← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 114

Sashe 38

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 2 A mugun dake ya ce" Yaya sunnan ki? " Muneerath ta dago innocent face dinta a sanyaye ta ce" Muneerath " Bakin nata ya kala kafin ya yatsina fuskarsa ya gyada kansa da yan yatsunsa ya nuna mata wajen zama yana jira ya ga ikon Allah shin zaman zata yi ko meye? Ai kam Muneerath, ta gyara tsayuwarta ta zauna abinta tana kara sada kanta, sai dai bata idasa zaman ba ta ji wata irin razananiya firgitaciyar tsawar da ta tabata har na wajen nan idan dai sunna ji Sun firgita da wannan tsawar, Bata idasa mikewa a kan kafafuwanta ba ta ji an jijigota daga zaunen da take an yi baya baya da ita an hadeta da jikin garu kafin cikin yaren turancin da da kyar take ganewa ya shiga fadin" wacece ke? Me kike takama da shi? A duniyar mararsa kunya wani mataki kika taka? A duniyar yan ta'ada wacece ke? Ko a duniyar yan bariki awa nawa kike iyawa da namiji mai sunnan namiji?" Da dan ihu ya karashe maganar hakan ya saka Muneerath rintse idannuwanta zuciyarta na dokawa tamkar zata faso daga kirjinta ta fito, gashi dai hannu ne mai laushi ya taba fatarta, ya makureta, sai dai abin takaicin hannun garjejen katon da ba muharaminta bane, uwa uba zafin da take ji a makurar nan tamkar za'a kasheta A gigice ta buda tsumamun idannuwanta da suka tsumu da ruwan hawaye ta sauke a cikin nasa wanda yake binta da wani irin kakausan kallo wanda ya taru da tsagwaron tsana , Numfashinsa na dukan nata sakamakon irin matse mata wajen da ya yi , gaba daya numfashinta neman gagararta yake a irin wannan lokacin , jinta ya fara yi mata nisa kafin ta tsinkayo wannan murya tasa mai dauke da amo irin na zaki ya ce" Babu macen da zata shigo ni da raini dan ta birgeni da kowace irin halita take takama da ita domin a mace ba kalar da ban gani ba , ban ganta ba, ba'a haliceta ba, bale a filin aikina dukan mata maza suke a gabana! Tsagera kuwa ni babansa ne!, Dan ta'ada ni ubansa ne domin bana daukan kalmar ta'adanci, bama sasancin da dan ta'ada, kuma babu maganar sulhu ko yafiya tsakanina da dan ta'ada! Kin fahimta?" Ya idasa da wata tsawar da ta saka Muneerath kuma rintse idannuwanta kafin ta bude da karfi tana kallonsa Zuru zuru take yi da idannuwanta kafin ya cikata ta samu didigenta a kasa ta karasa kasa ta zube gaba dayanta yadda ka san an jijiga bera an sake shi sai zarar ido take kamar ta zagi babar sarki , jikinta kuwa yadda ka san an jonna mata soket rawa yake gab gab gab kamar zazabin bana idan ya maka mugun kamu Kamar ba shi ba ya gama hayaniyar ya juya ya koma saman kujera ya zauna a saman wace ta tashin yana gyara hannayyen rigarsa dan sun dan ja baya zuciyarsa cike da takaicin wannan rana da shi hanja ya kai hannunsa jikin mace ba dan ya yi having sex da ita ba sai dan yamata kashedi, ashe shima zai iya aikata wannan shirmen? Ashe shima aikata wannan shirmen na iya hayo masa kai tsaye? Tabas wanan yarinyar ko yau ya maida ita kasarsu sai ya rubuta ya ajiye cewar ya kai hannunsa wuyan mace ba namijiba da nufi shaka irin na kashedi Da sauri madame ta shigo ita kanta jikinta na bari, sai da ta ja kanta a sade ta bashi hakuri kafin ta yi wajen Muneerath ta kamata ta mikar da ita a sannu ta nufo wajen kujerar da ita Da sauri Muneerath ta ja ta tsaya jikinta na bari ta kalli Madame tana girgiza mata kai ta ce" Me na masa? Kar ki kaini wajen cen kasheni zai yi kin ga bindiga ce ya ciro" Ita dinma jikin nata na rawar ta ce" No baya kisa ba zai kasheki ba, aman rashin zuwan naki zai hadasa mana matsala baki dayanmu,baku yi maganar ba ai" Muneerath wannan karron sai ta gama yarda cewa garin jarabarta ta kawo kanta wajen da zata rasa rayuwarta, ya salam wani irin basu yi maganar ba? A wannan maganar ai ya yi ya gama fadin komai kuma ta yarda ta dauka ina ita ina kokowa ko fada ko dayan abin da ya fada wa wannan mai karfin yan film din indian? Sai dai tana ji tana gani madame ta karasa da ita auka tsaya bata zaunar da ita ba sunna jira ya basu damar zama Kansa ya dago tun daga kan gashin kanta ya bita da kallo har kafarta kafin ya sake kallonta daga kanta ya dire a wajen tumbin da ya gani wancen karron ya ga yanzun babu shi ko kadan Kansa ya cire a kanta ya karra hade fuskarsa sosai yana kallon yadda jocyline ke karra hade hannayenta tana karra bashi hakuri kafin da yar yatsarsa ya nuna tana iya zama Da sauri Jocyline ta zaunar da ita kafin ta juya ta fita tana share kwallah ta tausayin kanta da kanta Sai da ya gama shan iskarsa kafin ya bude litafin tambayoyin da aka tanadar dan a yiwa wanda ake tuhuma A nutse ya bi rubutun da kallo kafin ya tabe bakinsa ya rufe ya hade hannensa cikin junna yana kallon yadda idannuwanta ke yin marmarmar ya ce" Ba a maki lesson na ducation ba?" Muneerath ta ringa hanna kanta sob dagowa ta kale shi, aman cikin ikon Allah sai da ta ji gaba dayanta ta dago da dubanta ta kuma masa duba a karro na uku ido cikin ido Nasa idannuwan ya cire a cikin nata, ba dan komai ba sai mamakin kwayar idannuwanta da kuma yadda suke da kyan kallo, du irin yadda take cikin tashin hankali basu nuna ba saima wani walwalwal da suke A takaice ya ce" kin san wanene ni? " Muneerath ta kuma bin gashin kansa da kallo a sanyaye ta ce" Kaine ka kawo ni daga garin mu, tare da matarka" Da sauri ya kale ta jin ta ce da matarsa, matarsa kuma? Sai ya kuma cire duban nasa ya girgiza kansa yana ayana ya sani dama bata san waye shi ba, da ta sani du tsaurin idannuwanta ba zata iya fuskantarsa da yannayi na rashin kunya ba Sai kawai ya ga ashe bata lokacinsa ne ya yi na yin hargagi a gabanta , yanzun tsakani da Allah idan na wajen nan suka fita suka yada yanda ya yi da yarinyar nan me za'a kale shi ? A ce masa me du ya tsalake manyan mutane ya zo kan sa'ar kanwar bayansa ya yi hayaniya? Dan shafa gaban goshinsa ya yi ya mike tsaye ya dauki bindigarsa ya mayar jikinsa a dake ya ce" Mu je " Da sauri ta mike tana kallon bayansa ta ga yadda nan da nan ya kai kofa a dan kankannin taku ta waiga ta kuma waigowa ta ga ba kowa bale ta arce ta labe a bayansa, ta ga ba dakin buya bale ta shige ta labe sai kawai ta bi bayansa jiki a mace tamkar kwai ya fashe mata a cikin cikinta Daga nesa take kallon yadda gaba daya manyan wajen suka nutsu sunna gyada kai sakamakon maganar da ta kula yana yi da yannayi na bacin rai yana nunawa da hannunsa kafin ta ga ya dago dan yatsansa na kusan babar ya kada ya kuma kadawa ya yi wata maganar da bata fi biyar ba kafin ya ga du sun gyada kawunnansu a tare sunna amsawa sannan ta ga ya juya ya yi hanyar dogon coridon da zai fitar da shi waje A hankali ta sauke ajiyar zuciyata bishi da kallon uma ta gaida asha, sannan a bayane cen kasa kasa ta ce" Who are u?" " Muneerath tunanin me kike, wuce mu je na raka ki wajen motar, mu kam abin ya zo mana da sauki my munnee sai wata haduwar" A dan firgice ta kaleta kafin ta ce" Mu je ina?" Joyceline ta kaleta da mamaki ta ce" tare zaku tafi fa, ya ce kin gama formation din " Muneerath ta girgiza kai ta ce" kai ina, na je ina? Haba kamar mahaukaciya na bi wannan mutumen mu je ina? Nononono ba inda zan je babu inda zani koda da bindiga a kaina, baki ga matse min wuyan da ya yi ba? Hala so kuke ya kasheni? Me na maku? Ku mayar da ni niger na fasa aikin na fasa walahi" Wani katon soja ne ya zo fari ya tsaya ran nan a hade ya ce" Sir zai shiga mota fa mu je " Da ido Muneerath ke girgizawa alamun ba zata je ba, sai dai daga ita har Joyceline din sai suka samu kansu da nufar motar da aka nuna mata zungwui zungwui tamkar zata fashe da kuka har suka karasa aka bude mata ta shiga motar da bata taba tunanin akoy irinta a duniya ba tana ta kyafta ido tamkar zata balo ta bala a guje dan firgici da tashin hankali Ita kadai ce a bayan a zaune a wawakeken wajen, sai direba da soja daya a gaba hakan ya sa ta yi zama irin na zulumi, ta kurawa waje daya ido tana kalo a lokacin da motocin ke sharara wani matsiyacin gudu har suka karasa ainahin gidansa Da ido ta bi shi har ya fice ya shige wannan waje na gilas watau falonsa kafin ta kuma duban sojojin da suka hadu suka baje ta ko'ina a wajen kowane ka kalla ba zaka so kuma kallonsa ba domin fuskokinsu sanye da mask, hannayensu da gam, kafafuwansu da manyan takalma hannayensu rike da manyan bindigun da ta tabata da alburusai na balaki a cikinsu Ajiyar zuciya ta kuma saukewa wasu zafafan hawaye suka zubo mata a hankali ta dora hannunta ta talabe habarta da kumatunta kafin a bayane ta fashe da kuka irin mai karan nan ta ahiga rusa shi tana fadin" Wayo oga, wayo mamanmu, wayo yan uwana ku zo ku dauke ni daga wannan gidan kar su kashe ni, wayo Allahna na shiga ukunna ni ba yar daba ba, ni ba barauniya ba, ni ba karuwa ba, ni ba kisa na yi
Chapter 38 · 0% Book details