← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 114

Sashe 91

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

sai da Hanja ya yi kuka du rashin imaninsa kuwa !" Mamanta ta hae girar sama da ta kasa tana fadin" Je ki shirya bara na sa yayanku ya kai min y'ayana gidan yayana kar kafin mu dawo na tardo sun bar kasar sun tire!" Oga ya kankance ido ya ce" Da alamu kin manta ni ne ubanta kuma ke kuwa a karkashina kike, dan haka ba inda zaku" Muneerath ta riko hannunsa kanta na sarra mata a hankali ta dora kanta a gefen hannunsa tana murzarwa zafin da kanta ya dauka na shiga hannun nasa muryarta a mace tana fadin" Oga dan Allah ka barni ka ji aban Muneerath ?" Hanci ya ringa bugawa yana hararen gefen Mamansu da ta yi gaba ta shiga kimtsa y'ayanta da hada masu kayansu dharda na islamiyarsu sannan tana neman layin danta dan ya zo da motar da ta siya ta sakar masu ya kai mata y'ayanta cen a kula mata domin ba zata iya iya barin Muneerath ta tafi ita kadai ba walahi, kuma da ace bata ji irin kalaman da suke fadawa junna da irin tada hankalin da yarta ta yi a daidai gabar nan da suke kaunar junna take jin son yarta tamkar ranta da ba zata barta ta wani je ba, sai dai a yanzu suke karra sannin junna dan haka ba zata bar abinta ba gaskiya zata je kafarta kafarta Sun yi tafia mai nosan gaske, mai daukan lokaci Sunna sauka Sir Attahir ne da kansa ya saka aka dauke su sannan ya shaida zuwansu Palace din dake rikice wanda gaba daya da kyar ya iya samun damar a barsu su shiga da adadinsu Gaba daya jikinta karra yin sanyi yake a lokacin da suka durfafi palace din Bayan sun samu shiga sam ba ta iyayenta da suka rude da kasar da gidan da matakan tsaro take ba Da gudu gudu ta shige motar palace din ta umarci a kaita asibitin palace din ta bar Oga na kiran sunnanta A lokacin da ta saka kafarta baban filin idannuwanta suka yi arba da abinda take iya kira baban tashin hankalin da bata taba kawowa ranta ba Da karfi ta rufe idannuwanta ta kuma budewa a kan gadon da ake son turawa da mutun sama rufe da farin abin rufa wanda Pah dake tsaye a gak da HANJA suka zubawa gadon ido haka kuma Iman dake tsaye gaba daya ta yi jajajir dan birkicewa itama ta bi gadon da ido har aka tura shi aka shige wani dakin dake hanyar coridor din watau daki ne na tiyata ko na meye oho A hankali take daga kafarta, jikinta sanye da atamfa mai ruwan ja mai dan duhu an yi mata dinkin riga da sket wanda ya mata dasss a jikinta ya kamata sosai a jikin nata ya fitar da dukan wani yannayi na kyau da tsarin halita a jikinta A hankali ta tsaya a gabansu idannuwansu suka ringa sarkuwa da na junna har ta sauke dubanta a kan HANJA wanda suka tsaida dubansu tsai ido cikin ido sunna kallon junna A hankali ta motsa lebenta dake naturel baya dauke da ko man lebe tana kallonsa cikin ido ta ce" Me yake faruwa ?" Idannuwansa da yake ji sun gama kyekuashewa ya lumshe a hankali ya kuma budewa a kanta Dukan da zuciyarsa ke masa da halin da mamansa ke ciki na rayuwa ko mutuwa da kuma ganninta da ya yi a irin wannan lokacin na ba zata a gabansa sai ya ji zuciyarsa na kakaryewa Dukan da zuciyarsa ke yi da kuma irin yadda yake neman jin wani sa'ida da ganninta ya saka shi daga kafarsa a hankali ya matso daf da ita daidai lokacin da sojan da doreban da ya rako su Oga suka karaso daidai lokacin HANJA ya aikata aikin da ba wanda ya kawo haka a ransa, domin ita kanta wace ya aikatawa hakan bata taba tunanin haka daga gareshi ba a daidai lokacin da ya mika hannunsa ya damko nata ya janyota da karfi ya bata wata wawar rungumar da ta cuje dan kwalin kanta ta saki yafar da ta yiwa jikinta da mayafinta fari kal ta yi kasa kasa dan firgici da tsoro ta yi baya baya aman duka ya tarota a jikinsa ya kara rukunkumeta da rukunkumewar nan mai neman karya kashin bawa inda su OGA, da MAMA, da IMAN, da PAH , da dukan wani dan adam din dake wajen ya zarro ido kafin da sauro sojojin wajen su aniya neman kare hakan da tare Oga da ya zarro ido a zuciyarsa ya ayana' Kuturu uban meye wannan kuma' yana neman karasawa ya raba wannan garjejen jan mutumen da yarsa, a daidai lokacin da itama take mutsu mutsun son kwatar kanta idannuwanta duka a waje muryarta har tana rawa tana son ambatar sunnansa aman bugun da zuciyarta ke yi ya tsananta ta yadda ta kasa fitar da koda kalma daya ce saima jin lalausan sajensa na gogar gefen fuskarta muryarsa cen ciki sannan yana fuzga haka kuma yana goga mata sajensa ba da wata manufa ba sai dan neman inda zai saka ransa ya ji sanyi ya furta" TSORO NAKE JI, I'M AFRD MUNE..................... MUNEERATH ...........MU...... MUNEERATH MAH, MAHNA MAH............. " SAKAMAKON LABARINA NA KUDI MAI TAKEN *WATA KOKOWAR* DUTSE ZAI RINGA ZUWAR MAKU LITININ DA ALHAMIS KADAI IN SHA ALLAH.......... .. .... KI GARZAYO KI YI RGST YA UWA DAN SAMUN NAKI CIKIN AMINCI IN SHA ALLAH........DAGA ALKALAMIN SAJIDA 11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 91 · 0% Book details