← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 114

Sashe 24

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
1
*GODIYA TA TABATA GA ALLAH SUBAHANAHU WATA'ALA, DUBUN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI YA TABATA A GAREKU MUTANEN KWARAI DA ALLAH YA HADA MU DA SU BAMU SAN JUNNA BA AMAN MUKE KAMANTA KYAUTATAWA JUNNA TA HANYAR ALKHAIRAI DA DAMA, JINJINA A GARE KU MUTANEN GIDAN DUTSE ........A DUNIYA DU WANDA YA TASHI YA YABA MAKA DA ADU'A MASOYINKA NE, KU HARDA KOKARI TA HANYAR MOTSA ACCT DINKU KUKAI MANA KYAUTA KUKA CE A SAKA KATI A YI DATA, TO BARA KU JI MAMAN JARIRI TA CE KAZI ZAMU CI ALKUR'AN
......, KUN GANE, MUN GODE, BAMU DA BAKIN GODIYA SAI ADU'A A GARE KU, ALLAH YA KARRA MAKU BUDI YA KARRA RUFA ASIRI DUNIYA DA KIYAMA DA WA'INDA SUKA SAMU DAMAR SAKAWA DA WA'INDA SUKE DA NIYAR SAKAWAR ALLAHNE BAI YI BA, DA WA'INDA SUKA LULUBE MU DA ADU'O'I NA FATAN ALKHAIRI BAMU DA BAKIN GODIYA SAI DAI MU CE DA KU ALLAH YA KARRA RUFA MAKU ASIRI DUNIYA DA KIYAMA AMEN.....MR SPECIALLY AMINENENMU, DA ALEESA DA SUKA JAGORANCI WANNAN CONTRIBUTIONS, DA SISINA MAH SISI, HAJIATA, SISINA SIS BILKISU KANAR DA TA CE SAI AN AMSA AKA KUMA AMSAR DAN TA ISA, SAI MARUBUTAN DA SUKA NUNA FARIN CIKINSU HAR SUMA SUKA ZUBA DAN KARRIN KWARIN GWUIWA DA TAYA MU MURNA, DA MAS7 HALIN DATAKON BAYIN ALLAH DA SUKA ZUBA SUKA CE A BOYE.....ALLAHU YA BARMU TARE, YA SA SOYAYAR DA MEKE YIWA JUNNA DOMIN ALLAH CE WACE ZAMU SAMU KYAKYAWAN SAKAMAKON A RANAR KIYAMA AMEN....... DAGA BAKIN MAMAN JARIRINA WARAI SAMIRA HARUN...DA NI SAJIDA KULEY DAN BUZUWA MUNNA MASU YI MAKU FATAN ALKHAIRI DA ADU'A TA DARAJA DA FATAN GAMAWA DA DUNIYA LAFIA AMEN*
Sosai ya ari jarumta dan ya iya tsare dukkan yannayin da zai nuna mata da al'amarinta na neman saka shi a hali na tunani ya ce" Zamu koya maki a nan"
Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta karra rage muryarta sosai ta ce" Ka ga ita wannan din me yasa ta cika fada? Ni kuma tunda na ganta da sket a tsage uwa karuwa na ji bana sonta"
Dan gimshewa ya yi ya yi gyaran murya ya karra hade fuskarsa sosai ya ce" Yanzun na gama ce maki dole ki darajata, kina so mu fitar da ke a nan ne? "
A hankali take girgiza kanta ta matsa ta yi tsaye tana kallonsa
Mikewa ya yi yana sauke ajiyar zuciya a boye kafin ya juya ya bude ya mata umarnin ta shigo
Tunda ta shigo take son gannin wani abin da zata ce Muneerath ta mata aman bata ga komai ba, hasalima tunda ta yi tsaye a gabanta da yaren freinch tana yi tana jefo turanci a ciki tana mata bayanan dukan abinda ya zama wajibi ta kiyaya kanta a sade tana gyada mata kai cike da ladabi har sai da ta gama sannan ta bata minti talatin dan ta je ta kimtsa jikinta ta dawo
Kayan ta dauka cike da ladabi ta tambayi inda zata je din?
Shi dai yana jingine da garun yana kallonta, nan ta yi gaba ta ce ta biyota
Sai da ta dan dago ta saci kallonsa kafin ta bi bayanta jikinta a mace aman a kasan zuciyarta cike take da yannayi biyu masu karfin gaske
Farin ciki da murnar sabon al'amarin da ya sameta sai kuma yannayi na rashin jin dadi na irin yadda iyayenta suka banzatar da ita, aman kuma idan ta tuna ta fara taka matakin samun dogari sai kawai ta kawar da kai ga dukan damuwarta ta fawalawa Allah komai
A haka ta sadata da dakin da zai kasance nata har barinta a gidan baki daya
Dakin dauke yake da bed daya madaidaici, sai wrdrb da wani irin sif dauke da kayan kwaliya bitjik, sai madubi tafkeken gaske wanda zaka iya kallon kanka a ciki
Dubanta ta maida wajen bayin a hankali ta karasa ta shige da adu'ar shiga bayi a bakinta
Tsayawa ta yi tana kallon yadda bayin ya hade, ba wani mai girman a zo a gani bane aman irin tsarin da aka bashi ya isa ya birgeta duba da nasu bayin na gidansu yadda yake
A bayin kama daga abin wanke masai, da su Hypo da clean, da tsintsiyar wanke bayi, da soson wanka da broch da maclean , da sabulun wanka da na wanke gashi, da abin wanke kafa da abin aske gashi, da su abin jona turaran ruwa da na wuta kusa da soket dinsu
Komai a kilace yake harta da tawul kwaya biyu a ninke suke
A hankali ta idasa shiga tana karra bin ko'ina da kallo kafin ta gyara tsayuwarta ta kai dubanta wajen kayan wanke bayin, ba wani dati gareshi ba, aman haka ta maida hankali da gagawa ta shiga wankinsa, tana yi ta jona abin turaran ruwan sannan ta ci gaba da aikinta
Sai da ta gama tas sannan ta dauko tawul din masu dan girma ne dan zasu iya kawo mata cinyarta idan daurin kirji zata yi da su
Su dinma wanke su ta yi tas da hannunta bata saka su a washing machine ba ta shanya su a igiyar da ta gani duda ta cika da tunanin ta yaya zasu bushe a haka duba da nauyinsu da kuma yannayin wajen a dan matse ba iska bale rana
Daidai da pant dinta sai da ta wanke shi da rigar da ta cire tas sannan ta zuba ruwa masu zafi a bokicin ta dauki soson wanka sabo ta saka shi a ciki, harta da brush din wankin bakinta da macaji sai da ta dafa su da ruwan zafi kafin a gagauce ta yi wanka ta wanke bakinta sosai kamar wace zata dawo fara haka ya dirji fatar jikinta sannan ta ringa sanda dan fitowa domin ta wanke komai nata ta shanya bata sanye da komai a jikinta
A hankali ta bude ta leko kanta gashin kanta na digar ruwa ta duduba sosai, gannin hajiar dinkim ta yi waje ya sakata fitowa da sauri tana adu'ar fitowa a bayi a zuciyarta ta nufi kayanta
A gagauce ta saka suturar da aka bata cike da mamakin yadda ta rike mata jikinta taf bale wandon shi ya fi kamata du irin fadinsa ya rike mata kugu taf aman kuma na kaushu ne domin jayuwa yake sosai sai dai wata irin kunya ta sakata ja ta tsaya tana karra bin jikin nata da kallo tamkar zata fashe da kuka a bayane ta ce" Anya kuwa zan iya da matsalar fitar da tsiraici? Dama zasu amince min su bani wa'inda suka fi wannan girma da sun taimakeni"
Gashin kanta ta kama ko bushewa bai gama yi ba ta hade shi sosai ta dunkule shi cikin ribom ta masa dauri kamar na huhun goro sannan ta dauki dan kwalinta ta yi jeka ka dawo da shi ta daure kan nata taf kafin ta ringa sauke ajiyar zuciya tana kallon madubi sai kuma da sauri ta kalli agogo
Idannuwanta ta zarro dan ta karra mintunna har ashirin da bakwai a kan wanda aka bata..................................................
11/14/21, 12:46 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 24 · 0% Book details