Sashe 26
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
dan yar lakar dake kasansa idan suka tasheta?.....wannan nutsewa da ta yi dan son gannin ainahin tsayinsa shi ya kayarwa da kowa gaba, a zabure Ameerah ta matso kusa da ruwan lokaci daya tana kallo tana kuma bale botiran gaban rigarta sannan ta danna a bin dake cikin kunnenta da zai sadata da office din Shugaban makarantar a dan tsorace sa furuci rake shaida masa ai yarinyar nan ce ta fada ruwa da baya gashi kusan minti uku bata fito ba bata bayana ba su a hangenta da suke ta yannayin kalan suturar cikinta kamar wace ke kara shigewa kasa ne Shi dinma a tsorace ya fice da gudu gudu da kuma equipe din dake ciro da mutun daga cikin ruwa suka nufo wajen, a lokacin yan matan du suka yi cirko cirko kowace a tsorace suka jira su ga ta ina za'a ciro da gawarta? Domin su dai a TV suke gannin mutun na iya daukan dan lokaci a kasan ruwa, kai yawancinsuma a cikin irin film din Sirene suke gannin hakan dan basu taba ganni ko ji a labari cewar mutun na iya rike numfashinsa a kasan ruwa ba, ta yaya? Ya rike numfashinsa kuma ya jima a ciki? Wannan sai SARAKAN RUWANMU NA GALGAJIYA..........sai ko wanda ya dauki lokaci mai tsayi yana faman koyon hakan Sunna zuwa ya ringa jin hankalinsa na neman tashin da zai fara rufe kowa da fada a wajen, a hankali ya ringa rike kansa ta hanyar yin tambayoyi da hannayensa, gannin Ameerah na cire kayanta hakan na nufin tana gaf da fadawa ne A kausashe ya ce" Kai tsaye kika sakata shiga ruwan bayan kin san baban burinta ta zamo Hottest ne ba zata yi maki gardama na shine kika sakata shiga ba tare da kin duba faiblesse dinta ba , ba tare da kin gaskata idan zata iya shigarsa ba , ba tare da kin kaita ta fara shiga wancen marar zurfin ba?" Bakinta na rawa cike da tsoron kar dai ta kashe yar mutane ta janyowa kanta hawa media da balakin duniya baki daya da rasa aikinta da rasa komai nata ta budi baki zata yi magana a lokacin ne kuma du sun gama shiryawa dan bin bayanta sun saka abin numfashi a kasan ruwa dan a yanzu mintinta takwas har da yan sekwani a cikinsa sai dan buiiiiil dake dan fitowa jefi jefi a nesa da nesa da ba za'a taba kawowa cewar itace ke iyo da gudun nan ba , Ameerah ta budi bakinta dan ta kare kanta suka ji yan matan sun kwala ihun "Gata nan gata nan" Da sauri Ameerah ta juyo , haka shima da sauri ya taka ya matsa yana kallon wajen da ta fito din, ta tafi cen fiye da rabin ruwan kuma bayanta suke gani gashin kanta ya warware ribom dinta da dan kwalinta sun zube a cikin ruwan gaba dayansu , bakin gashin kanta ya malalu a cikin ruwan , ruwan ya dago shi haka, kafin ta juyo a hankali tana karra kallon ruwan cike da shinfidadiyar fara'a ta jin dadin jinta kwalim a cikin ruwa, dan tana matukar jin dadin ta jita a cikin ruwa a rayuwarta A hankali ta ringa binsu da kallo su dinma ita din suke bi da kallo, idan bata manta ba da zata shiga babu wadinnan tarin mutanen, hakan ya sa take kallonsu da mamaki sai kuma jin da take sunna cewa "Da ranta, abin mamaki, da ranta" Idannuwanta ta kifta ta shafa kanta, sai kuma ta zarro idannuwan nata da dan daga murya ta shiga eaige waige tana karra tatara gashin kanta a bayane ta ce" dan kwalina, Ribom dina...." da yaren hausa kafin ta hango dan kwalin nata ya yi sama sosai kasancewar na raga ne , ribom din ne ya sha ruwa ya yi dan kasa kasa domin baya sama Tsayin da dan kwalin yake akoy nisa kadan, kafin su ankara ta nufi wajen tana wana kafafuwanta da hannayenta ta kwaratiyar kwarewar iya ruwanta har ta idawa wajensa ta kamo shi ta rufa a saman kanta tana karra kallon mutanen da yar yatsarta ta nuno masu ta dan daga murya ta ce" Minti daya zan dauko ribom dina " Bata tsaya ta ji amsa ba ta yi kasa abinta, a tare suka kalli junna da ameerah da Sir Ameerah zata yi magana ya girgiza mata kai ya mata nuni da su je sannan ya salami wa'inda zasu bita cikin ruwan ya rage daga daliban sai ita suma sunna jira ta fito sun yi cirko cirko aman a yannayin fuskarsu yannayi ne na mamaki da sakin fuska Bata jima irin na dazu ba ta samo abinta ta fito, tana fitowa ta nufo su ta kama katangar tana kallonsu Wata mai sanye da wani tsohon kashi na punichment wato symbol wanda kana yin hausa za'a rataya maka shi du inda zaka shiga da shi zaka shiga gashi har wani dan wari wari yake na wuya du dan ka daina yin hausa ta duko tana dariya ta rataya mata da yaren freinch ta ce" Muna maki oyoyo a gidan HOTTEST" Gaba daya suka saka ihun daria wanda sai da ta zabura sai kuma ta kura masu ido ta ga sunna ta daria, a hankali ta ji wani farin ciki da murmushi na wanzuwa yun daga cikin zuciyarta har saman fuskarta Du zama suka yi a waje ruwan kowace na jefo mata tambayar a ina ta koyi ruwa, a wani club aka koya mata, waye ya koya mata dai da sauransu........ Kallonta yake tana kai kawo kafin ta tsaya, har yanzun hannayenta rawa suke muryarta na rawa ta ce" Baka tsorata da irin iya ruwanta ba? Wa ya aikota? A ina aka koya mata ruwa? Wai shin anyama mutun ce? Iyayenta da suka nuna halin ko'in kula da kasancewarta tare da mu su suka haifeta kuwa ko kuma an saka su nuna su suka haifeta ne?" Rai bace ya ce" Ya isheki haka, zaki rufe min tabarmar kunya da hauka ne? Yau da wani abu ya sameta na sakakinki ko tsanarta da kika dorawa kanki ta dalilin da ban ko na meye ba me zaki ce?, kina da bakin kare kanki ne ko zaki ce baki san lokacin ba ? Da kin ja ba kalacin ke ba ni kaina an maka ni a kaso na sakena da na yi na baki amana a kan y'ayan mutane! Nan fa ba filin daga bane, ba filin tsanar junna bane, ke kin san yanzu aka fara idan an saka su dakin da jirgi yake yaya kike tunanin koyar da su aikin da ya fi wannan tsauri?, idan kin nuna iyayenta an fada masu su ce su suka haifeta mutanen anguwa da makarantar da ta yi da doguwar takardun tarihin makarantun da ta yi da kawarta dake kuka na jin ana bincikarta duka mugayen da suke son cin mana ne suka tsara haka?........ina gannin kin fasa tunani da kwakwaluwarki sai da kanki!" Rai bace ya barta nan tsaye ya koma wajen computer dan karra bincike a kan lamarinn Muneerath~~~~~~~~~~~~ _____________________________ Girgizar da jirgi ya yi da shi ya saka shi karewa jirgin kallo a lokacin da ya samu kafafuwansa a kasa a baban birnin garin da mahaifinsa yake sarki Da sauri ya saka hular rigar darin dake jikinsa dan ya kare kamaninsa dan kar a gane shi a masa caaaaaaa gashi tafiar ba zata ce au kansu sai sun duba zasu ga harda shi a cikin jirgin da ya kawo pasingern yau ba Idannuwansa ne suka sauka a kan wani datijo yana tafia a hankali, tafiar irin idan ya cira kafarsa guda kafin ya cira dayar sai ya jima kuma a dukan yannayin tafiarsa zaka gane cewar a wahalce yake yinta A hankali ya dan girgiza kansa ya juya ya fita kwata kwata ya tsayar da makekiyar motar da ake taxi da ita a kasar ya yi bayanin wajen da za'a ajiye shi domin taci bata bin hanyar palas A hankali ya jinginar da bayansa ya ciro blok note dinsa da byro ya bude a shafin ranar ya rubuta da manyan harufa kamar haka......" *ASHE KO BABU MUTUWA, TSUFAMA AYA NE* ", rubutun ya kurawa ido yana kallo kafin a hankali ya rufe ya rufe golding brnsa ya saka a gaban aljihun wandonsa ya dauki karamar wayarsa ya danna kira ya karra a kunnensa a sanyaye ya ce"