Sashe 45
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kyau ba Hannunsa ya mike ta gefenta, sai dai ya yi daf da ita sosai ya amshi takardar ya juya da yannayin takun nan nasa ya kai saman teburin likitar sannan ya hau kan kujerar dake kusa da ta likitar ya zauna Da sauri ta lumshe nata idannuwan itama tana jin bugun zuciyarta na ta tsananta har sai da Sir ya karaso kusa da ita muryarsa kasa kasa ya ce" Ki je ki tsaya kusa da su har a zo kanki, dukan tambayar da aka maki ki yi kokarin bada amsa a kan tsari idan har kina so a yi tafiar nan da ke yau" Sai a lokacin ta sauke ajiyar zuciya ta gyada kanta kafin ta karasa kusa da yan matan ta tsaya, Sir ya bita da kallo cike da mamakin yadda ta sauya sosai kamar ba ita ba, fatar jikinta, wannan kiba tata da tumbinta du babu, sai abin kwalin da ya nuna masa harta da idannuwanta aun kara fari masha Allah, bama a maganar abubuwan da suka fi saka shi shagala da tunaninta wanda yake gannin ai normal ne idan dai namiji na iya zayane abinda yake so da mace dan ya yi tunanin nan ba matsala bane tunda dai ba tabawa ya yi ba A nutse take bin dukkan yannayin tambayoyin da ake masu da irin amsar da suke badawa cikin ladabi da kallo harta da comportement dinsu Yawu ta hadiye a lokacin da ta kusanta ta je ta zauna itama bayan an bata damar hakan tana kallo aka tsikara mata allura itama aka dauki jikkinta , aka kuma auna idannuwanta da hawan jinni akai mata tambayoyin nan kafin a umarceta kam ta je ta yi fitsari ta bada dan a tantance mahaifarta idan bata dauke da ciki Ba yadda zata yi ta iya hanna kanta barin jiki Ba yadda zata yi ta iya hanna kanta jin tsoro Babu yadda zata yi ta iya hanna kanta kallonsa domin shine dodonta, shine abinda yake bata tsoro, shine wanda ta ganni yana wasa da zakanya hankali kwonce, shin idan aka ce ya yi wasa da mutun fa yaya zai gabatar da wasan? Zai cire kan bawan Allah daga gangar jikinsa ne ya wurgar, zai kama ya raba mutun biyu ba tare da ya saka wuka ba, hakan ya sa du takunta ke saka jinninta hawa wanda ta tabata ana aunawa za'a ce ta koma gida ba zata iya tafiar nan ba Zama ta yi ta sauke dubanta a kan farar takardar dake ajiye dan idan ta dago idannuwanta a cikin nasa take saukewa wa'inda suke mata kama da zaki, domin ja ne da su sosai kamar ya sha abin maye Likitar ce ta gama daukan jinnin da yannayin bp dinta ta mikawa wace ke tafia dakin gwaje gwajen da shi sannan ta koma ta zauna ta shiga yi mata tambayoyin kamar haka Yaya sunnanki ke haifafiyar ina ce? Shekarunki nawa? Muneerath ta gyara zamanta a hankali ta ce" sunna na Muneerath M , ni haifafiyar kasar Nijer ce, shekaruna ashirin yanzun " Da mamaki ta kalli HANJA da yake kallon Muneerath dan shima maganar shekarunta yanzun ya ji, sai dai ba damar ta masa tambayar yaya aka yi ya ce yar mamansa ce da kuma karancin shekarunta, Sai kawai ta yi shiru ta ci gaba da tambayoyin kamar haka" Muneerath ke musulma ce ko christa?, Kina da aure ko baki da? " Muneerath ta bada amsar ita musulma ce, sannan bata da aure zuciyar fal tunanin ya aka yi sauran ba'a masu irin tambayar nan ba, bata san cewa dole bakuwa take sai an bi hawa hawa kafin a bata damar shiga Likitar ta ce" kin taba haihuwa ne ko kim taba samun ciki baki haife shi ba? Idan kin taba sau nawa? Da rai ko babu? " Da mamaki Muneerath ta waiga wajen Sir sai ta ga yana tsayen dai aman kasa yake kallo dan haka ta maido dubanta ta ce" Cewa fa na yi ban taba aure ba" HANJA dake dan kada kafarsa ya wurga mata wata irin harara dake nuni da ki bada amsar da aka tambaye ki a kai Sir ya matso da sauri domin dama yana wajen ne dan shine responsable din Hostesss ya kalli Muneerath ya ce" Amsa zaki bada daidai da tambayar da ta maki " Muneerath ta lumshe idannuwanta a hankali ta cike lalausan fizgegen pink lebenta da tsararun hakoranta na kasa sannan ta bude ta dora dubanta tar a kansu ta ce" Ban taba haihuwa ba, ban taba zubar da ciki ba, cikinma ban taba samu ba" Sukan amsoshinta tana rubutawa ne har ta gama ta dora da fadin" Saurayi nawa kika taba yi, da nawa kika kwonta ?" Tambayoyi ne da ake yiwa kowace bakuwar Hostess kafin ta fara aiki, tambayoyi ne da ba'a dauke au a bakin komai ba domin ana so aikin da za'a fara da kai a san waye kai a bayane a kuma gamsu da bayananka , sai dai gaba daya wadinnan tambayoyi suka zubawa Muneerath matsanciyar kunya da jin haushin masu yi mata itan , ita kuwa likitar tana cikin mamakin amsoshin Muneerath inda Hanja kwata kwata baya yarda da amsar shi bai wani yarda ba yan matan nan na yanzu ai sai su Muneerath a sanyaye ta ce" Bani da saurayi " A kufule HANJA ya daka tsawar da ta saka Muneerath rintse idannuwanta ya ce" Amsar tambayar da aka maki ake so ki bada ba raina mana hankali ba , a nan babu wanda ya damu da ke bale ki yi kokarin birge shi!" A rikice ta dago ta zubawa fuskarsa ido kafin ta bude bakinta lebenta na rawa ta ce" Na ce bani da shi, ban taba yi ba ban sanshi na, ni ba yar iska bace ta yaya kuke so na ce maku ni yar iska ce, bai ce yana so na din ba tukunnan sai na koma ko!".....sai kawai ta fashe da kuka tun karfinta ta kifa kanta saman table din gaba daya jikinta na rawa dan ita bata ga a wani dalili za'a ringa mata wannan wulakancin ba, a karuwa suke daukanta hala ko me? Hanja , chok, Hanja bakon lamari, HANJA madaukakin rainin hankalin yarinyar ya saka shi ruko ido da sauri ya kai hannunsa wajen bakinsa da mamakin da ya saka shi bude baki na irin ihun da ta yi a lokacin da shi Prince HANJA kuma shugabanta a wajen aikinta ya yi magana ta masa ihu da magangannun da ihunta suka dauka da kuma kukan da ta fashe da shi ta kifa kanta a yau ranarta ta farko a wannan waje ya saka shi jin wata juwa na son kwada shi da kasa.....ya Rab MAH da wa kika hada ni kuma? Likitar da ta ruruko ido itama ta mike tsaye tana kallon ikon Allah da sabon al'amarin yarinyar da kukan duka ta gama sakawa ranta shikenan yarinyar nan zata ja a koreta ko aikin bata fara bane ta kalli Hanja dan so take ta dan bashi hakuri kar ya yi gagawar furta kora a bakinsa dan ba zai dawo baya ba ta ji muryarsa a dan sanyaye na irin takaici ya kume kan nan ya ce" ................ Alhmd 11/14/21, 12:49 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*