ya daure ya kasa falasa kansa a gaban yaron nasa dan taimakon yaron nasa ne ba dan wani abin ba,
A nutsue ya kuma hade lebunnansa da jikin kunnen Mah na dama a sanyaye ya lumshe idannuwansa ya shiga karanta mata surorin alkur'ani dan kara sama mata sukunin zuciya, ya yi imanin idan me take ciki adu'a zata sanyaya mata cutarta
A haka har suka gama ziyartar nata suka fito da zumar sai da rana domin likitocin dake tsaye a kanta sun basu lokutan ganawa da ita idan a ra'ayinsu ne, sai dai kuma ifan sunna son ganninsu wannan kuma ba laifi bane sai su zo su ganta su zauna da ita adadin lokacin da suke so, domin a cewarsu idan ana yiwa mutun magana yana ji a mafarkinsa
A falo Pah ya zauna har lokacin bai ga wulgawar Iman ba, bai san tana wajen mahaifiyarta ta labe cike da tsoron bayanuwar abinda ta aikata wanda ita da kanta ta san cewa fitina ta janyowa kanta da kanta
Kamar yadda ya yi niya, bai iya komawa barci ba , wanka ya dauki lokaci mai tsayi yana yi kafin yake fitowa da wayarsa ya zauna dan shi kam bai san wani irin kaya suka dace ya saka a irin wannan lokacin ba
Abinda bai taba yi bane ya yi ta hanyar tabo number masu shirya su na masarautar ya nemi kan su zame a bangarensa da irin shigar da take iya birge mace mai tsatsauran ra'ayi su taya shi shiryawa
Ai kam hakan ce ta faru, a cikin minti ashirin suka karasa da dukan abubuwan bukatunsu suka zame a bangaren nasa inda ya zauna daga shi sai rigar wanka suka shiga shirya shi ta hanyar sake lumde fatarsa da sinadarensu na shirya mutun, shi kuma ya zauna ya basu hadin kai idannuwansa lumshe yana tunanin ta yaya zai iya da ita ne?
Sun dauki a kadan awa daya a kan shirin Hanja, domin shirin da bai taba tsayawa ya yi bane akai masa, barta da gashin kansa sai da suka caje masa shi suka yi tsaga ta yadda wani ya yi baya kadan ya tsaya sama sama kadan
Suit ruwan baki sidik ne suka gabatar masa , da macheste, da safa fara kal kamar yadda rigar ciki take fara kal, da bakin takalmi kafa ciki, harta da gajeran wando sai da suka hadowa shigar nasa suka hada masa
Nan ya shiga ciki ya saka kayan ya fito , suka hau gyara masa mabalan wuyan rigar da komai cike da yabawa da irin kyan da kayan sukai masa, inda shima da kansa yake yabawar a zuciyarsa
Kampanin Julieta ne suka kawo flowers din da shi da kansa ya bada ordensu aka shigo masa da su rututu dan so yake Pah ya taya shi zabe aka zubewa Pah a gabansa wanda jikinsa ya karra yin sanyi sosai yana kallo cike da tunanin yaya zasu kare da yaron nasa
Kyau kam, Hanja ya yi kyau, ruwan kyau da fuzga ya yi shi, kayan sun amshe shi sosai harma ya yi masu maganar cewa idan har ta amince da maganar daje tafe da shi, lalle zasuna shiryashi kulun
A nan ya bar wayarsa ya sauko yana tambayar idan har darius ya shigo domin shima a yau ya bukaci ganninsa dan ya samu kwarin gwuiwar tunkararta da kalaman da suka dace
Pah ya lumshe idannuwansa bayan kamshin turaran yaron nasa ya fara isowa inda yake yana fatan Allah dora shi kansa kar au raba hali gashi yau mai tsawatar masunma bata nan
A gaban Pah ya ja ya tsaya yana murmushi tare da dan yin alamu irin na ya fada masa ya yi kyau kuwa?
Pah ya saki murmushi yana kallonsa ya furta" Masha Allah, my hero, my son u look lk a
Dan murmushin ya kuma saki yana bada damar Darius ya shigo ya fada masa me yake gani da kalamansa
Pah ya zauna ya karra bada hankalinsa a kansu yana murmushi
Darius cike da farin ciki ya shiga fadin" Duk matan duniya sunna son idan aka tsaya a gabansu a koda kyansu, farinsu, gashinsu, dukiyar da suka malaka da......"
A tausashe Pah yana tatare girarsa na sama ya furta" Plz Darius ka dakatar da abubuwan nan da kake fada domin na tabata idan ya yi kokarin nunawa wadda yake so wannan tabas zata nemi fada da shi ido rufe, bama irin matan da ake sace zuciyarsu ta haka bane, an fada maka kowace mace ce wannan ke rufe mata ido? Wata macen tana sonagana ta gaskiya ne, wata macen du tsakaninta da kai bata so ka yi mata magana irin ra karya"
Hanja ya dubi Pah yana murza agogon hannunsa ya ce" Pah, ban taba jin shakar duban halita na yiwa maganar kamar yadda nake jin na yarinyar nan, me zan ce mata dan ta saurareni?"
Pah ya yi murmushi yana kallonsa ya ce" Ba tsoronta kake yi ba, tsoron amsarta kake ji, bale a irin wannan lokacin ban san yaya zaku kare ba"
Yana kallin Pah ya sauke ajiyar zuciya yana fadin" Nima na kula saboda rashin lafiyar Mah itama sai kuka take bata son damu, ban san yaya zamu karre ba"
Pah ya ari jarumta yana kallonsa da kulawa ya dan watsa hannayensa ya ce" Khadija mama take a wajenta, shi yasa a rikice ta zabi ta koma daga gida ko daga cen adu'arta zata tardo Khadija da bacin ran da ta kwasa, shine abin ya daure min kai irin kukan da take a jiyan nan, anya itama ba sonka take yi ba?"
Darius cike da farin ciki ya ce" Sarkina, ko dai princesses Iman ce mai wannan sa'ar?"
Hanja da yake ta auna maganar Pah a ma'auni da sauri ya ce" Pah, ban gane ba, wace ta tafi ina? Take kuka a kan me?"
Pah ya kuma yardawa kansa jarumta ya ce" Inaga ko a cikin hira ne jiya ta tsinci labarin ka kasance mai yin taraya da wasu yan matan da ba matayen aurenka ba, ni kam ban san meye ya hargitsata har haka ba, baka ga kukan da take tamkar zata mutu, cewa take kirjinta ciwo, ji take kamar lokacinta ne ya yi a taimaka a kaita Niger, gannin abin nata da gaske ne ta kasa nutsuwa da gagawa na umarci kan a kaita gida tare da bada umarnin ATTAHIR AHMAD ya yi jagorar bukatarsu ta cikin jirgin"
11/14/21, 12:54 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 99 · 0% Book details