Sashe 72
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4 "s ok" kawai ya fada ya ajiye wayar yana mai tsatsare Hanja da kallo Shi da kansa yanzun kuma sai tausayi da kaunar yaron nasa ke neman hanna masa kwashewa da daria, Mah har ta fara sharar hawaye dan yannayin nasa baya mata dadi gata dama mai kuka a kusa A hankali Pah ya ce" Me zaka yi?" Hanja da ya cije lebensa yana kallin Pah a kan me yasa ya kashe masa kira ya buda bakinsa da kyar ya ce" Korarsa zan yi!" Pah ya mika hannunsa a hankali ya kami na hanja ya nufi wajen kujera da shi bayan ya yi alamu kan a basu waje hakan ya sa kowa ya yi gagawar kama gabansa Zama ya yi yana kallonsa a hankali ya ce" Cire rigar" Hanja ya Kali rigar jikinsa ya ga har zufa ce ta wanke masa rigar fa, a hankali ya cireta yana jin kansa na sara masa ya lumshe idannuwansa a hankali ya kuma sada kansa Pah ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" Ba'a yi masu garaje su, baban damuwar idan suka yi niyar rike wuyan mutun komai tsufansa, kudinsa, mulkinsa, takamarsa, gatansa sai ka ga ya dawo yana walagigi kamar mai shan giya bayan shi din ba dan maye bane, dayar matsalar kuma itace ba kowace mace ihu ke tafia da itaba, ba kowace kyau, kudinka, ko isarka zai sa ta yi flln a soyayarka ba, Watan kamar da wasa sai ka ga kaine sarkin an kuma sai ka mata fadanci, watan ta fi lu'u lu'u daraja , irinsu ne idan ka kilace su ka gama samun nutsuwar duniya ka mutu kuma ka tarda alkhairi domin sune masu kaika ga aikata alkairin da zaka shiga aljana gibe kiyama, matar kwarai itace abar alfahari ga namijin kwarai" Hanja kallon Pah yake, gaba daya zai iya cewa a baibai yake daukan maganarsa baima gane ina ta dosa ba dan haka yake dan murza hannunsa so yake a gama masa nasihar ya tashi shidu gani yake idan ba balbalin balaki suka yi da yarinyar cen da wancen ciki caka din ba ba wani sauki da zai samu na rainin wayon da take masa Pah ya ce" da yawa na rasa abinda suke so dan sun kasa gane meye suke ciki da zuciyarsu, da yawa na afkawa da fada da kokawa har su bata rawarsu da tsale, Hanja shin ka kuwa ga abinda kake zama a gabanta? Famanka ka kai mata duka bayan idan ta jigata kaine zaka fara hakacewa, so kake ka mata ihu maganarka ta girmami tata karfi da yaji bayan a ruwan sanyi take soyeka tsaf a tanda, kali fa yarinyar nan jikinta ne ya debeta domin ko kiriniyar masu shekarunta bata da ita dan a milieu din da ta mike bata san haka ba, me yasa kake neman nesa bayan ga amsa a kusa da kai?, Sai an maka ruftawar da kudinka ko mulkinka ba zai hanna ka kwonta a gadon asibiti jinya ba sannan zaka ankara ka farka ka farga?" Hanja ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana kallon hannayensa , sannu sannu ya shiga tariyo abubuwan da yake yi a gaban Muneerath, walahi sai wata kunya ta nemi hanna masa hada ido da pah, sai dai ba zai yi haka ba zai hada ido da shi ko dan ya nuna masa cewar bafa abinda yake tunani bane ba fa, haba meye yake damunsa haka ne? Dole ne iyayensa su yi tuninin da ba shi ba a kansa, yanzun tsakani da Allah meye hadinsa da yar nan da har zasu ringa yi masa irin tunanin nan? , A nutse bayan ya mayar da bacin ransa a lokacin da ya gama gannin a kan mema zai wani damu wai? Ya ce da pah yana kokarin mikewa ya dan dafe gefen cikinsa rike da rigarsa ya ce" Na rasa macen so sai wannan? Ban taba yin facing din fitsarariya irinta shi yasa nake samun kaina a irin wannan yannayin, aman gabanan zai kasance tsakanina da ita relation ce ta yaya da kanwa a cikin gidan nan kamar yadda tsakanina da Iman yake, idan mun fita wajen aiki kuwa zan kasance uban gidanta a abinda ya shafi aikinmu ,ba sai na kawo maku karar ku mata maganar bane har zaku yi wani tunanin a kaina ba? " Pah ya rakashi da kallo kafin ya yi murmushi a ransa yana ayana 'Allah ya takaita maka wahala a game da makauniyar soyaya, ban san ko zan ga karshen wasanka kai da Muneerath ba? Ko sai dai na gani a gobe kiyama?'............tunanin mutuwa bai taba barin tunaninsa ba koda kuwa likita ya fada masa da sauki jikinsa da waye waye, ahi ya tabata saukin a wajen Allah yake, kuma idan mutuwar cema saukin *Alhamdulilah* . Kamar da awa daya tsakani sunna hade a falon Mah gaba daya yan matan inda a zaman hirar ta Muneerath ce kawai sai saudat da bata gama sakin jikinta ba da take yar dariya, sai Iman dake kwonce tace kanta ke ciwo bayan ta gama shan maganin da ba ciwon kan bane sai cinkushewar tunani, sai Mah dake biye da hirar tasu, kira ya shigo t phone din a nan ne ake shaidama Mah likita ce ta zo wai an ce ta zo ta duba jikin Muneerath dake da zafi Da dan Mamaki Mah ta tambayi bata da lafia ne? Wa ya ce? Amsar da aka bata ne wani tausayin yaron nata ya karra tsarga mata, shin yaya zata yi da gardamamen yaronta da Halayan Muneerath mai wuyar fasara da abansa da ya nuna ba zai takura yaran ba? Yaya zata yi ta taimaki y'ayan nata?......................bata san yaya suka kare da Pah ba hakan ya sa ta mike dan nufar bangaren Pah domin ta san yanzun ya koma dan ya huta kafin yama su hadu su yi yar kwrya kwryar birthday din yaron nasu wanda du yadda zasu kai da kin son gayatar mutane sai manyan kusoshin kasar sun halarta.....( Biki na manya kennan A wannan rana sai hakura familly din masarautar suka yi da son yi masa dan clbrt din zagayowar ranar haihuwarsa domin a lokacin da suka kuma waiwayarsa dan yin hajan gaba daya baya gidan ....................................... Bangaren Hanja kuwa yana gama abubuwan da zai yi a gidansu ya zauna da computersa a gabansa ya gama latse latsensa duda gaba daya yana yi ne kawai irin basarwar nan dan kar ka afka cikin tunani har kira daga wajen likitan da ya turawa mesage dan irin yadda jikin yarinyar nan koda yaushe da dumi ya same shi cewar lafiyarta kalau haka yannayin jikinta yake sako daga Mah dinsa sai kawai ya kure waje daya da kallo Cike da takaicin kansa da gannin kamar mema ya kaishi aikata hakan ya saka shi dafe gaban goshinsa yana mai tunanin shin me yake damun tunaninsa ne? A hankali ya girgiza kai shi kadai yake ba kansa amsar shin so yake Pah da ya gama dora masa abinda ba haka ba ya yarda da hakan harma ya yi convncng din Mah a kan tatsuniyarsu? Yanzu fisabililahi yau yake yin yan mata su yi soyaya? Ana so ace du soyayar da ya yi bai yi ta cikin zuciya ba irin bai yi soyaya ba shirme yake yi sai yanzu ya hadu da abin sonsa tamkar shirin film?, Idan ya kula iyayensa sun hau kan maganar da suka gama yankewa cewar shi Hanja wai yana son yarinyar nan? Dan murmushi ya yi yana Girgiza kansa cike da takaicin kansa da kansa, shin sun manta waye shi?, Ya rasa ina zai harbi sai afrika kasar Niger?, Ya rasa wace zai kyalo sai Hostess masu rabon abinci da murmushi wa ppsnger?, Ya rasa wa zai so sai wannan mai rainin wayon?, Shin sun manta a irin kasar da suka daukota su da kansu burinsu su mayar da ita lafia?, Dan kyaci ya yi yana murza hannayensa tare da kuma girgiza kansa, sai ya ba kansa amsa cewar ai koma me za'a yi tunani da kai Hanja kai ka janyowa kanka, duba ka ga yadda kake daga murya da kwonji kana zakalkalewa a kan maganar yarinyar? Yana cire dogon wandonsa na pilot yana jin yadda ya ba kansa amsa ya girgiza kai tare da hade rai sosai yana mai ayana' tabas laifina ne, dole a min gurguwar fasara, basu san cewar aiki da jirgi bai haukatani ba, ina haka ne dan na kareta daga irin namu mazajen masu dukan du macen da ta wangale kafa su tsalake su manta da ita tamkar sun shiga injin sauke nauyinsu sun sauke sun biya an wuce wajen ne, yana gudun kar a bata tsoron da idan ta yi wata sumar ba zata farfado ba, aman ya yi haka daga yau ba zai taba daga dan yatsansa dan yin wanni abin a kan hakan ba, zai karyata tunanin dukan wani mai tunanin wai wai shi Hanja ........' sai kuma ya danne lebensa na kasa yana girgiza kai da dan alamun abin shi yanzu nema ma yake ya bashi dariya Sai kawai ya yi wankansa ya saka sasaukan kayansa ya amsa a gagarumar shirin birthday dinsa da yarinyar yar gidan ministern kasar kuma dan kasuwa ta shirya masa duka a kan idasa nufinta na ta ganar da shi cewa baban goro sai magogin karfe, du wata mai rawar kan son ta nuna kanta a lamarinsa takan motsa dan yatsarta ne ta bata shawarar kaucewa ko ta kawar da ita ta kowace hanya domin ita a ganninta ita ta fi cencenta amsa kiran sunnan matar sarkin garinsu duba da cewar idan kyan ne ta samu, nasaba tana da kyakyawa, dukiyar ta wanke kafa a ciki ta yi asuwaki da kafar kaza, iyayenta sun bata goyon baya to fa bata tunanin akoy wai shamaki da ya dara nasa wanda a kadan a yanzu ta kusa shekara tana kara yada masa manufarta aman cikin ikon Allah tamkar kurma kuma bebe a yarenta, dan ko hannunsa ta rike sai ya bata umarnin saki bayan ta san cewa a yana musulminma su musulman da basa harkar mara shi yana taba abinsa, domin tsaf ta san waye shi kafin ta ji cewar du duniya babu namijin da zai