Sashe 50
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3 "Assalamu alaika " ta fada a sanyaye sannnan a irin ciki ciki dinnan Sai da ya yi tsam dan tabatar da a bayansa ne aka yi salamar kafin ya juyo a hankali yana mai cire hannunsa daga wajen da ya dora Watau saman mararsa Yana juyowar idannuwansa suka sauka a kan pankamemen kugunta, da sauri ya yi sama da dubansa ya kai saman fuskarta,, mamaki ne ya kama shi lokacin yaga itace tdaye firit a gabansa, a cikin zuciyar sa ya amsa sallamar tata kallonta yake yana jiran yaji dame kuma tazo shifa ya fara tunanin ko gamo yayi agarin kwashe kwashen shi na mata Bai dawo daga duniyar tunanin ba ya tsinkayi muryarta mai sanyi da dadin sauraro tana cewa" Dan waya nakeson ka aramin zan kira mah " Mamaki ne ya kara kashe shi wai shi take cewa ya bata wayan shi? ikon Allah, ikon Allah, shin wai ba ita ce ya damki wuyanta ba? Ba itace ta masa fitsari a mota ba? Ko ba ita bace yanzun ta gama sheka kuka? hannunshi ya kalla wanda wayar tasa ke ciki kafin ya kalle ta, kai shikam wllh badan m Mah ba da ya batar da yarinyar nan a garin kawai kowa ma ya huta Tsintar kansa ya yi da mika mata wayar batare da yace mata komai ba yana kallon ikon Allah, hakama Sir da ya taho da servic din da suke kawo pizza da samari uku a bayansa ririke da katan katan din pizzar ya samu kansa da rage saurin da yake ya zubawa bayanta ido da kuma tsayin HANJA da ya kereta yana jingine da jikin garu gashin kansa ya yo gaba ya kurawa Muneerath din ido hannunsa kuwa ya miko mata abinda shi dai bai san ko menene ba, haka kawai ya tsinci kansa da faduwar gaba har ya ji kamar ya kasa idasawa kofar dakunnan nasu Ita ko muneerath kanta tsaye ta karbi wayar ta juya cikin takunta mai birgewa wanda idan mutum bai santa ba zai yi tunanin cewar da gangan take karkada bombom dinta , ita kuwa baiwar Allah abin ne ya mata pantsam a bayanta kuma ba hadaden nan bane yana juyinsa ne da an bashi damar hakan watau da an motsa da shi Sam ba da gangan ya yi jiran ta juya ya bita da kallo , hasalima da ya san idan ta juya iya shegen da zata yi kennan wanda shi ya dauka kan da gangan ne ta yi haka da bai tsaya mamakin ta amshi wayar tasa ya nemi bita da kallo ba Mutuwar tsaye ya yi yana kallonta tuni zuciyar shi ta ringa bugawa da sauri da sauri, mararshi ta amsa lokaci guda ya runtse idanuwan shi da sukayi ja dan azabar ciwon kai da jarabar da ta sako shi a gaba baiyi auni ba tsabar ya lula duniyar tunani bai ma san mintuna nawa ta dauka tana wayar ba sai jin sassanyar muryar muneerath din tana yi masa godiya tare da miko masa wayar Idannuwansa dake rintse ya bude da yannayin magagi magagi ya kai hannunsa dan amsar wayar shi, a rashin sani carab ya hade da hannunta, Munnerath a birkice ta daga idonta ta kalle shi gabanta ne yayi mummunar faduwa lokacin da taga cikin idanuwan shi , 'innalillahi wa innah ilaihirraji' un' abinda ta ke furtawa kenan a kasan zuciyarta nan da nan jikin ta ya hau bari dan walahi idannuwansa kadai ita ta gani aman sun mugun tsoratata dan ita bata san idon mutun na yin duhu dan ja ba sai yau kamar wanda aka tsikara ya saki hannun nata da sauri ya juya ya fada dakinshi muneerath kuwa juyawa tayi kamar wanda kwai ya fashewa a ciki cike da tunanin shi kuwa ciwon ido ne ke damunsa haka har haka? Dakinta ta shige tana mai kai duwawunta saman bed ta zauna tayi tagumi da hannunta ta shiga tunanin to ko ta fadawa Sir Hanja ciwon ido yake? , Sai kuma ta shiga tunanin shin a ina zata ga Sir din kamar dazun ta ganshi kuma sai ta ga wayam baya nan ........a hankali ta zubawa hannun nata da hanja ya rike ido batasan lokacin da hawaye suka fara xuba a idanunta ba , a hankali ta fara fadin" Na shiga uku na lalace aka, Mah ta ce ciki na shiga da namiji ya tabaka......" Mai yasa ya rike mata hannu mai kuma ta kara yi masa?, Itadai tasan wayar shi kawai ta mika mishi kuma banda kalmar godiya ba abinda tace to ko dai kalmar godiyan ma laifi ne tayi bata sani ba oh ita yar oga ta kawo kanta wata rayuwa mai cike da abin mamaki, yanzun tabatan da ya yi yaya yake so ta yi da ranta? to shi wai wane irin mutum ne haka da komai laifi ne a gurinshi? Turo dan bakinta tayi gaba ta kuma lumshe manyan idannuwanta da suka mata nauyi sabida gajiyar hanya da suka sha haryanxu bata samu ta warware ba Kwanciya tayi tana tuna idanun hanja da ta gani da irin jan da sukayi ko mai yake damunshi to kodai baida lafia ne a zuciyarta take kara wannan tunanin juya wa tayi irin to ita meyema ruwanta dashi har da xata tsaya tunani akan shi kara tsuke bakinta tayi ta gyara kwanciyarta da tufafinta ba tare da ta yi tunanin wani cenzawa ba, nan ta fara dan gyadi gyadi, sai dai bai yi nisa ba ta jiyo ana kwonkwasa mata kofar Da sauri ta zabura ta mike tana zarar ido cike da tunanin waye kuma? Karasawa ta yi ta bude kofar idannuwanta suka sauka a kan Sir wanda du yadda ya so dan boye yannayi na bacin ran da yake ciki ya gagara boyewa a fuskarsa hakan ya sa fuskar tasa sam ba walwala a tatare da ita Kwalin mai dauke da pizzar ya miko mata yana mai tsatsareta da ido Ita kuwa da murnarta ta ce" Wo sir ka ga irin aikin da na yi yau kuwa? Yanzun na gama fadawa Mah tana ta daria Allah allah nake mu je Niger idona idon Oga na ga irin murnar da zai yi, menene a cikin kwalin nan?" Gaba daya magangannunta na innocent girl da shirmenta ya zubawa ido kafin ya ji kamar zai yi kuka a hankali ya rabata ya shige yana tunanin ita batama san ransa a bace ba kau? Yana shiga ya zauna saman kujerar dake dakin yana kallonta ya nuna mata wajen zama Baya ta waiga ta ga su kadai ne fa, a haka yake so ta zauna da wando tikaka a gabansa? A hankali ta ce" a islamiya an hane mu kadaicewa da namijin da ba muharaminmu ba, malama Shamsiya ta ce a wannan zamanin ko muharaman namu ya kasance muna suturce jikinmu idan zamu kadaice da su komai kankantar lokaci, domin mun shigo zamani mai wuyar fasara wanda shedan yake kara samun galaba a kan bayin Allah, na saka kayan nan ne dan ba yadda zan yi, na sakankance ne dan na ga ba ni kadai bace da mata sosai, kuma na kiyaye da dukan karfina, dan Allah ka ga bani da sutura a nan ko sallah ban san da me zan yi ba, ka yi hakuri mu je dakin daya daga cikinsu sai mu tatauna" Ajiyar zuciya ce ta kwace masa ta farin ciki, wai dama akoy sauuran yan mata haka? Ba abinda yake tunani bane dai kennan ya kaita wajen HANJA, shima ba cln yake ba domin shima ya sha ratsa gonar da ba tasa ba, a cikin wa'inda ya samu mu'amala harda wace bai taba tunanin zata bude masa sket ba, aman shima yana rike dautuncinsa wa yaran da yake horawa, dan murmushi ya ji ya kwace masa da tace wai su je dakin daya, to ita bata san idan har lalatar ce a gaban dayarma sai su yi ba abinda ya sha mata kai? Lale Munnerath na dauke da tarbiyar Allah , sam bata san irin rikicewar da duniya ta yi ba, kuma yana godewa Allah, Yana gannin mutuncin yarinyar nan har yanaiwa kansa fatan wayar gari ya malaketa ta zamo uwar y'ayansa , ba dan komai ba sai dan nutsuwarta da kamun kanta, walahi a da bashi da damuwar auren wace bata watsa kanta ba ko wace ta watsa, haka kawai a shigowarta rayuwarsu ya san girmama darajarta, a shigowarta duniyarsa ya iya bambance muradinsa, da ace zai samu da sai ya fi kowa farin ciki ( Yan matanmu, zamani ya zo wajen da mazan na lalata da mu ne dan biyar bukatunsu, aman kuma idan ta kama namijin nan ya kilace walahi talahi bilahilazi idan kika ga ke abokiyar watsewarsa ya aure ki karfin rabo ne da Allah ya saka a tsakaninku,kina ji kuma kina ganni zai je ya dauko wata kamilaliyar da kika fita a komai ya aura ya kilace abinsa, a haka zaki ji ana fadin du irin jiransa da wance ta yi? Bayan ke wancen din nan ke kika gama wulakanta kanki kika bashi dan so da kauna baki san cewa shi lalatacen ya fi son kamilaliya ba? Ai ko yann iskan mazan sun fi so su kilace kamilalu, haba yar uwa dan Allah yaya kike so namijin da yana gani kike cin amanar iyayenki kina fitowa kina tarda shi kuna badalarku ya yarda cewar idan ya aure ki dan soyaya ba zaki masa haka ki tarda waninsa ba? Soyayarsa ta fi ta iyayanki ne ko ta kai ta mahalincinki? Ko bakya jin tsoron Allah ne?, Dan girman Allah mu yiwa kanmu da kyau, idan kina yi ki tuba ki kilace kanki ki kiyayi maza, namiji na iya kashe ki ya kashe dubunki ya karar da dukan alkhairinki, namiji na iya binki ya bi kawarki shi bashi da faduwa......nasiha ce garemu baki daya Allah ya shirye mu) Yana karasowa dan kusa da ita kadan ya tsaya yana kallonta a sanyaye ya ce" Muneerath, na san ba zai fara a kanki ba, aman ban san ko zai iya rike kansa a kanki ba, Munee ki sani ke diamant ce kuma burin kowani namiji, kar ki saka ni hawaye dan Allah, domin kin ga walahi ba wanda zai iya