Sashe 61
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (A SSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4 Likita ne namiji docter ne da yake ja gaban likitocin palace din, Da sauri mutun uku ke biye da shi dadauke da yan abubuwan kawo agaji na kusa kusa Sai da chef din s curit din nan ya caje su kafin su karasa wajen da Mah ke zaune rungume da Muneerath hankalinta tashe tana dan share hawaye gefe da gefen idannuwanta Dayar ce ra kama Mah dan ta taimaka mata ta dan matsa su duba Muneerath din Kwontar da ita suka yi saman kujerar suka aaunata Da sauri ya bukaci da a kawo masa oxyg ne domin ifan mutun ya suma wannan shine dama mafi sauki da ake yiwa mutun dan ya dawo da hankalinsa idan bai samu numfashi bane ake zuwa ga allurar karin ruwa wace ke dawo da mutun ana kiran da abubuwan nan R animation, idan ya ja dama ne ake kara daukaka bincike dan gannin abinda ya hannaka dawowa a hayacinka Wannan karonma basu dauki lokaci sosai ba sai gasu nan tafe da dukan abubuwan da ya bukata Mah na zaune gefen HANJA ko nace dan face da shi tana kallonsa Gaba daya a zaunen nan da yake zakin nan a jikinsa yake , kansa a saman kirjinsa, shi kuwa yana shafa bayansa ne aman kuma tsuru idannuwansa a wajen inda likitocin nan suke tsaye cikin nutsuwa sunna aikinsu, a hankali ta maida dubanta wajen likitocin ta ga irin yadda dukansu babu mai kwakwaran motsi sai da dalili du kuwa dan yana wajen ne kafin ta kara maido dubanta kansa a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana kara kureshi da duba dan burinta so take ta karanci abinda ya samu yarinyar nan dan ta kula dikim din ya tashi Irin yadda mutun ke farkawa a tsorace yawancin lokutan summa hakan ne ta faru da Muneerath wace dama a tsoracen ta summa sai kawai ta dawo a firgice bayan ta kwala ihu ta nemi rarumar wanda a tunaninta har yanzun a jikinsa take hakan ya sa da sauti likitan nan ya kama damatsunnan hannayenta cikin yaren turanci da rarashi ana taimaka masa dan kar ta cire abin numfashin da aka saka mata ya kara kusanta jikinsa da nata sosai a cikin aikinsa ba da wani abin ba yana kara dan matsar da ita kan kujerar yana fadin" Shuiiiiiiiiit, is ok, ya isa haka ba wani abin da zai kama ki, ki nutsu kar ki cire abin hancinki" A hankali ya bi hannayen likitan da cinyoyinsa dake kusa gak da gak da nata, Idannuwansa ya yi gagawar rintsewa jin irin dukan da zuciyarsa ta masa da bai san ko na wani daukar maganar bane Cire dubansa ya yi daga bangarensu ya juyo kann Mah dinsa Idannuwanssa ya lumshe a lokacin da suka yi ido hudu da Mah wace ta wara nata duban tana kallon yadda idannuwansa ke nuni da ransa a matukar bace yake A hankali ya mike tsaye daga zaunen da yake hakan ya sa Tgr ta ringa zagayarsa tana kada bindinta hankalinta kwonce domin ita kam nata bukatar a cike yake tunda gata ga uban gidanta Wajen agogo ya kai dubansa kafin ya juyo yana kallon Mah a hankali kuma ya juya ya nufi bangarensa inda Tgr ke biye da shi yana tafe a hankali kamar yadda jiya ya fita a hankali jikinsa tamkar ba lakkah ko daya Da ido ta idasa raka shi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta koma kusa da Muneerath sosai tana kallonta ta rike hannunta tana shafa gashin kanta a hankali ta ce" Ki yi hakuri yar albarkana, ki daina zaburar nan" Muneerath ta lumshe idannuwanta tana kallon Mah kasa kasa muryarta ta ce" Mah?, Zaki ne ya biyo ni" Mah ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Ba fa zai cije ki ba, kin ga ai Hanja na nan ba zai bari ya cije ki ba" Sai a lokacin nan hoton wanda ta rukunkume ya shigo idannuwanta, cike da takaicin kanta ta jimke hannun Mah ta rintse idannuwanta da karfi hankalinta tashe tana jin haushin kanta Zuwa lokacin ne wayarta ta dauki tsuwa, Mah ce ta mike ta dauko mata ita cen yashe domin likitocin sun tafi, tana jujuya wayar tana kallon yadda ta ratatake da kyar ta iya daga mata ta saka mata ita a handsfr ta miko mata kafin ta kuma zama a hankali ta dagota tana mata apkin sannu ita kuma sai kara langwabewa take tamkar zata fasa kuka bayan ba abinda take ji a yanzun, da gaske ne a dan rikice take ta ji tsoro dazun sosai aman yanzu da ta ga Mah a kusa da ita sai take jinta cikin nutsuwa dan haka kawai take ji babu abinda zai kuma tabata a gaban Mah ciki harda danta, langwabewar nan kuwa da take gani ta yi kamar da wasa dan bata da lafia ne ake tatarotan nan to ai kuwa Mah ta shiga uku domin ita dai zata yi ta kwonci ne tana zuba iya shege, aman gabanan kafarta kafar Mah dan ta kula dan Nan na Mah bashi da lafia, sam ita ko wa zai ce mata yana da lafia ba zata yarda ba, yaya mutun mai hankali zai yarda ya ringa wasa da ransa? Haba dai walahi ita dai da ranta da hankalinta ba zata yi kawance da zaki ba! A hankali ta amsa muryarta a sanyaye Daga dayan bangaren aka shaida mata cewar tana da tashi karfe biyu na dare Da sauri Mah ta amshi wayar ta datse tana fadin" Ba zaki tafi ba yau kam, ke da baki da lafia?" Wani irin mikewa Muneerath ta yi tana kallon Mah ta dan girgiza kanta a hankali ta ce" Haba mahna, wollah nu kalau nake kin ga? Kalau nake Mah, zan iya barama na je na dan rintsa kadan kafin karfe goma dan Allah mahna ki tasheni wollah dan suma ne mu a garinmu da za'a maka dukan mutuwa kuma a sakaka aiki ka yin kuwa bale suma a kwonce cikin nutsuwa ? Wama ya san ko Niger zamu sauka na ga Oga? Mah plz ga wayata dan rike min bari na je na huta" Da gudu ta yi wajen accenceur, Mah ta rakata da kallo baki bude Dan murmushi ta samu kanta da saki tana girgiza kai da mamakin kokarin Muneerath din, sai ta ajiye haka a matsayin yarinta ne , dan yarinya ce ya sa da ace wata baba ce ta suma yanzu ai ba inda zata iya zuwa, kai bama zata iya aikata komai ba sai dai a ringa mata sannu Mikewa ta yi a hankali ta kurawa hanyar da zai sadata da bangaren yaronta So take ta san me ya faru? Yaya aka yi Muneerath ta suma a kan kujerar da yake zaune? Me ya kawota inda yake zaune? Ba dan komai take son sani ba sai dan tabatar da tsaro a tsakanin yan matan nata da yaron nata, sam bata zarginsa da komai suma haka, aman zata kasance mai taka tsantsan a tsakaninsu dan gudun tasiri irin na shedan ya yi karfi a tsakaninsu Komawa ta yi wajen accenceur da yar karamar wayarta da kuma ta Muneerath a dayan hannunta ta dana ta yi kiran matar dake kula da Camerar gidan Cikin nutsuwa ta shaida mata tana son vidion da ya wakana nan da awa biyu, sannan ta nemi da a kawo sabon phone ....... ........wannan kennan........... Ruwa ke zuba a jikinsa, idannuwansa a bude suke ruwan na ratsa masa idannuwan aman baya rintsewa kuma baya kiftawa har sai ya dauki dan lokaci kafin ya kifta din A hankali ya karadaga hannunsa dan so yake kwata kwata ya daina yi masa dan barin da yake masa Gannin ya daina kwata kwata ya jimke hannun nasa ya sada kansa yana hararan jikinsa cike da jin haushin wannan rashin kunyar, mema aka yi da har zai nuna kansa? Gannin zai bata lokaci sosai gashi zasu yi tafiar kwana biyu cif ya saka shi daura alwallah ya fice a bayin Sallah ya fara gabatarwa ta la'asar a dakinsa domin lokaci ya shige bai yi ba kafin yake karasawa wajen kayansa da yar wayarsa a hannunsa ya rubuta message ya tura a VIP na matan da yake dauka ya tura Tsai ya yi da ifannuwansa yana tuna magangannunta A hankali ya lumshe idannuwansa yana jin kansa ya fara daukan zafi........"BAKA JIN KUNYAR MAHALINCINKA? KA YI AURE, KA YI AURE" maganar da mah taje yawaita fada masa "IDA AKA CE DA KAI MEYE HUJARKA ME ZAKA GABATAR? RASHIN MUHALIN AJIYEWA NE, RASHIN KUDIN SADAKI NE? KO RASHIN LOKACIN BATA NE? KA JI TSORON ALLAH KA YI AURE"............ Idonsa rintse ya daki madubin jikin wrdrb din da karfin da ya saka madubin zubowa gaba dayansa kasa Bai kula da hannunsa ba ya dauki wayar a takaice ya rubuta sako kamar haka "A BARI!" Ya tura kafin ya juya a hankali ya nufi wajen bed dinsa Kwata kwatama sai ya fasa tafiar ya nemi wajen kwonciya inda tgr ta haye saman itama tana gyarawa ta kwonta kusa da kafafuwansa ya yi adu'a ya fara neman barci karfi da yaji cike dajin haushin abinda shi kansa bai san dalili ba..........ya fi ajiye hakan a gurbin rainin da wannan yar african ta masa, ta rasa wajen hawa sai jikinsa ? Ta rasa wa zara ringa cirewa kai sai shi? Lalema! Dukan abinda ya dace a yi an yi sun kama hanya tafia ta cikin dare ce wace bata da nisa sosai domin duka duka awa hudu ce ta sauke su a kasar da zasu je Wannan karronma dakunnansu suka shige suke hutar da gajiyarsu , sun samu isashen barci domin a garin ne zasu yi kwana har biyu kafin su juya dan akiy jirgin da zai duba wanda ya kakare a cikin garin ya ki tashi yana kampanin gyaransa , kasancewar jirgi ne da kampaninsu ya kera sai aka nemi da ya zo ya ga meye matsalar idan ba sai an kai jirgin Ingila ba sai kawai a fadi matsalar a kawo kayan gyaransa, idan kuwa sai an kai shi dole a ga ta wace hanya ya dace a kai shin Shi dinma wani barcin ya nema dan zuciyarsa a cinkushe take duda ya samu sun