← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 114

Sashe 82

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 5 Ta ce" Me yasa kike son saka wasa a dukan lamarinki?, Me sarkin garin ingila yake nufi da maganar cewa ke din SARAKUWARSA ce? Meye fasarar karamawa da muka samu irin wannan?, Abinda muka malaka a yanzu ni kaina da sanadiyarki na malaka ko sir da ya yi shekaru a matsayin ma'aikaci baba mai horar da hostess bai malakesu ba duka hakan a kan wani dalili?, Da aka yi maki accct na kasar ingila da takarda ta shaidar da aka baki damar zama na dindindin a kasar ingila wada kike iya shiga ba tare da visa ba kai tsaye ki shiga wajen da ya maki ki kama gidan da ya maki da dukan isa irin ta haifafen kasar me suke nufi? Meye fasarar fadan da kuke yi ke da Princ HANJA?, Me yake hasala shi a kan maganar da ta shafe ki?, Me yasa a ranar nan ya yi maki tambayar me wani namiji ya fada maki , ke kuma kika dubi tsabar idannuwansa kika bashi amsa kai tsaye ba tare da kin ji dar din abinda ka iya zuwa ya zo?, Shin inai maki kallon marar wayo kina mani na shahsasha ne?, Soyaya kuke da magajin kujerar garin ingila ko me?" A firgice Muneerath ta ce" Dan Allah sasauta da magangannun nan naki Saudat kina neman tarwatsa min kwakwaluwa, me hakan yake Nufi ? Me magangannunki suke nufi dan girman Allah?, Wacece ni? Me ya hada ni da irin wannan kokowar? Koda na kasance mai aiwatar da lamurana kai sake na san wajen wasana, kin ga tunda Allah ya hadani da shi na fahimci ya tsane ni, Saudat mutumen nan da ba dan mamansa na gefe ba da ya karya ni, kina gani fa ba laifin tsaye ba na zaune zai kama hararata, ki duba ki ga sau biyu ina suma a saboda shegen Zakinsa, Saudat ke fa shaida ce dan tsabagen tsana na ce Freind zai zo wajena ya ce ba zai zo ba dan yana gidansu ko?, Kuma sau uku yana zo min dan Mah ta ce idan ya kara ne zan samu ciki na ki ya karan fa, aman dan Allah me hakan yake nufi ke da kanki kin san koda Pah ya fadi haka ya fada ne dan ya kular da shi, baki ga haka yake tsokalarsa ya yi ta cika yana batsewa ba?" Dafe kai Saudat ta yi cike da tunanin ta inda zata fara kafin ta dago kanta ta ce" Da farko kar ki kuma budar bakinki a gaban kowa ki ce wai namiji ya zo maki, kin kuwa san menene ma'anar an zo maki?, Ciki baya samuwa sai idan mace da namiji sun kwonta sun yi hvng sex , idan na ce maki sex ina nufin sun samu moment a tsakaninsu da basu da shamakin komai babu wani hijabi da ya tarewa daya gannin tsiraicin daya, zasu raya sunna ce mai tsafta da tsayawa a rai, zasu zama abu daya ne , zai kasance sun samu nutsuwa da junnansu ne ta yadda a duniyarsu babu wani abu kuma da ya rage da zai zamo boyaye ko bako a garesu, na biyu ki fito min a mutun ki min maganar tsakaninki da SIR HANJA, na uku daga nan gidanku na nufa domin nawa iyayen sun yi tafia paris dan visite na rashin lafiyar mahaifina, kafin su dawo ba zan je gidanmu daga ni sai mai aiki ba , ba kuma zan kama h tel ba" Muneerath ta dafe gaban goshinta itama cike da rikicin magangannun kawar tata, ita har ga Allah abin daria nema yake bata, kuma dukan abubuwan da ta zayana ta yi masu waje ne ta ajiye su a irin tsabagen kula irin ta Familly din Su Pah Gaba daya sai ta mata shiru ta tada motar, kai itafa abinda ya fi damunta shine tunanin yadda za'a yi Ta samu waje a gidan Oga ba tare da an kai ruwa rana ba Cike da shagalta da kallon garin haihuwarta, wajen da ya tara iyayenta kakaninta, danginta take tuki har ta dauko duguwar hanyar da zata sadata da kofar gidansu Abubuwan da suka cenza a garin basu da yawa sosai, sai gine gine da ta ringa ganni sai gyaran hanyar da aka yi wanda idan za'a hada da kasar da ta fito ne babu mahadi, sai dai abinda yake tsaye a kasan zuciyarta irin farin cikin dake daskare a zuciyarta ya wuce tunanin bawa A hankali ta yi kwana ta samu ta dakata dan nesa kadan da gidansu tana karra wara dubanta a kan wanda idannuwanta ke ganni A hankali kafafuwanta suka dan fara yi mata rawa rawa, zuciyarta ta shiga dokawa da dukan karfi, zufa da tsoron da Saudat bata taba ganni ba a tatare da Muneerath ya bayana a tare da ita Tabas da take ce mata idan tana so ta ga rauninta ta bari idan tana kusa da ahalinta A hankali ta ce" Muneerath ? " Muneerath ta juyo da sauri tana kallonta ta kasa amsata A hankali ta ce" Ina ne gidan? Kin ja kin tsaya jikinki na rawa kin kafe wancen mutumen da kallo?" Muneerath ta hadiyi yawu a hankali tana karra jimke hannunta dake saman cinyarta a sanyaye ta ce" Oga ne cem tsaye, wannan tsayuwar da Oga ya yi idan aka tabo shi ne, ni kuma bana so na fado daidai ran oga a bace, kin ga tsayuwar cen da ya yi ko dansa ya taba shi zai ga ikon Allah, ga kuma gidan namu a bude ham ban san me yake faruwa ba" Da mamaki da kuma tausayi ta karra kallon gidan da Muneerath ta fito, a kasan zuciyarta ta ayanna 'Lalle babu mai daukaka bawa sai Allah' Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" To ki tada motar mu karasa mana" Ido ta zarro ta ce" Wa ni?, Na je gaban oga da motar nan a haka mu yi kaka da shi?, Kin ga mu juya kawai mu koma karma idannuwansa su juwo kaina a haka idan ya bar kofar gidan sai mu dawo" " KUT Walahi baki isa ba!" Saudat ta ce , da sauri ta kama marfin mota ta bale ta fita kai tsaye ta durfafi wajen da Oga ke tsaye zuwa lokacin ya ga tsayuwar motar duda bai kure su da ido ba aman haka kawai ya ji zuciyarsa na yawan son ya kalli motar Da sauri Muneerath ta fito tama zarro ido ta ce" Kan balaki, Saudat ki fa bar balaki ya yi barci , karfa ki yi garaje fa" Wani marfin langa da aka jefo daga anyar kofar ya saka Saudat ja da mugun sauri tana kallon wajen da kuma hayaniyar dake fitowa sama sama Kafin ta idasa fahimtar komai wani uban dutse ya biyo baya ya sauka a kusa da kafarta harma ya shafi yar karamar yatsarta Da sauri Muneerath ta ja hannunta gefe ta nemi nausuwa cikin gidan ranta bace, sai dai kafin take idasa saka kafarta aka yi baya da ita Wani wawan mari dayar ta kifawa daya, da gudu suka karra kurmiyar junna sunna dukkan junna da kokowa Oga dake tsaye dadage yake dan gannin wai da gaske abinda idannuwansa ke gane masa ne? Gannin ta shige cikin al'umar gidansa ya saka shi nufar Saudat da ta yi mutuwar tsaye tana kallon ikon Allah Da sauri Saudat ta rufe fuskarta dan tsoro ne ya shigeta kar a je Oga ya wanka mata mari Oga ya kare mata kallo ya ce" Ke dillah bude idannuwanki ki fada min wannan yar wacece?, Kamar kamar y'ar oga sai dai abin mamakin kalar fatar wannan ba ta africa bace sam sam" A hankali ta bude idannuwanta tana kallonsa da tsoro, ta kuma hangi Muneerath ta hakikance a cikin yan uwanta ba mai ba yar uwarta hakuri domin a fadan harda kanwarta ana ta dakuwa A dan tsorace ta ce" Eh Muneerath ce" Sai da ya kwalalo ido kafin da sauri ya nufe su Da wani yannayi irin na yan daba ya ringa eartarsu da daidaya yana kifa masu mari yana maida su gefe da gefe kafin a haukace ya ce" Zaku nutsu ko sai na kira police ya kwashe min ku baki daya na huta da jaraba?!" Du wajen ne ya dauki shiru sunna kallonsa koea na huci tamkar kububuwa A dake ya ce" Yar oga? " Muneerath dake tsate rike da kanwarta gaba daya sun kara tara mata gajiya sai da gabanta ya fadi da sauri ta kale shi kafin a raunane ta amsa still tana kallonsa Du da mamaki suka juyo suma sunna kallon nata lokaci daya ana kare mata kallo tun daga kasa har sama Daya daga cikin matansa ne ta saki buda tana rike dan karamin hancinta ta ce" Lale bariki ta yi rana, wai dama wannan Muneerath ce? Tabdijan iskanci ga mai daure maka gindi a gidan Oga!" Muneerath ta budi bakinta zata yi magana idannuwanta suka sauka a kan fuskar mahaifiyarta Shigar maman nata ta so ta bada mata ko wacece, sai dai irin yannayin da ta tsareta da duba ya sakata karra kallonta da kyau Oga ya yi juyi ya kuma juyowa cike da mamaki ya ce" Wai yar oga da gaske dama a ingilar kike? Muhamadu rasululahi salalahu alaihi wa salam na shiga uku, wai yanzun ke din nan Hostess ce? Walahi ni du a tunanina kin hadu da wani dan iskan ya gama hore maki kunne irin na yar uwarki, Yar oga yanzun daga ina kike? Na shiga uku dama na san zuciyar nan taki tawa kika gado idan nace sai na yi sai fa na yi, gatanan Babarki da na ganta na nace sai ita na kuwa bi ta inda na bi itama ta haukace sai ni aka aura mata ni iyayenta suka yi fushin zuciya da ita suka salama min na rungumo abina gatanan wai yanzun ta saku ta daina sona aman saboda ke take zaune ta ga ta inda zaki dawo yau gaki Allah ya dawo min da ke shikenan sai ta daina fushin ta fuskanceni mu fuskanci junna" Da rashin fahimta take kallonsa tana son karrin bayani, sai dai bai bata wannan damar ba ya shiga kora yaren cikin gida Ruuuuuuuuuu da su da
Chapter 82 · 0% Book details