← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 114

Sashe 54

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
3
Muneerath ta ce" Mah kin ga daga Allah ba wani ni ban ce ya taban hannu ba, daga maida masa wayarsa da ya ara min na yi kiranki shine ina mika masa na ga ya taban hannu kuma ina gannima na warce hannuna...."
Da sauri iman ta matso ta ce" Wayarsa ya ara maki?"
Muneerath ta dan kaleta sakalau gannin yau ta mata magana da kanta ta kebe baki ta ce" to da da wata waya kike so na kiri Mah ni da na bar wayar a daki?"
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana gyada kai cike da mamaki Muneerath ta dora da fadin" tun a nan na shiga tunanin kin ce min idan na ga ko hannuna za'a taba na kiya dan ta haka suke fin karfin mutun har ya samu ciki sai na shiga tunani, kuma sai na y
anzun da ya min walahi daga shi babu wani taba min hannun kuma"
Mah kawai kallonta take , daga bisani ta ce" Muneerath, je ki ci abinci kin ji, ga imanma yanxun take ce min yinwa take ji ku tafi ku ci abinci"
Iman ce ta girgiza kanta da sauri ta juya ta shige accenseur tana fadin" Aa na koshi" ta dana hankalinta tashe cike da rudani, tabas fada ta ga sunna yi, aman darajar yarinyar nan da suka dauko a wannan garin har ya kai ya yi fada da ita? Aman a kan me ya ara mata wayarsa? Ya salam, ya salam................................
Muneerath kuwa kai ta kada abinta itama ta nufi kicin domin so take ta je a mata wainar kai yauma ta gwada soyawa da kanta ko za'a dace
Mah a hankali ta idasa shiga da salama a bakinta
Wajen da yake zaune ya rike kansa da hannunsa ta nufa watau saman wani kujera kamar na lybi din nan masu laushin gaske
Zama ta yi ta tsura mada ido a sanyaye ta kuma furta" Asalamu alaika "
A Hankali ya dago jajayen idannuwansa a saman lebensa ya furta" Amen wa alaiki sakam "
Mah ta mika hannunta wajen dafe kumatunsa da ya yi muryarta a nutse ta ce" Me yake damunka? Me ya hadasa maka tagumi? "
Hanja ya cire dubansa a kanta na dan lokaci kafin ya juyo a sanyaye ya ce" Mah, me yasa ina kiran waya bakya dagawa hakama Pah ?"
Ajiyar zuciya ta sauke tana dan hade fuskarta ta ce" Dan na fara jin haushin amsa maganarka komai kankantarta "
Ido ya tsura mata a kasan zuciyarsa kuwa mamakinta ke son kashe shi, lale ya yarda cewa Mah haihuwarsa ne kawai bata yi ba aman irin yadda take karantar dukan motsinsa sai abin ya ringa bashi mamaki.....wani lamarin sai uwa
A hankali ya sauko ya dora kansa saman cinyarta muryarsa a sanyaye ya ce" Inafa neman auren, ko dazun sai da na so kallon wata a Hawai....to kawai sai na ga tana ta kalona ......sai na ji haushin hakan wai me yasa da sun ganni suke fara son nuna min sunna so na? Waye ni? Me na fi wani? Ni ina so na ga wace ban dameta ba, ina so na ga wace zata wahalar da ni ba kawai dan kina mai zaman jira ba daga kin ganni ki nunan so, Mah sam ban yarda cewa ni din take so ba sai na ga akoy dai abinda take so...... Dan Allah kar ki yi fushi da ni, rabona da mace tun da zamu yi tafiar nan sai yau"
A hankali Mah ke shafa gashin kansa tana jin yadda yake sauke ajiyar zuciya wai shi a nan magana ce ya yi mai tsayi
A sanyayenta ta ce" Anya kuwa za'a samu? Wace zaka nuna mata so ta nuna maka aa? Wacece zata ga yarona a tsaye a gabanta komai kyanta ta girgiza maka kai ? Anya son kana so ka yi auren nan kuwa ? "
Hannunsa ya dago ya dora saman nata da take sosa masa ya dan dago ya kali fuskarta kafin ya maida kan nasa a hankali ya ce" Ni na san akoyta Mah, akoy wace ba kuduni, kyauna, ko mulkina ke gabanta ba,,ni na san akoy tawa a kilace a wani wajen duda zuciyata na cike da zulumin wacece ita?, Abinda na sani koma wacece ita din ba zata amsani a zuwan farko ba, ba kuma zan sha wahala dan tankwasata ba fa.......no ina dai so ra nunan ban mata ba ni kuwa zan saka a dauko min ita na aureta"
Mah ta yi murmushi dan walahi irin yadda ya yi maganar sai ya bata daria domin ya wani takwakwabe fuska dan kawai ya sa ta manta fushin da take masa
A hankali ta shafa gefen fuskarsa ta ce" wace uwa ce zata so yin fushi da yaronta?, Wace uwa ce zata kulaci yaronta? Idan ha uwa takai ga yin haka tana cike da tsoro ne, shin yaushe zaka daina? Bana so ka dauka cewar ai kai naka zunubin karami ne, a zunubi babu karami bale idan mutun na yinsa kai tsaye, kai musulmi ne, zina ta haramta a gareka Khalb"
Hannun nata ya rike a hankali ya lumshe idannuwansa ya ce" Mah?, Zan daina ina ji a jikina zan daina"
Mah ta ce" ka ce min ka daina, ka yi min alkawarin ka daina"
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce" Zan je nemo maki sarakuwar ki, zan kawo maki ita ki rungumeta......zan aurota ......zan samo wace zata zauna da ni, zafa iya rayuwa da ni....Mah bani da ra'ayin mace sama da daya shi yasa wani sa'in sai na shiga tunanin ko sakawa nake a kawo min yan barikin na zaba?, Ni kam a halin tunani nake"
Kanta ta girgiza a hankali ta ce" Idanma yar barikin ka aura da niyar cetota daga aikata aikin nan....ceto ne, aman ka sani zan fi farin cikin ka samawa y'ayanka uwa ta gari"
Murmushi ya yi a hankali ya kara dora kansa saman cinyar Mah din a kasan zuciyarsa kuwa yana aiyana' tarbiyar uwa a yanzu ta fi ta ringa nunawa yaro soyaya, ba ruwanta da inda zai shiga su waye abokanansa , idan kana son gane ita ta haifa a taba shi yanzu zata fito a shiga dibar albarka da ita, Mah a tunaninki akoy iyaye irinki kuwa ?, ni ko na yi aure zan ringa zuba mata ne tana haifowa ina tarbiyantar da kayana ko na kawo maki da an haifa ki bashi tarbiya dan ni ba zan ba mace ta lalata min yaro ba!'
A batane kuwa sai ya ce" i miss u"
Mah ta yi murmushi a hankali ta ce" Gashi yake fitowa a kansa, gashin kuma mai duhu......kuma, kuma...." Sai wata irin kunya ta hanata karasawa , saima ta rasa ta yaya zata fada masa kuma din
Idannuwansa ya rintse yana jin yadda bugun zuciyarta ke cenzawa irin abin na taba mata zuciya a hankali ya ce" Kina so ya warke ko?"
Mah ta gyada kai da sauri tana kallonsa
Murmushi ya yi mata ya tashi ya zauna a kusa da ita yana rike da hannunta a hankali ya ce" Yanzun zamu je mu kaishi wajen likita, kuma sai ya je"
Yar daria ta yi tana kallon yadda yake harhade girar gishinsa irin zasu raba hali kennan
Mikewa ya yi yana fadin" mu tafi"
Ai kam Mah mikewa ta yi ita dinma cike da farin ciki domin dama ta fi son su je din dan a cen akoy kayan aiki komai da komai idan kuwa zuwa ne zai yi daga shi sai yan kayan aune aunensa
Da sauri ta nufi wajen nikaf dinta ta dauko ta cire mayafin dake kanta ta daura sanann ta kara yafa mayafin sosai a jikinta
Shigar nata ya kurawa ido, kulun Mah cikin shigar abaya take koda kalar ba baka bace aman abaya ce kuma kowace kala zata saka da nikaf dinta,
Haka kawai a ransa yake jin sha'awar irin shigar nan nata, ji yake idan aka ce yau zata fita ba shigar nan ba zai yarda ba, yana wani irin jin shigar a ransa
Murmushi ya mata ya juya ya nufi waje
Ita kuwa ta bi ta dayar hanyar dan fitar da Pah cikin dabara
Tunda ya nufo falon yake jin dariyarta
Haka kawai ya samu kafafuwansa da rage saurin da yake dan gannin ita kuwa mahaukaciyar yar nan da wa take daria? .....ntd Hanja din da ba abinda ya shafe shi da abinda wani yake yi?
Yan mata biyu ne suma a tsaitsaye da plat plat a hannayensu masu aikin gidan ne sunna sanye da dogayen sket da rigar kicin kawunnansu da hulunna itin na chef, itama ta daura hular ta chef a kanta ta cire dan kwalin hakan ya sa gashin kanta bayana har gadon bayanta sannan ta daura abin daurawar nan da ake daurawa idan za'a yi girki
Muneerath ta ce" ku tsaya ku tsaya ku tsaya na irga uku sai a taba a tare, kun ga du wace ta ce wainar kwon nan bata yi ba dadi na san dan kawai mu yi fada ne, kun ga dan ta yi duhu ai ba matsala bane magi ne ya isheta sosai"
Wata dariar ta kusanta ta saka ta ce" Madame, wannan kwon konewa ne fa ya yi"
Muneerath ta ce" lalala, tabas baki san shi kwai sai an masa haka vitamine dinsa ke fitowa ba?, Ai idan dai kwai ne ya soyu da kyau shine darajarsa yanzun dai ku tsaya wollah ku ce ya yi dadi dan in fadawa Mah ta yi murna kun ji?"
Dayar zata yi magana idannuwanta suka sauka a kan Hanja, da sauri ta ajiye plat din dake hannunta jikinta ya dauki rawa , likaci daya ta tabo yar uwarta itama ta ajiye din suka duka kasa kawunnansu a kasa dan sam basu san cewa yana gidan ba da basuma shigo a warhaka din nan falon kasan ba, ba wai dan basa shiga ba domin su suke jera abincin sai dai daga wanann basa rabarbajewa har haka, yanzu haka sai da suka kiya ta tirsasa su kan a nan zasu taba konaniyar wainar kwonta
Da mamaki take kallonsu jin gaisuwar da suke fada ta juya da sauri dan gannin ko waye
Ido hudu suka yi da shi ya ja ya tsata yanzunma rigar dai ce singileti fara a jikinsa bai dora Wata ba ya rufe hannayen nan nasa, a kasan zuciyarta ta shiga fadin' Kai ban taba gannin sarkacecen kato marar kunyar nuna suturarsa irin kyankyasar injin nan, yana yawo tsirara salon a yi daria ya shake mutun kai dai ka shiga uku ba komai a ranka alamu sai iskanci ni kam ai na fada ba ni ba kai mafadacin banza mafadacin wofi, sarautar takuma da ba rawani ake maka ba fuska a bude kowani banza yana kalkonka in zaka fita....' daidai accenseur din yabude su Mah suka fito Mah na fadin cewa a rufe hanyar kasa zasu fita da PAH
Idannuwansune suka sauka a kan Hanja da ya zubawa Muneerath ido yana jira itama ta kwashi rawar jikin ta sada kanta kamar yadda Iman ke yi, sauran ke yi, ga kuma Muneerath vry cute.....so muah yarinyar ta keru rigar kuma ta karbeta, da sauri Mah ta riko hannun mijinta da ido ta nuna masa sannan ta masa alamun ya yi shiru
bata kula da su ba ita domin ya kare su da wannan kirjin nasa ya wani tsaya yana hararar mata kawaye, idan takamarsa gidansu ne ai mamansa ta kawota bale ya koreta kau? Dama irin wadinnan sai girman ba wayau
Dan bakinta ta murguda ta juyo da dan fada fada ta ce" Kai dillah ku tashi mu yi wasanmu ku kuma"
Wayo yaya zan yi da muni ni kwate
11/14/21, 12:51 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 54 · 0% Book details