Sashe 6
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
4 "Barka da sauka Londre" Bai amsa gaisuwarta ba sai fitar da dayar kafar tasa ya yi ya fice a motar gaba dayansa Da sauri ta raka shi da kallo tana kallonsa ta ga an bude wata bak'ar mota kirin da ita kirar kampannin Bintley Limozine Bai kuma kallon kowa ba aka ja su a cikin motar tare da yan matan nan biyu da suka fito daga cikin jirgin Wannan karron kasa rike abinda ke zuciyarta ta yi a hankali ta hade kanta da jikin kujerar bayan sun taso ita daya kwal a bayan sai masu tsaronta a gaba wasu a wasu motocin da gayar da suka zo dan tarbarsa sula juya palas ta hade kanta ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya tana girgiza kanta, sam bata san me ya dauki kansa ba aman ba komai zata je ga Sarki ta sanar masa komai shi ya isa da shi ai Wani irin falelen plt Wajen ba a wani zagaye yake ba sai shukoki da suka zagaye shi Wani bangare guda daya ne tal mai dauke gls wajen kamar an yi shi a tsakiyar filin ne wanda yake da kofar shiga daya tal Fitowa ya yi ko matan bai yiwa magana ba bale wanda ya tuko shi ya yi ciki cikin nutsuwa Yar yatsarsa ya dora a kofar shigar wajen wani farin madubin da na yi tunanin na kallon kai ne, sai dai yana dorawa wajen ya bude bayan ya gama scanning ya gane mai wajen ne ya bashi damar shiga Da sauri masu biye da shi din du suka shige sai iya masu escorted dinsan ne suka ja suka tsaitsaya sunna kara expect din place din Dan ja ya yi ya tsaya a lokacin da ya ga yan matan nan biye suke da shi A nutse ya juyo yana kallonsu sai da ya bale babar rigar dake saman jikinsa yana kallonsu da yar yatsarsa ya masu nuni mai hade da tambayar da suka gane ba tare da ya yi masu magana ba Kallon kallo suka shiga yiwa junna su biyun, du da irin tarin jin haushin junna da suke ji aman basa taba bari su nuna a gabansa A hankali dayar cikin sanyi ta dan daga kafarta da nufin karasawa inda yake tsaye muryarta na dan rawa ta ce" My Prince, ka gama da ni ne?" Dayar kuwa bata matsa din ba aman kuma ta tsura masa ido tana karantarsa, domin ita din ta kasance baba yar manya kuma mai tarin ilimi, tana tare da shi ne dan nata manufar ba dan wani abin daban ba A hankali ya motsa labansa cen kasa ya ce" Ku tafi ba zan yi fly ba " Kallon junna suka kuma yi a lokacin da ya juya ya nufi babar kofar da zai fita gaba dayansa a falon nan Murmushi ta yi ta juya ta nufi waje dayarma ta bita dan sun gama sannin tunda ya ce su tafi hakan na nufin ya gama morar ganga zai yarda kwalonta ne Da dan sauri sauri ya karasa wakeken kejin, hankalinsa a tashe ya karasa wajen da take kwonce Cike da tausayawa y kai gwuiwarsa kasa ya dora hannunsa a hankali yana shafata yana karawa kafin a sanyaye da yaren turanci ya ce" i'm sorry, yaya jikin ki?" Da kyau na kara wara idannuwana cike da tsoro da kuma mamaki kafin na fala a guje gefe na labe sosai ina hangen ikon Allah Wani dankareren kosashen ZAKI ne mai tarin gashi da yannayi na karfi mai dogayen hakora ya je ya rungumunma a irin wannan lokaci da ba dan haram bane mutun ya ci naman mutun ba da wasu sun yanka junnansu sun cinye dan halin rayuwa bale shi da ya zame masa wajibi kuma aikinsa kisa da cinyewa ya bi ya farauta ya dane ya cinye tas bale har an kawo masa a gida? Aman maimakun ya dane ya saka kan wannan bawan Allan da na kasa tantance balarabe ne ko jar fata ne ya masa danysa daya tak ya raba kashin wuyansa da dogon wuyansa da gangar jikinsa ya masa tauna daya ta yada kwala kwalan idannuwansa zasu bultso ya taune su tas ya hadiye kafin ya farwa sauran jikin ya dandantsa cikin nutsuwa ya yi karin safe da shi ya kora da ruwan dake ajiye, sai na ga ya dan jijiga daga inda yake ya mike tsaye kan kafafuwansa kafin ya shiga wani irin jijiga yana cira daga inda yake yana dora jibga jibgan hannayensa masu dauke da tarin gashi a wajen kafadun *HANJA* sannan yana kawo bakinsa dake bude yana shafa masa uban gashin dake wuyansa yana ta karra goga masa Sai a wannan lokacin na ga yana ta sakin murmushi kamar ya samu dan uwansa ya bashi kyakyawab runguma yana karra shafa shi a sanyaye ya ce" Nima na yi farin cikin ganninki, na damu da rashin lafiarki sosai, ina fatan yanzun da sauki my royal freind?" Kamar wace take jin yarensa haka ta sake shi ta yi baya baya tana tafia cike da kasaita da karfi da jin kai da wata irin isa wace daga inda nake a labe nake jin takun a cikin kirjina haka kuma zuciata ke yin dak dak dak domin wannan zaki ko nace zakayar ba karama bace , tabas da ake cewa yannayin girman kashinsu da zakin kiwo na gidan zoo da na jeji sakaku ba daya bane sai yau na yarda, tsarin kwalin dake cikin idannuwansu kadai abin shagala da kallo ne, sai da ta yi nesa nesa kadan da shi kafin ta wani irin girgiza sannan ta durfafoshi a gujen da ya saka na nemi sakin mutumen daga tsaye, aradu ban taba yarda cewar akoy masu wasa da rayukansu ba sai yau, tsaye yake a gabanta jama'ar rasululahi (S.A.W), ba tsoro, ba firgici, ba alamun zai juya ya fita a guje, baya tsoron kar a je koda mugun sabo ne suka yi da junna a yanzu kwakwaluwarta ta juye tana isowa inda yake ta cire masa kai? Bama wannan ba shin jama'a dama Zaki abin sabo ne? Kai jama'a Haka ta iso inda yake ta kuma neman dare shi, tagal tagal suka yi da sauri ya iya rike kansa da karfi yana murmushi ya kai hannunsa har kusa da bakinta hakan ya saka na kwalalo idannuwana ina kuma kallonsa kafin ya karra shafa gashinta sosai sannan ya saketa ya shiga tafia hankali kwomce tana gefensa itama tana tafiarta cike da kasaita har suka fito daga wajen da yake rufeta idan zai yi tafia Wani wajen suka je ya tsaya ya kurawa wani tableau ido, ita kuwa ta shiga dan zagaye shi cike da kasaitarta Habarsa ya dan dafe ya juyo inda take zagayen nata ya dan dafe kugunsa yana kallonta a hankalin nan dai kamar wanda yake yin rada dan baya so wani ya ji shi ya ce" Kin kyauta kennan? Kin rage cin abinci sosai dan baki da lafia ko? Idan nine kin iya zuwa kina son tayar da ni na ci ko? Zan rama ne" Ajiyar zuciya ya dan sauke dan hutawa da doguwar maganar da ya yi kafin su ci gaba da tafia, da hannunsa ya ci gaba da nunawa ya ce" I'm tired, u see ko cofee ban sha ba tafia ta tsayin awa takwas dan ina tunaninki " Ita dai Allah bai bata damar magana ba, aman wani ikon Allah idan ya fara magana har kamar mai dago kai ta kale shi kafin ta ci gaba da tafiarta A haka suka karasa kusa da bayinsa, abin mamaki a lokacin da ya saka kafarsa ciki sai na ga ta shiga kai kawo a kofar maimakun ta bi shi Wanka ya yi mai daukan lokaci kamar rana ce bayan yanzun lokacin sallar asuba ne ya gabato, hasken fitilun garin da gidan kansa sai ya saka bawa a cikin tunanin ko dai safia ta waye ne idan ba sama ya daga kansa ko ya kai dubansa waje da zai nuna masa cewar dare ne Yana fitowa daure da tawul kadai a kugunsa ya nufi wajen da suturarsa take, Iya gajeran wando ne ya saka kafin ya muke tsaye yana lumshe idannuwansa ya kai dubansa wajen agogon dakin dake kafe Kuma lumshe idannuwansa ya yi ya dauko wata jalabiya fara ya saka kafin ya nufi wajen da yake kebance a cikin wannan tankamemen falon ya mayar da gabansa gabas ya tayar da sallah Kwarai na yi mamakin ganninsa yana sallah, a irin wannan gari a yannayin halitarsa, irin shigarsa, irin yadda yan mata suka shige gidansa wa'inda na kasa gane mene dinsa ne, wace ya yiwa magana irin shigarta, kai lamarin da yawa, sai dai a irin yadda ya gabatar da ibadarsa ya tabatar min cewa idan ya tsinci kansa gaban mahalincinsa bashi da wani abin daban a gabansa sai shi, ya dukufa ya gabatar da sallarsa kafin ya yi adu'o'i sosai ya shafa ya kuma mikewa ya cire wannan jalabiyar ya mayar da ita wajenta Ido nake rinrintsewa, kai shi haka yake ne? Wane Wardugu (Na cikin Bak'a ce) a kirar diraran jiki, ginanen jiki, mai sanka sanka, shin karfe yake dagawa ko menene? Saman lalausar shinfidarsa ya haye a hankali ya lalubo commande biyu dayan fari dan karami dayan kuwa bak'i Daga kwomcen da yake ya gyara kwonciyarsa da kyau ya kara gudun AC sannan ya danna na labule suka rufe kansu su dukansu kafin ya karra rike bargon nan a jikinsa yana lumshe idannuwansa kasan zuciyarsa yana adu'a dan samun barci cikin tsari da amincin Allah Saman ta cira ta haye kusa da kafafuwansa ta kwonta saman lalausan bargon wutsiyarta cen gefe kanta ta kai ta shigemar da shi wajen kirjinta ta kwontar da kyau itama ta shiga neman barcin hankali kwonce A kalla ya yi barcin kusan awa biyar kafin ya ringa jin yadda take ta goga masa gashin wuyanta da ta karra buda shi sosai tana ta son juyo da shi tana ta cinninsa kan dole sai ya tashi Manyan idannuwansa ya dan buda da mayen barci da jan da suke dauke da shi ya juya a hankali a kasan makoshinsa kuwa cike yake da jin haushin yannayin jikinsa a cikin ransa fadin yake"Ya rab, yanzun kuma ina zan samu mace?" Dan tsaki ya