← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 114

Sashe 2

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

1 _*Darasinmu na yau, hadisin da ke da ala'ka da hali 01 cikin 46.*_ _*Manzon Allaah( )* *ya ce:{WANDA MUSULUNCIN SU YAFI KYAU DAGA CIKINKU SUNE WA'DANDA SUKA FIKU KYAWUN HALAYE, IN SUN FAHIMCI ADDINI.}* ```[Sahihul Adab;285]``` _Wannan hadisin yana nuna mana cewa a cikin musulmi, wanda halinsa yafi kyau to shine kuma musuluncinsa yafi kyau. Ai kyawun hali shine mutum, shine dottaku. Allaah Ya azurta mu da halaye masu kyau. Allaahu aalam. ) A hankali ta lumshe idannuwanta cike da wani irin mad'aukakin shauk'i, leb'unnanta ta d'an cije sai kuma ta bud'e tana kallonsa a sanyaye cike da wata irin k'aunar jar rigar dake jikinsa mai had'e da wani shar shar sai rawanin da gaba d'aya ya rufe masa gaban goshinsa. Cike da shauk'i tace "Dogarina, ina sonka, ina sonka kamar na mutu, ka ganni a nan tsabar k'aunarka ya sakani a kullum sai na je wajen hanyar ficewarka, sai nai ta ganninku ku dayawa kuna wucewa ashe dai kai d'in har an d'aura mana aure oh dad'i kasheni." Wata murya marar dad'i ya bud'a yace " Ke yi min shiru, ni bana son hayaniya ni nan da kika ganni sai dogariya nake iya so dan haka ki min shiru." Hannayenta ne ta had'e cike da tsoron ganin suturar jikin nasa na son komawa irin ta mutane sak sak ta had'e hannayen da kyau tana girgiza kai cike da hawaye take fad'in " A'a, a'a kar ka b'ace, kar ka saka irin kayan al'umma sak mutuwa zan yi idan baka zo min a mutun ba na ganka gani gaka kar kar ka min haka dan Allah!" Marin da aka kwad'awa fuskarta ne ya sakata bud'a nanauyan idannuwanta da suka gama rinewa suka gama macewa suka tafi duniyar mafarki, a firgice take kallon mutanen da suka zagayeta kafin ta ringa jin dariarsu sama sama sunna yi da dan karfinsu A birkice ta kuma zuba masu ido kafin ta kai dubanta kan hannayenta dake rawa ta kara jimke su da wani irin karfi a bayane ta sauke wata irin nanauyar ajiyar zuciya kafin ta ji muryar kawarta na fadin " Sai ki tashi mu tafi, an tashi fa kina barcin asara" Da sauri ta kuma kai dubanta kan allon rubutun kafin ta mike tsaye daga bajewar da ta yi tana duba jikinta cike da tsoron kar a je ta kwala fitsari sakamakon marin da ta sha, ita bama wannan ba shin kawarta ce ta kwada mata shi ko waye? Da sauri ta suri jakarta ta juya ta bi bayan kawar tata tana kara hararar du wanda suka yi ido hudu da shi har suka fito tsakiyar titi sosai Ba wada ta yiwa yar uwarta magana sai cen kamar an tukota ta nisa ta ce" Abin da mamaki, yadda kika san a gaskene haka na ganshi kai jama'a ko dai mahaukaciya ce ni?" Juyowa kawar tata ta yi da dan bacin rai ta ce" Ai in dai a da ke ba mahaukaciya bace a yanzu zaki ja a maki irin mugun kallon nan, haba dan Allah kin ga yadda kike makyarkyata kina magiyar kina sonsa? Kina son waye ne? Ke haka zaki yi ta yin abin nan?" Tsayawa ta yi jikinta ya yi mugun sanyi muryarta a sanyaye ta ce" Ko dai na haukace din ban sani ba?, Juyowa Amina ta yi tana kallonta, irin yadda idannuwan nan nata masu kwayar ciki mai blue mai duhu da dan baki tsakiyarsu suka tara ruwa suke wul wul da su ta tabe baki kafin ta cije bakin nata ta kara fara tafia Da sauri ta kamo hannunta a sanyaye ta ce" Amina, dan Allah ki fada min ko dai alamu ne na ciwon hauka ya kama ni? AMINa ni ko dan aiken gidan sarki ne a aura kin ina so, da na tsaya a dogari dan na ga a duniya idan kana son gannin wanda ya fi kusanci da sarki to dogari ne, dogari fa shi ke gyarawa Sarki zama a saman doki, ya gyara masa babar rigarsa ya saka masa lema ya rikw masa, a duniya sirrin sarki sirrin dogari an ce fa har bayi yake raka sarki, idan Allah ya amshi adu'ata da na jima ina yi na kasancewata yar uwar sarki ya bani dogari na aura ai na gama zama dangin sarki" Galala Amina ta yi tana kallonta kafin ta janye hannunta da sauri ta ce" Walahi ki nutsu , kulun ina fada maki ki fa nutsu, ba dai sirrin sarki ba shine matar sarkinma! Wannan abin na tabata baki da lafia a kan maganar sarauta ke kam a nan kika kare, a duniyar nan du labarin wata masarauta a tafin hannunki take, idan ana history na sarakai har lumshe ido kike , kai ina kwakwaluwar nan taki da sake walahi!" Kanta ta ringa gyadawa kafin ta tabe lebenta na kasa ta juya kwayar idannuwanta da yannayi na dan fada fada irin ta ji haushin nan ta ce" Sai me? Inace ke a duniya dan wake ko a gaban waye akai maki tayi zaki ci? To kowa da irin jarabawar da Allah ya dora masa, ni tawa ta dogari ce idan ana budar kaini dakinsa ki fadi ki mutu don Allah!" Itama bakin ta tabe kowace ta juya cike da bacin rai ta kama gabanta Jira nake na ga ta nufi wani lalatacen gida duba da yannayin suturar jikinta, jira nake na ga ta shiga wani gidan namu na yaku bayi duba daga makarantar da ta fito, sai dai wani rantsatsen gida mai shegen kyau ta kutsa kanta kai tsaye ba tare da shayin mai gadin dake zaune yana busar tabar sigarinsa ba, shi din kansa sai na ga bai wani yi yinkuri na dakatar da ita daga kokarin shiga gidan da yake ba nasu ba wanda ga dukan alamu aikota aka yi Kai tsaye ta zagaya ta gefen da yake kamar madafa ne , mace biyu ta wuce sunna zazaune sunna cin abinci ko ci kanku basu yiwa junna ba har ta karasa madafar nan ta shiga da sauri ta shiga bubuda kwanikan da ta tabata a nan ake saka mata nata kason abincin da sam mutun ba zai yi tunanin a gida irin wannan ana rabon abinci irin haka ba Gannin wayam babu ya sakata fitowa rai bace ta kare masu kallo kafin ta girgiza kanta ta koma cen hanyar shigar ta buda tankameman falon da yake falonsu ne Ja ta yi ta tsaya tana karewa falon kallo bata san lokacin da ta saki jakarta ta makaranta a nan ba ta janyo wani ashar ta dire tana kallon falon ta ce" Kai uban kowa ya fito daga wajen da ya shiga ya labe yau a yita ta kare a gidan nan" Ba wai maganar a fito din ba, ko wa'inda ke zaune wani shashakai suka kaleta suka juyar da kansu Kanwarta ce ta zo wucewa da roba a hannunta ta ce" Ke kauce zan shige" Hannunta ta saka ta janyota kiiii baya ta yada sai da ta yi tangal tangal kafin ta juyo da yannayi na tashin balagar rashin kunya ta buda baki zata yi magana maganar ta makale mata sakamakon shako wuyanta da ta yi tana firfito mata idannuwa ta ce" Ke yaushe na zama sharar da zaki bangajeni ki nemi wucewa ko tunani kike kin fara tara mazaunan da suka kai nawa da zasu iya bangaji a bakin hanya? Bama wannan ba uban wa ya bata falon nan da na tashi tunda safe na share dan na ji dadin zama idan na dawo?" Muryar maman wace aka shake din ce ta fito tana zarro ido cike da mamaki tana tafa hannu ta ce" Ke ke ya haka, yaya zaki kama min y'a ki makure haka salon ki saka fatar jikinta ta yi birdi bayan yar ja ce ba bak'a ba?" Da yannayin jin haushi ta hankadata tana kallon kishiyar maman nasu da kuma kanwar tata dake gudu tana ihun sai ta halakata tana neman mabugi ta ja wani uban tsaki ta ce" Dan Allah mama kin ga ni ba wannan ne ya tsayar da ni ba, idan kin tuna tun da safe na gyara dakin nan aman shine dan rashin tarbiya yaren nan suka lalata kuma ba zan san waye ba dan na hukunta shi?" Maman ta gyada kai tana kallonta ta ce" Ke yanzu banda jarabar tsafta me kika iya da har zaki tisa mutane a gana daga dawowarki ki shakar min yarinya ne, wai ko dai kin manta yadda aka haifeki da jinni a gidan nan haka na nakudo yar nan na haifi abina ko wani shegen ne ya rada maki a daki cewar kin fita iko da gidan ubanta? To ki shiga taitayinki, ki je ki ja tsuman rayuwarki ta kamaceceniya da namiji sannan ki iya da rashin lafiar dake damunki na haukan son dogari ki barmin yata ta wala son ranta a gidan ubanta, waje ne idan kin yi niya ki gyara idan baki yi ba ki matsa abinda ke ajiye ki zauna ehe!" Tana gama fada ta ja hannun yarta suka yi waje tare, uta kuwa ta kuma bin falon da kallo kafin ta girgiza kanta cike da takaici ta dauki jakarta ta nufi dakin mahaifiyarta Tana zuwa ta tura kofar ta ja ta tsaya tana kallon maman nata du wannan hayaniyar barci take kashirban a irin wannan lokacin da aka yi salar la'asar aka gama har duhun magariba ya fara shiga A hankali ta karasa bakin gadon ta tsaya a sanyaye ta shiga dan kiran sunnanta tana kallonta A firgice ta farka suka yi ido hudu da yar, da sauri ta maida idannuwanta ta rufe tana girgiza kanta ta kuma budewa a kanta ta ce" kai subahannalahi wannan ido naku na gado ba dai abin tsoro ba, ke wai ban ce da ke ki ringa barina ina barcina idan ta kama ba yanzun da kika tasheni muka hada ido da ke da magagin barci yaya kike so na yi ne? Idanfa na firgita na zo ina mafarkinki kai ku dai kun dauki jinnin wahala walahi gashi tun kina jaririya nake kaiwa sarkin mayu ya duba min kar a je mayu ne ku ban sani ba aman amsar daya ce ku din ba mayi bane kuna dauke da baiwa ce idon mage
Chapter 2 · 0% Book details