← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 114

Sashe 49

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ja da shi sai dai Allah ya kama shi, ke kece ya fi dacewa da ki kame kanki kin ji?" Tsakani da Allah bata gane me yake nufi ba, sam batagane inda ya dosa ba, hakan ya sa take binsa da madaukakin kallo sanann Allah ya haneta cewa me yake nufi har ya fita ya rufe mata dakin Dan tsuru ta yi kafin ta yi murmushi , ita dai bata san da wa yake nufi ba, abinda ta sani shine ya mata nasiha ne kuma ko yaya yake nufi ta ji ta dauka in sha Allah koma waye ba zai cin mata ba Hanja na shiga dakinsa ya kira likitarshi wace ya kasance du garin da suka dira akoy likitocin da suke basu kula Ba bata lokaci ta taho tana isa kofar dakin ta kwankwasa kofar ta dan dakata har ya bata ixinin shigowa Tana shiga a ladabce ta karasa gunshi farawa tayi da auna bp dinshi ya dan hau kadan shine ma ya haddasa karuwar ciwon kan nashi sai kuma ciwon jarabar tashi da bata rabuwa dashi dagowa tayi ta dube shi xatayi magana ya daga mata hannu nuni ya yi mata da tayi aikin ta kawai ta tashi ta bashi guri dan yana bukatar hutawa kan lokacin tafiyarsu ya kusa nan da nan ko likitar ta shiga ta kama aikin ta ta farane da daidaita bp din nashi sannan tayi kokarin ganin ciwon kan ma ya ragu sai yanayin jikin shi ne da bai sauya ba har yanzu to shima dai ta bashi magani sannan ta mishi sallama ta fita tana ta tunanin sauyawar ogan nasu, da da ne zai ce ta zo da su ne ta dauko masa kuwa tsala tsala ya hau kai, bata san ko bashi da karfin hakan bane oho Bangaren yan matan hottest kuwa kowace tana dakinta cikin farin ciki sun san indai suka zo hawai to oga hanja yana basu dama sosai sukanje gurare daban daban na shakatawa da sauransu shiyasa suke matukar jin dadin kasancewar su a k arkashin wannan kamfanin sabida ogansu yana bawa kowa hakkin shi shidin mai alkhairi ne, sosai yasan darajar mutum Suna tsaka da wannan ne sukaji sanarwar kowacce taxama cikin shiri dan nan da yan mintunan zasu juya kuma nan da nan farin cikinsu ya gushe domin basu so haka ba , amma yaya zasu yi ? tuni suka hau shiri murnar ta koma ciki ita dai muneerath dataji ma murna tayi zata koma gun mah dan nan duk a takure take ta bude pizza ta zuba mata ido cike da jin haushinta, ita bata san a kan me suke son abin nan ba, ita yaukima take mata a bakinta , gashi a cikin jirginma abinda suka ci du na cikin leda ne ba zazafawa ba komai malan ita fa kar a rikita mata ciki salon ta samu gudawa a samu na fada! Ta ga haza, aikinsu ashe ba na hutawa bane? Sai da suka kuma daukan doguwar hanya doguwar tafia sunna tsaye kan kafafuwansu , tun tana gane rabon kayan da kulawa da bukatar Hostess da sun nemi hakan da kwari kwari irin abin nan na farkon shiga har ta dawo yi da salo salo ga tarin gajiya na ciciyarta Sun samu kusan wuni kafin suke sauka, wannan karronma sai da akai masu su test na cutar nan Corona kafin a barsu su fito Cike da mamaki take kallon dogarinta kafin ta tafa hannu ta ce" Wai dan girman Allah zuwa ka yi ka dawo ko dama kana nan?" Shi dai kikam ya kasa bata amsa, to shi me zai ce mata dan Allah su da ba magana suke da iyayen gidansu ba ita kuma sai ta ringa masa tambayoyi dab Allah bayan ana sauraronsu kuma ana kallonsu ta camerar dake jikin rigarsa daga cen Palas ? Bude mata motar ya yi ta shiga tana sinsina hamatarta ta yi murmushi a bayane ta ce" ashe warima dan zahi ya mana yawa muke yi, ka ga na wuni na kwana a hanya da kaya daya kwalin kwal ban cenza ba , ban yi wanka ba aman kuma kanshin turaran da Mah ta fesa min bai fita ba ka ganshi yana nan, koda yake na san turaran ya sayi tanadin oga aman kuma ai ya ci ace na yi dan tsami tsami kadanma kau? Wannan karron ya so ya juyo ya kali wannan budurwa, aman tsoro ya hanna shi sai ya dake yana kallon titi shi kuwa direban yana tuka su shima tamkar wani status aikinsa kawai yake.................(Sauka lafia yar Mah) Idannuwansa har nema suke su rufe dan abinda yake damunsa, a wannan lokacin ya manta jawaban mamansa da na abansa, a irin wannan lokacin ya manta komai da kowa domin da sauri magannin nan ya sake shi hakan ya sa tun yana hanya ya bada damar a turo masa mace biyu wa'inda zasu iya daukan lalurarsa kafin yake shiga motar da ta je daukansa ya bada umarnin a kaishi gidansa A haka suka nufi gidansa duda Mah ta bada umarnin a kawo mata shi gida ne, Da kyar ya iya bude idannuwansa yana mai bale botiran rigarsa tun daga cikin motar kafin ya sako kafarsa waje ya fito yana dan son bude idannuwan nasa ya hango su tsaye dan sunna gannin shigowar motocinsa suka fito daga cikin motar da ta kawo su itama wuleliya da ita cikin shiga ta dogayen wandunna dan ya hanna dan za'a kawo masa abin cikin pant a kawo masa shi a bude, fita yake a ransa............................................. A hankali yake takawa bai yiwa kowa magana ba ya nufi ............. 11/14/21, 12:50 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 49 · 0% Book details