← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 114

Sashe 71

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
4
A rikice saudat ta ce" Kar ki bude dan Allah kar ki bude kin ce zaki kuma zaki bude?"
Munnerath ta ce" Idan ban bude bane zamu kara laifi, to wai mema na masa daga dawowata? Kin ga walahi idan ban bude ba ya fara ihu a wajen nan abin hauhawa zai yi sai gyaran Allah, na tabata Mah na kusa dan bata bari ya dakeni, kakarinta shaka ce da ya shakeni kuma kafin Mah ta iso wataranan sai na gala masa cizo a hannu wollah"
Tana fada tana murda ky din ne ta bude dakin gaba daya
Irin dukan kofar da yake, irin yadda yake jijiga kofar kai kace daga an bude zai dauke wanda ya bude din da mahaukacin marin da sai ta ga walkiya, Saudat kanta da ta duke ta rufe ido cike da tsoro da gannin gangancin Muneerath a kan wai tunanin da wanda zai amsheta ta bude kofar nan j'ai n shirun ya yi yawa a hankali ta shiga bude idannuwanta dan gannin ko ha ya shaketan ne ya yi waje da ita
Ido ta kura masu kamar yadda ta ga ikon Allah Muneerath ta bude kofar aman kuma ta ja baya kadan ta tsaya da shigarta tana kallonsa
Tun daga kafarta ya dauko kallonta har ya dire saman fuskarta da ta yi wuki wuki tana kallonsa ta kwashashabe fuskar tamkar zata fashe da kuka
A hankali ya mika hannunsa ya damko nata hakan ya sa Muneerath fadin" Innalilahi kuma taba min hannun zaka yi? Dan Allah ka daina min haka ni walahi irin abin nan naka mamaki yake bani bayan mamanka ce da kanta ta hanna kuma kake yi!"
Hanja ya lumshe idannuwansa a lokacin da ya nufi wajen kofar Iman da ita, ba dan komai ba sai dan kar ya yi magana a gaban Saudat wace take kasa da shi ma'aikaciyarsa
Jikin bangon kofar Iman din ya turata kadan hakan ya sa ta hadu da Bangon tana rintse idannuwanta domin har ga Allah ita idan yana cikin halin nan tsoronta daya kar a samu matsala ya dankareta, fada da namiji ba riba gashi namiji mai aljanu idan ya riketa bata san yaya zata yi da ranta ba hakan ya sa a rikice ta yi gagawar rufe ido tana kuma kai hannayenta dan kare fuskar tata
Huci yake tamkar kububuwa
Gaba daya ya gama hargitsa yannayinsa
Fuskar nan tasa a hade take ta yi jajajir kamar wanda aka tsoma a ruwan zafi ya silgeta
Lebensa kuwa sai shan tauna yake dan tsabar balakin dake kan harshensa
A dake ya ce da ita" Me kike so da ni ne? Me yasa ban isa na saka ki ko na hanna ki ba?"
Munnerath jin yana mata tambayoyi a hankali ta buda idannuwanta
Gabanta ne ya fadi sakamakon idannuwansa da ta kalla cikin ido, haka kawai ta ji kirjinta na dokawa kafin ta cire da sauri, sai dai bata idasa cirewar ba ta dawo da duban nata wannan karron a hankali tana mai son rintse idannuwan tana kuma shakar kamshin jikinsa
A sanyaye ta ce" Me na yi kuma?"
Hanja ya lumshe idannuwansa dan a yanzun da ya tsatsareta sai yake jin fushin nasa na yin kasa kasa a hankali
Hajan ya sa amon muryarsa ya sasauta a lokacin da shi kansa bai fahimci haka ba ya ce" Me yasa ku yan africa bakwa bada amsa idan akai maku tambaya sai dai ku mayar da wata tambayar ne?"
A hankali Muneerath ta dora dubanta a kan damtsen hannunsa da ya cika ya tumbatsa a hankali ta dan yi murmushi ta ce" Kai fa yaya Hanja, to kaima yanzun ba tambayar bace ka maido da ita ba? "
Gefen kunnenta mai dauke da dan saje kwontace a kusa da kunnenta wanda bashi da tsayi sosai aman ya kai rabin kunnen nata kuma bakinsa sosai ne gashin nata hakan ya sa kalar fatarta ta fi shi haskawa, ya kurawa ido yama rasa me zai ce mata
Gannin zata juyo dubansa ya saka shi sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Me ya ce maki?, Dama so yake ya lalata maki tarbiya ko? Ko kuma kema irin mai biye biye kowani shara ne?"
Munnerath ta kwashashabe fuska a hankali ta ce" Wane? "
"Ya Rab" shine abinda ya fada a sanyaye kafin ya ce" Attahir "
Da ba dan ta san waye attahir ba da ba zata iya cenkowa ba, a hankali ta ce" Cewa ya yi yana so na fa, kuma shi din ai ba lalatace bane"
Dole Muneerath ta ringa tunanin ko dai aljannu ne da HANJA, domin yanzun suke magana ta laluma aman daga fadin haka ya shiga fada har yana rintse ido yana hade magana biyu , a fusace ya ce" In ji wa yace ba lalatace bane? Ya rasa wa zai ce yana so sai ke?, To zan kore shi na ga a inda zai ganki! Walahi ki kiyayeni Muneerah bana son shirmen yayume yayumen nan, ki bari idan na maida ke garinku ki kula maza dari ke ta gano ! Aman ba zaki bata mana sunnan gidanmu ba!"
Haushi ne ya shiga turnuketa, idonta ya fara rufewa dan fa ta tsani fa ya ringa nuna wani in ta je garinsu ta bude baja kolin iskanci, hala bai ga yaya tarbiyar nasu garin yake bane ko meye?
Bakinta ta tunzuro ta bi ta kasan hannunsa ta juyo ta ce" wollah ka ji tsoron Allah, wajen cin abincinutun dan ka raba shi da shi ribar me zaka samu? Koma lalatacen ne ina rayuwarsa ce? Kai dai sai dai ka ringa korar mutane kana masu fada ba gaira babu dalili? To ai kaima da Allahn ya baka ba dan ya fi sonka a kan sauran bayinsa bane! Idan ka kore shi ai Allah zai bashi wajen da ya fi wannan, kuma da kake cewa ka maida ni garinmu na yi maza dari ai ni ba yar iska bace ba kuma yan garinmu basa yawo da bingilin sket basa lalata a bayane dai ehe! Kuma Allah na gannin mutun, ni a maidanima na koma gaban Oga !"
Ido da baki da hanci gaba daya ya bude yana kallonta hakama Iman dake tsaye jikin kofarta ta leko ta ya kofar nan ta saki baki da hanci tana saurare
Da ido ya rakata har ta kusa shiga kafin ya zarro ido da ihu ya ce" Muneerath dawo min nan, zo min nan yanzu yanzu!"
Muneerath da ta saka kafarta daya a dakinta ta makale kafadarta tare da turo baki ta shige dakin ta turo kofar tare da murza ky tana fada a bayane cewar" Haka kawai ka ringa wani cewa zaka kori mutun ka kore shin mana, kaima ai sai a kore kan malan!"
Saudat da ta gama saka takalminta a tsorace kar zata fashe da kuka ta ce" Muneerath ni dai ki raka ni na koma dakinmu na hostess na fasa kwanan a nan, yanzu Muneerath bakya tausayin kanki kika yiwa Hanja haka? Zai hada har ni ya kora saboda wannan abin da kika yi, yanzun so kike ya kashe mu ?"
Munnerath ta yi turus tana kallonta, tsakani da Allah saudat kuka take hakan ya sa ta fara tunanin to wai meye na tsoro a jikin Hanja?, Ita walahi hargaginsa da daure fuskarsa du basa ce mata komai, a gidansu meye babu? Akoy mafadatan da asubar fari suke farawa basa dainawa sai duhun dare, akoy kuma wanda idan mutun zaku kashe ba zai kale ku ba dan bakin hali, au dai bambancinsu ba shiga sabgarka zasu yi ba idan suka shiga kuma a fito a caskale ne a ba hamata iska!, Shi kuma sai yana nuna ya mayar da ita kasarta ta je ta aikata abubuwa kamar wata yar iska?
Gwuiwa a sage ta ce" Saudat kali fa, to ba shine ya fara jana ba?"
Daudat ta dafe kunci ta ce" Baki da hankali?, Ko me ya maki ai daidai shine ko?"
Munnerath ta tabe baki ta ce" Ba inda zaki je, idan dan ina gidansu ne za yana wulakantani ai zan samu Mah na ce a maida ni ni na gaji ya ringa min fada dan ya ga kato ne shi !"
Hanja kam abin gaba daya fin karfin tunaninsa ya yi hakan ya sa tana kulewa ganninsa a haukace ya nufi matatakalar gidan da rabonsa da hawa ta nan har ya manta ya shiga tatakawa da gudu gudu yana bale boturan rigarsa domin ji yake kamar ana zuba masa ruwan zafi, gaba daya ji yake kamar zai summa, bai san meye wannan ba, bai san me ke damunsa ba, abinfa dai ya sani shi da Attahir Allah ne kawai zai raba su, baya gannin laifin Muneerath dan ita yarinya ce yana iya koya mata yadda zata wulakanta shi, aman shi malamin shi zai samu ya koyawa hankali, ba zai lamunci wannan haukan ba ba zai iya ba
Nan da na ya sauko daga sama wanda hakan sai da ya tsorata Mah dake zaune rike da result dinsa wanda basu samu komai da ya shafi zazabi ko wani ciwo a cikin jinninsa ba, jira dai sule su auna bp dinsa da matsalar zuciya dan su ga abinda ke saka shi bugun zuciyar nan
Gaba daya suka mika Banda Pah da ya kuma tsura masa ido
Wajen t
phone ya karasa ya dafa wayar ya shiga dadana number office din PDG na a
roport
Nan da nan aka daga
Hanja da ya murza gaban goshinsa ransa bace ya ce" Ka duba sunnan Attahir lawan ka ga me kampani ke binsa ko yake bi"
Da sauro mutumen ya shiga dubawa, daidai Pah ya taso ya karaso wajen wayar ana fadawa Hanja
A hankali ya saka hannunsa ya janye wayar ya kanga a kunnensa ya ce"
11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 71 · 0% Book details