Sashe 28
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
1
A hankali ta ringa sasautawa har ta daina gujin kukan hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya yana dan murza hannayensu su dukansu ya ce" Nawa suka warke masu dauke da ciwon nan? Shi likitan da wa suka tara sani da har zai yanke ranar mutuwar mahaifina?"
Da dan fada fada abansa ya ce" Ba wannan zaka yi ka birge ni ba HANJA, abinda nake so da kai shine ka ajiye tukin jirgi! Kai direba ne? Me aka yi aka yi aikin tuka mutane a lokacin da suke barci sunna shagalinsu? Ka kuwa san irin darajar dake tare da kai? Allah ne ya darajaka, ya baka damar da za'a yi maka biyaya, kai za'a tuka kana barci ko kana farke, kai za'a amsa kiranka a duk lokacin da ka yi gyaran murya ko ka so, aman ina kana zaune kaine ka zama abin gani ga kowa? Kaine ka zama abu mai arha ga kowa? Abinda nake so da kai ka ajiye jirgi, ka ajiye mata ka samu mace daya kwakwarar da zaka iya zama da ita, kai idan kana so ka dauki hudu ka zuba a inda kake so HANJA ka nutsu ka dauki mulkin da yake naka ka ja ragamar kasata! Hakan shine zai sa na je makwoncina cikin salama!"
Hanja ya cije lebensa na kasa kafin ya dago yana kallonsa ya ce" Meye a ciki dan ina tukin jirgi? Haramun ne dan ina dan sarki kar na yi tuki? Kai ka san bana son mulkin kasarka , ka ba dan uwanka mana? Ka maida sarauta gidan dan uwanka menene a ciki? Ko daga kasar nan muka fita zan iya yawon duniya da mamana na bata kyakyawar kulawar da ya dace da ita!"
Aleesa muryarta a sanyaye ta ce" Zaku fara ko? Fadan ne zaku fara ko? Maimakun mu yi zaman lafia ba zaku iya jimawa ba sai kun yi kau? Huby ba mun gama maganar aikinsa ba? Yaya kake so mu yi bayan aikin nan ya tashi ne yana hade haden abubuwansa? Lamarinsa da jirgi ya zama baban lamari mai ban mamaki, shi ba za'a ce jinnu ke bashi ba shi ba aljanin kansa ba, ka manta tun yana da shekara nawa ya gwada tuka jirgi? Ka manta irin faman da muka yi a shekarar da ka hanna shi tuka jirgi? Ina so mu fahimci junna bana son rigima dan Allah....." ta karashe maganar muryarta a sanyaye tana kallonsu su dukansu kamar ba yanzun suka gama kukan kaunar junna ba shine har zasu hau sama su fado dan kawai rigimar da basa gajiyawa da yinta
Ajiyar zuciya Hanja ya sauke ya kara lalubo hannun mahaifinsa da shima jikinsa ya yi sanyi, muryarsa a sanyaye ya ce" Ba mamaki ni da ake yiwa kallon mai lafia na rigayeka shiga kabarina Papa"
Kallonsa ya yi da sauri hak
an ya sa Hanja sakar masa murmushi ya ce" Mutuwa yanzun ta zama lafia lau ka ji an ce mutun ya mutu, idan lokaci ya yi za'a mutu koda ba'a shirya ba, idan lokacin ne ya zo ko ana barci za'a mutu ne, ko ana tsere a doki za'a mutu ne, bale masu hawa abin hawa......."
Yanzun kuwa Aleesa ce ta masa kallo irin na ka tausaya min ka daina maganar nan, aman bai daina ba ya ci gaba da fadin" Mun kasance musulmai ne mu, hakan ya sa muka taki baban sa'a ta rayuwa ta imani da daukan komai daga Allah ne, Mutuwa hutu ce ga mumuni, sannan bawan da ya kasance mai kare dokokin ubangijinsa ne, mai jin tsoron Allah a badininsa ba wai kawai a bayane ba aman kuma a cen cikin zuciyar ba haka ba sai ka ga bai kasance cikin annabawa ba aman kuma kasa bata ci namansa ba, nawa ginni ya biyo ta kansu aka tono su kamar yanzu aka birne su? Papa ka kasance mai kamantawa, kana bayar da sadaka da hannunka na dama ba tare da na hagun dinka ya sani ba, kana ta yakin yada adinin musulunci a kasarka ba dare ba rana, ka gina masalatai, ga gina rijiyoyi, ka gina gidan marayu bila'adadin a kasarka, kai din mai lazumtar Suratul *Mulk* mai falala ce, kana karantata ba dare ba rana wace ko ni nan kai ka sabar min da karantata maimakun zancen zuci sai na yi nisa a ita nake gane ita nake karantawa, wace idan bawa na karantata bale idan ya zo kwonciya kabarinsa zai kasance yana wani irin kanshi koda yaushe kanshin nan yana nan, sannan tana taya ka hira a cikin kabarinka, tana cikin surori masu ceto, koda yaushe tana tare da kai Papa, Papa ko kana aikata wani aiki a boye ne mumuna wanda ya dace mu fito da shi mu zanta a kansa? "
Ya karashe yana tsatsare mahaifinsa dake jin wata salama a kasan zuciyarsa da idannuwa
Mahaifinsa ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Eh "
Su dukansu kallonsa suka sake yi da jiran jin karrin bayani a kan hakan
Mahaifinsa ya hade hannayensa ya ce" Laifuka bawa na aikata su a ko wani motsinsa, sai dai ina astaghfari a kowani motsin nawa, baban laifina Hanja shine na kasa hanna ka baban zunubi a cikin zunubai, an ce idan mutun ya mutu in yaronsa na aikata laifi za'a tashe shi a nuna masa, shin yaya zan yi da tashina da za'a ringa yi ana nuna min kai kana aikata ZINNA?"
Idannuwansa ya lumshe cike da jin kunyar maganar, kafin a sanyaye ya ce" Na san zan daina, dan ina kokarin son gannin na daina din Papa....."
Aleesa ta sauke ajiyar zuciya tana dai kallonsu
HANJA ya hade hannayensu a hankali ya ce" Zan daina aikata zinna in sha Allahu, ba zan dauki alkawarin na daina ba, aman zan kasance mai tuna nasihohinku a duk lokacin da hakan ya nufo ni, kuma zan tuna azaba da bin bashi irin na zinna na tabata in dai a hankalina nake zan hanna kaina aikatawa"
Murmushi Aleesa ta yi tana jin sanyi har a kasan zuciyarta kafin ta mike ta nufi wajen table din nan na gilas ta kunna AC dan har zufa take ita ta dawo ta zauna wajen da suka ci gaba da tataunawa
Cen Hanja ya bushi iska ya ce" A yanzu burina shine na zaga duniya da ku, zan debe ku mu tafi yawon kasashe da ku, ina kuke son zuwa? Ina da ina?"
Murmushi mahaifinsa ya yi cike da jin dadin irin yadda yake karra dauko jarumta yana yafawa kansa ya ce" Baban burina shine na ga aurenka, na biyu na je saudiya na jima ina bauta, na uku na taka kasar AFRICA na ga namun daji...."
Aleesa na yar daria kadan kadan ta ce" Yeah, ka kuma min alkawarin zaka kaini ka hauda ni Giwa"
Shima da yannayi na farin ciki ya ce" Eh ban manta ba, da kuma......"
Hanja dake kallonsu cike da kaunar iyayensa a sanyaye gannin karfi da yaji su so suke su nuna masa sun fa sakar basu da wata damuwar a ransa yana ayana ba Africa ba , ko kudus idan kafa na takawa zan kai ku, a bayane kuma ya ce" zamu fara shiga Africa, mu je ka ga dukkan abinda kake so, akoy jirgin da zan ja nan da sati uku zuwa Africa, in sha Allah zamu je tare , yanzun Ku tashi mu yi sallah, lokaci ya yi......"
Kwarai murnar ganninsa ya shashantar da su duba lokaci, duda ba kira aka yi ba aman sun saba da alwalarsu ake kiran, nan kowa ya tashi ya nufi bayi dan daura alwallah dan su samu sallah a kan lokaci zukatansu cike da farin cikin jin yau shine ya yarda zai fita da su...........
WANNAN kennan
..........................................
A kwana a tashi yau kwananta goma talatib cif a wannan gida
A wajen nan ta hadu da mutane kala daban daban masu halaya kala daban daban
Har yanzu tsakaninta da Ameerah ba wani jituwa, to da wa Ameerah ke jituwa? Bata jituwa da kowa dan dai na wani ya fi na wani ne
Rayuwarta take a nutse, tana kokarin daukan dukan horon da ake basu, duda har yanzu ta kasa yin tafia ras da dogon takalmi, ta kasa iya yin kwaliya uwa uba Girki ya gagareta, dan ko dan wulakancin Ameerah ya ci ace ta iya abubuwan nan aman cikin ikon Allah ta kasa iya su, wanda hakan ke sakawa Ameerah fadin cewa ina za'a yi zama da Hottest din da bata iya girki ba, bata iya tafia da takalmi a saman kasa bama bale a cikin jirgi? Da bata iya kwaliya ba? A yaya take so ta tsaya gaban Pasinga da katon tuwon takashi? Dan kuwa duwawunta sunna samun hutu karra bajewa suka yi abinsu, Ita kawai ta san asara ce da bata lokaci bayan wannan ina yarinyar nan ina wannan aiki mai daraja?
A haka take karra dadafawa,
A tsakaninta da daliban nan babu tsana ko bakin cikin junna dan ba wanda yake gefen mamansa ko abansa kowa kansa yake nema kowa kuma horo yake dauka, abotarta da Saudat ta zama kut da kut domin sunna taimakon junna ainun sai dai gaba daya Ameerah ta dora mata karan tsana, da tana nan da bata nan idan abu ne ita take dorawa, ya kasance kowa ya gane tsanar da ta yiwa ameerah mai yawan gaske ce
Gefe daya kuma Sir na nan, Sir ya kasance mutun mai taimaka mata sosai, ita har mantawa take cewar shine shugabansu a wajen nan dan idan waje ya kasance daga ita sai shi takan yi mamakin irin yadda yake mu'amala da ita, tana jin dadin mu'amala da shi domin har kiransa take da freind ya kuwa amsa mata cike da farin cikin tana sakewa da shi yana mutunta ta, yana mata tambayoyi kan rayuwarta, yakan kwontar mata da hankalinta, ya mara nasiha sannan ya shaida mata ta ci gaba da kokari kar ta gajiya, domin babu maraya sai rago! Walahi zai iya rantsewa rabonsa da ya ji mace har tsakiyar ransa har ya manta .......
.......
Kamar yadda aka saba sau uku ake shiga kicin dan girki, yau asabar ranar girki ce
Gaba dayanta a tsorace take, hankalinta a tashe yake
Du sun halara aman bata wajen, tana labe ne bata fito ba
Ameerah dake tsaye sanye da wando da riga farare irin na chef da hula fara ta kalli Saudat a dake ta ce " Ina isashiyar kawar taki?"
Saudat ta sosa kanta a hankali ta ce" Muneerath ki fito mana "
Muneerath ta sauke ajiyar zuciya bila adadin kafin ta fito tana sanda ta zo ta layu da su
Ameerath ta yatsina bakinta ta mika mata takardar da abinda za'a girka ke ciki a dake ta ce" Ki dafa mana kina mana bayani"
Ido Muneerath ta kurawa rubutun cike da tausayin kanta , ita sai ta rantse da Allah bata san meye ktp ba, ta taba ganninsa ne? Wani abin takaicin wai atahugun da ake jajagawa a nan aka ce ta yanka salon ta manta ta murza ido ko ta kama ruwa ko?
Juyowa ta yi ta mikowa Ameerah takardar ta ce" Ni ban iya ba!"
Ameerah ta zarro ido , yau kam ta kai bango walahi yau ba zata iya ba, watan yarinya guda cir a tare da su aman bata iya girki ba? Rai bace ta ce" Ku biyo ni ku dukanku dakin taro! Yau za'a yita ta kare dan walahi yau sai kin bar wajen nan!"
A tare suka fito su dukansu sunna son su bata hakuri da sauri Muneerath ta sha gabanta jikinta na rawa ta hade hannayenta kamar zata fashe da kuka ta budi bakinta zata yi magana aka danna laluwar makarantar tasu
Kasin su ankara suka hango an wangale katoton get din
Kafin suke yin wani yinkuri suka ringa gannin wasu irin dakarun mutane masu sanye da kakin da a inda suke ba zasu iya cenko ko na wani gari bane , sai dai abinda suke ganni na ban mamaki ya saka su dukansu maida hankalinsu
Tarin dakarun sojojin nan ne suka layu tun daga bakin babar kofar shigowa har inda suke tsaitsaye
Jeruwa ne suka yi sunna facing din junnansu gaba dayansu ririke da wasu dogayen wukake farare tastas sannan sun hade wukaken waje daya su dukansu
Waji dankareran namiji ne ya shigo ta tsakiyarsu rike da bindiga da wani usur mai karran balaki, lokaci daya kuma SIR da sauran sojojin gidan masu nasu tsaro suka fito suka nufi wajen su dukansu a hanzarce sai dai basu karasa ba aka dakatar da su kan su tsaya a inda suke har bakin su tardo su
Zuwa yanzu sun fara tsurewa da wannan lamari, Saudat jikinta na rawa kasa kasa ta riko hannun Muneerath da ta saki baki da hanci tana ayana abin mamaki baya karewa a wajen nan ta ce " Muneerath mu gudu kar a je kashemu aka zo yi "
Muneerath ta ji cikinta ya bada wani irin kuuuuuuuuu ta juyo da sauri tana kikifta ido zata yi magana da baban abin magana aka ce" KU SADA DUBANKU, KU DUKA KAFAFUWANKU, KU KASHE WAYOYINKU, KU BADA HANKALINKU DAN KUN SAMU ZIYARAR.......
Shin waye ya zo?
Me yake shirin faruwa?
Wai yaya kuke jin labarin nan?
Taku ce yar mutan niger
Na yi mantuwa AKPI ne sunnan ba APKI ba
11/14/21, 12:47 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*