← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 114

Sashe 47

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

soyayar Jirgin ke ratsa gaban jikinta Tana taka matatakala tana hawa ne zuciyarta na kwadaita mata son gannin yaya cikin yake har kasan zuciyarta A lokacin da ta tsinci kanta a ciki bayan sir ya rabawa kowa irin aikin da yake so ya gabatar ya nemi fa ta biyo shi ita da take bakuwa ya shiga cen ainahin wajen da pasinger zasu zauna sunna tafe yana mata bayanin komai har sai da suka raba tafiar suka isa tsakiya sosai sannan ya juyo yana fuskantarta Murmushi ya dakar mata mai daraja kafin ya ce" kin daina kukan?" Muneerath ta daka fuska ita a dole haushinsa take ji domin yana kallo aka ringa wala gigi da ita ana mata tambayoyin mararsa da'a bai tsawatar ba, bama wannan ba tunda ta sanar masa tana Palas rabonsu da su yi wani zance sai fai su gaisa sama sama ya shaida mata a Palas komai na fara bi ta wajen dakin computern da ake binciken mesg ko call din du wanda ke cikin gidan more spcialy na kusa da sarkin, hakan ya sa ya daina dogon surutu da ita dan kar magana ta kai kunnen Hanja ya ce meye tsakaninsa da dalibarsa? A sanyaye ya ce" Fushi kike da ni? " Muneerath ta kawar da kanta gefe bata bashi amsa ba hakan ya sa ya ce" Yanzu kin iya girki? " . Muneerath ta juyo da dan sauri tana murmushi kafin ta gyada kanta ta ce" Yanzun ni nake dafawa Mah shayinta ta sha ta more" Murmushi ya mata yana gannin bai taba gannin mutun mai chance irin nata ba, kwarai yarinyar da Allah dogara Allahn kuwa sai yake dafa mata a dukkan lamuranta A nutse ya ce" Mutun ne da ya dauki aikinsa da daraja, yana daya daga cikin wa'inda suka malaki jirgin kansu a kasar nan da basu fi su uku ba, yana da arziki mai yawa, ya fara tuka jirgin fa ya kera da hannunsa na wasa kamar da wasa, a harkar da ta shafi jirgi harta yadda za'a ba pasinger kulawa ya karanta, son abin yake a zuciyarsa ba wai haye ne ya yi dan ya yi arziki ba, aikin nan ba aikinsa bane ya saka kansa ne dan yana so, ina girmama mutumen nan domin idan kika ga ya yi fada da dalili , kar ki dauki tambayoyin cen da wata manufa dukkan bakuwa haka ake yi mata wannan din ba wani abu bane dan a san irin aikin da ya dace da mace ne, domin idan kina da yaro a san irin doguwar tafiyar da ta dace da ke, idan kina da aure haka, idan da saurayinki kike rayuwa haka, Muneerath daga bakin wannan lokacin kin zama karkashin kulawar kampanin nan, idan baki da lafia sune, idan wani abu kike so sune, cin ki, shan ki, suturunki, bukatunki, wajen kwonciyarki baki daya a wuyan kampanin nan ne, basu maki dan wata manufa ba......ana yin tambayiyin nan ne dan a tantance waye kai da irin aikin da ya dace da kai kin fahimta?" Sai a wannan lokacin Muneerath ta samu wani nutsuwa a zuciyarta, sai a yanzu ta ji hankalinta ya kwonta harma ta ji kunya na son lulube mata zuciyarta domin sai a yanzu ta ga rashin dacewar kukanta hakan ya sa ta rufe fuska tana murmushi ta ce" Tambayoyin ne sukai min kama da wada ake tuhuma da aikata hakan" Murmushi sir ya yi yana girgiza kansa ya ce" ba maganar tuhuma, bama wannan ba har yanzu dogarin ake jira?" Muneerath ta ji batu an tabo mata zushiya sai ta murmusa ta langwabar da kai ta ce" Uhum, ka ga dai sai tsofewa nake bai motsa ba, aman na san da na koma niger zai yi bayani ne na tabata sai ya rikice a yanzun dan na iya saka kwali..." Ta fada tana murmushin tuna aminiyarta amina dake fadan ko kwali bata iya sakawa ba wani namiji take so yace yana sonta wadinnan mazan na yanzu da kyalekyali ke wartarsu A kadan zuciyarsa yake ayana' inama za'a bani ke, da na dauke ki mun ringa yawon kasashe, ni kam bana sonki da kwalin a haka kin fi min kyau, aman na san zaki amsani idan na fada wata rana' Kawar da tunanin nan ya yi gannin lokaci ya yi yanzu an fara kiran mutane su shigo ya ringa nununa mata wajen da mutane ke iya boye miyagun kwayoyi suka zarce har bayi ya nuna mata da irin mu'amalar da ta dace tsakaninta da pasinger kafin su koma su yi jiran jirgi ya gama cika , aka bata abin aunawarta tana tsaye abinta zuciyarta fesss da farin cikin wannan rana ___________________&________________ Kafin ka yi tafia ne kake da ita, idan ka yita ita take da kai, a wannan tafiar tasu sun sauka lafia a kasar malesia inda suka yi hotel din dake jikin a roport din dan samun hutu na dan lokaci kafin su daga zuwa gida, sai dai basu kai ga hutawar ba aka shaida masu tafiarsu zata dauki hanyar HAWA Sakalau ta yi tana kallon yadda suke murnar zasu sauka a Hawa , ita dai bata san ina ne haka ba, abinda ya fi birgeta shine rabata da kwonciyar nan da aka yi, domin ita fa bata gaji da aikin ba, abin kasheta yake gata itane take wannan aiki, kai yaya Oga zai ji idan ya ganta a haka? Mamansu fa da tace bata da hankali idan ta ga yau gata tana wannan aiki? A yanzunma shine ya tuka su, ba su su sauka a kasar ba sai da sanyin safia gashi su basu rintsa ba Hakan ya sa sunna sauka wajen kwonciya aka fara gabatar masu domin basa tare da yinwa Dakuna ne a laye, daga su har ogan nasu du aka umarci yan matan da su shiga su huta Da ido ta raka bayansa da kallo a lokacin da yake tsaye a kan dokin kofar dakinsa da waya a hannunsa dayan hannun nasa kuwa yana dafe da cikinsa wanda ita bata gane cewar mararsa yake rike da ita ba, ga kansa tamkar zai tsage biyu A hankaki ta fara nufar infa yake tsaye, so take ta ari wayarsa ta yi kiran Mah ta shaida mata ga inda suke domin ta fada mata da ta samu sarari ta ringa sanar mata inda suke domin ta bata katin numberta ta gida wace ake samunta direct A hankali ta tsaya dan nesa da shi kadan ta budi bakinta a sanyaye zuciyarta na dokawa da tsoron kar a je ya mata wani ihun ta ce 11/14/21, 12:50 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 47 · 0% Book details