Sashe 27
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
11/14/21, 12:46 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
1
A sanyayan da yake tun jiya haka ya yi yar gajeriyar magana ya kashe yana kallon makeken titin baban birnin ingila har suka karaso daidai wajen da yake son sauka
Budewa ya yi ya fita ya shiga makekiyar motar da aka zo daukansa da ita wadda wani soja ya bude masa mai sanye da kaki irin na masu gadin gidan sarautar
Mai taxi din baki hangame yake son gane wai wa ya dauko? Sai dai ina yana kallo aka miko masa kudin da ya tabata ko a wata da wuya ya kama su kafin motocin su ringa tafia har sai da mota biyar ta wuce a gurguje kafin ya sara da hannunsa yana fatan prince dinsu ya gaji babansa dan akoy kyauta sosai
A gajiye yake, sai dai burin ya gansa gashi gasu ya hanna masa jin gajiyar
A hankali ya saka lalausar kafarsa cikin wawakeken falon da wani sojan ya bude masa bayan ya sara masa da yi masa welcom
Idannuwansa lumshe suke sai dai dubansu a kan mahaifinsa yake
Sanyin falon ya yi yawa sosai, hakan ya sa ya fara zarcewa wajen farin gilas din ya dauki remot din AC din dakin su biyar du ya kashe su
A hankali ya karasa yana kallon kan mahaifin nasa da ba gashi ko dis a sama, daga bakin lokacin da gashinsa ya fara zubewa ya daina barin komai kankantarsa a kansa, daga bayama sai ya daina fitowa ko kadan din ya zamana kan taltaltal ba gashi duda tarin gashi irin na baturen mutun
Hannun da mahaifinsa ke miko masa ya bi da kallo kafin gaba dayansa ya kai gwuiwoyinsa kasa ya kama hannayen na mahaifinsa yana kallon fuskarsa a hankali ya saka tasa fuskar a tafin hannayen mahaifinsa
Ajiyar zuciya mahaifin nasa ya sauke, cikin yaren turanci ya ce" Yaya zaka kashe min sanyi ina shan dadina bayan ka san bana jure zafi ka barni na mora kafin na je wajen da ban san ba shin sanyin irin mai daskarar da jinni ne ya daskarar da zuciya da kuma kwakwaluwa ko kuwa tsananin zafi ne mai zagwanyar da fata da hanji da tumbi......." da sauri ya yi shiru da maganarsa sakamakon jin ya matse masa kafarsa da dan karfi
A hankali ya ce" Zaka karya ni kai"
A hankali Hanja ya dago kansa yana kallon fuskar mahaifinsa, bai dauko kamarsa ba aman ya dauko jinninsa, kakarfan jinninsa ya dauko, irin jinnin nan da baka kama da mutun aman ana ganninka za'a ce wannan mahaifinka ne ko danka
A hankali ya ce" Ka daina fadin irin haka "
Mahaifinsa ya kama fuskarsa mai dauke da madaidaicin saje aman bashi da gemu ya ce" Lokacina ya zo yarona, yaushe zaka yarda ka dauki hakuri kamar yadda na dauka"
Idannuwansa ya karra rintsewa muryarsa cen ciki ya ce " Dan ko a da baka son kanka kamar yadda nake sonka"
Murmushi ya yi masa yana kallonsa kafin ya kara rike hannunsa murya cen ciki ya ce" I'm sorry "
A hankali Hanja ya dora kansa saman cinyarsa ya rintse idannuwansa, shin yaya zai kwatanta rauninsa a gaban mahaifinsa? Yaya zai kwatanta irin yadda yake jin zuciyarsa zata tsaya sakamakon zafin da yake ji? Gashi a gabansa ya zo, sai dai ji yake a yanzu ya fi jin tamkar bashi da lakkah a jikinsa baki daya jikinsa ba wani karfi, irin wannan yannayin yake saka shi guduwa sam baya son fuskantar mahaifin nasa, irin wannan sensation din ke saka shi gudun dukan abinda zai hadasa masa bugun zuciya, ina zai iya a girman jikinsa ya zauna yanna kuka? Idan sautin muryarsa ta fito yana gurza kuka ai sai ya tsorata du wani na kusa da shi ta ina ake so abin ya fara ne?
Idannuwansa ya lumshe sakamakon jin lalausan hannunta a cikin gashin kansa mai baiwar baki da santsi da sheki
A hankali ya karra lumshe idannuwansa jin shashekar kukanta kafin ya ji tsugunninta a kusa da shi sai kuma ya ji ta janyo kafadunsa daga jikin mahaifin nasa ta kawo shi jikinta
Duda irin yadda ya girmeta sosai a haka ya karasa jikinta sosai duda ba shine ya rungumeta dan kuwa a cikin kirjinsa take sosai kafin a sanyaye ta ce" Cry, cry bab"
A hankali ya karra rungumarta sosai yana jin hawayen idannuwansa na zubowa, kamar jirra hawayen nasa suke ta yi magana su bale, sun balen kuwa domin nan da nan ya jike mata wajen wuyan abayar dake jikinta da hawaye masu dumin gaske, idannuwansa suka kade sukai jajajir da su sosai
Mahaifinsa kansa sai da ya share hawaye cike da kaunarsa a kasam zuciyarsa, shi walahi a yanzu zai iya rantsewa cutarsa ta daina damunsa kamar irin yadda yaronsa ke tsaye masa a zuciya da kuma matarsa
Hannunsa ya saka daga zaunen da yake ya janyo su jikinsa shima a hankali ya ce" Sai nake gannin kamar muna so mu nuna bamu godewa Allah ba, bayan kune masu taro mutun ku ce ya kasance mai tawakali fa?"
Ajiyar zuciya Hanja ke saukewa kafin ya dago dubansa ya sauke a fuskokinsu, dan murmushi ya yi irin mai ciwon nan sannan dan ya saka su murmushin suma ya ce" Kai jan mutun bai yi ba kun ga yadda hancinku ya yi jajir?"
Daria mahaifinsa ya saka marar sauti kasa kasa yana doke kafadarsa ya ce" Kai ka ga yadda ka jeme?"
Aleesa kam bata iya yin dariar ba sai kawai ta karra barkewa da kukanta wanda ya saka HANJA tashi da sauro ya shiga tsakaninsu ya kama hannunta da na mahaifinsa a hankali ya ce" Mah, kin ga abinda ya sa bana zaunawa da ku, kin ga abinda ke tayar min da hanlali kennan har nake neman fada da shi mu yi na tsere, Mah yaya kike so na yi idan kina min kuka haka? Bana iya hakuri na jure jin kukanki a kunnayena, dan Allah ki yi hakuri ki ji wani zance"