← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 114

Sashe 98

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

gaskiya ta gama cutarta Cike da jin kunya ta fadi abinda ya farun da dalilin kukan na Muneerath tana ji a ranta Idan suka kasance daga ita sai ita sai ta rama walahi! Pah ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" Daughter shine kike yiwa wannan kukan kamar an yi rasuwa?" Muneerath ta ce" Pah, wannan abin ai ba karamin aabu bane, Pah ba abin wasa bane, shin idan ya mutu a irin halin nan fa? Ni kam dan Allah kaa taimaka a kaini gida cen Niger ba zan iya ba, abubuwaan garin nan yanzun na kula so suke su kasheni" Da mamaki yake karra kallonta , tausayinta ne ya ji a kasan zuciyarsa, yarinyar ta yi falng a love , tanaa matukar kishin abin soyayar nata, aman bata sani ba Sosai ya so ya rarasheta ta koma ta kwonta, sai dai wani tunanin shima ya same shi Ba tare da jan abin baa ya bada damar a tayar da Jirgin Masarauta da yake a A roport din bangaren Sarkin daban wanda yake taronsa da sauransu harda jirginsa a wajen , kan za'a kaita gida Iyayenta da suka samu dan lokaci nasu na kansu suka fara fuskantar junna Oga ya ji cewar wai wani yar Oga na kukan a maida ita gida A tunaninsa abin na wasa ne ya ga an kuma tashin Jirgi guda mai shegen kyau da sanyi an zubo au dagaa su sai su bayan sun yi salama sukai kuri a zaune a Hight class sunnaa kallon junna Aun kusan tafiyar awa daya abin ya tuko shi a hasale ya ce" Ke yar Oga dan ubanki ba kin sa an daukomu an ciro mu bamu shirya ba kuma kukan na uban meye kike ne? Ko salon sojawan cen dake cikin baya su zo su kashemu su ce mu muka saka ki kuka? Ashe sojojin nan dake yawo a anguwarmu masu tsaronki ne? Kai mutane Allah mai iko kai kacari ka haifi sarauniya" Mamanta taa ce" wai me yasa kai sai zagi dazu fa na ce maka ba mutunci bane zage zagen nan" Habarsa ya rike ya ce" Yo ni nana abin ne ke karra daure min kai,, kina gannin ikon Allah fa, wai dan ta yi kuka tsakani da Allah sshi jirgin hala da batiri yake anfani ba da esansi ba da za'a ringa tayar da shi saboda kukan yar ogo?" Muneerath da kanta kamar ya rabe biyu dan ciwo cikin kuka ta ce" Oga ka san me aka yi ne? Oga wai yanzu Hanja ashe mata yake bi? Me zai hanna ni kuka dan Allah?" Oga ya zarro ido kafin ya tafa hannunsa ya ce" In ban dake ki ba shege nake sai dai su kashe ni, yau na ga iskanci gannin idona, dan ubanki ubanki ne shi da zaki ringa rizgar kuka dan yana bin mata? Yo Allah na tuba yau talaka fitikma ya bi mata bale mai kudi kuma sarki? Ke ina ruwanku tunda dai sonki yake kawai mu daura maku aurenku mu tarkato mu dawo , halinsa kuma ya daina ko kar ya daina idan ya mutu sai su gana da walakiri!" Ido ta zubaa masa cike da takaici, hakama mamanta, suka rasa abin fada sai kallon kallo, inda Saudat ta mike da sauri ta nufi bayi dan ba zata iya rike wannan dariyar ba kam, kasheta zasu yi ahalin nan walahi. _____________________________________ Yinwar da ya kwasa manta batunta ya yi sakamakon tunani da ya sako shi a gaba Taa ina zai fara yada mata manufarsa? Dole ya hanzarta dan ya fara tsoron mai kiran nan nata shi kam, baya so su saka shi a ha'u'la'i, au saka shi yawo ba riga Sai da ya raba dare kafin ya mike ya dauro alwallah dan gabatar da sallah kafin ya zauna ya buda alkur'ani ya shiga karatu a nutse yana lumshe idannuwansa yana tuno fuskar Mah dinsa Tare da ita suke yi har sunna tsokanar junna idan mutun ya yi wani kuskure a wata gabar Sosai ya roki Allah a kan abu hudun nan Na farko gamawa da duniya lafia Na biyu shiriya Na uku lafiar Mah dinsa Na hudu Allah ya bashi sa'a a kan yarinyar nan, dan ya fara tsoron abinda ta yi dan kawai ya dan rungumeta tana cewa shi sai rungume mata, to idan ta san waye shi yaya kennan? Kai ikon Allah bai taba jin tsoron a san yana aikata zina ba sai yau Da sauri ya nemi da Allah ya rufa masa asiri kar ta ji........to amaan wai kishinsa take ko menene? Allah Allah yake safia ta yi, sai ya saka kayan da ya san dolema ya kasheta, sannan ya fada mata cewa" MUNEERATH ina son ki, ki yarda ki zama sarauniyar Ingila taa hanyar zamowa matata"
Chapter 98 · 0% Book details