← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 114

Sashe 70

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

kanta da fadin" Son, kishi nake gani a tatare da kai?, Son kishin Muneerath ne nake gani? Son ka fada soyaya? " Lalala kamar wanda yake jira hakan ya fito daga bakinsu, nan fa hali ya motsa kamar ba shine yanzun take kamawa tana kwontarwa tana lalasa kamar wani dan goye yanzun ya firfito ido cike da mamakin furucinta a birkice ya ce" Mah so? Soyayar yau na fara? Wani irin kishi? Ni? Kishi? Ni ban san kishi ba! Ke fa kike cewa yar amana ce kuma ta kiyaye du wani hulfa da wani, kuma ni fada ne nake mata in na ga na hanna ta tana yi, barama na tarda ita sai ta fada min abinda wannan sakaran ya fada mata kuma shi sai na kai shi conseil kafin na kore shi dan na kula yana cikin masu lalata mana ma'aikatanmu!"""""""""""" Fuuuuuuuuu ya mike kamar ba shi aka gama rikewa bashi da lafia ba ya nufi lft Da sauri Mah ta mike tana kiran sunnansa Pah ya tiko hannunta yana daria a bayane yana girgiza kansa ya dawo da ita saman kujera sunna facing din junna Irin yadda hankalinta yake tashe ya saka shi kara yin dariar da ta jima bata gani ba Har dafe kansa yake a hankali ya ce" Alhamdulilah" Mah a sanyaye ta ce" Du sai na ga kamar ba kai na, du sai na ga kamar baka damu da damuwarmu ba, duba fa ka ga halin da yake ciki, kuma duba ka ga ya bi bayanta kar ya daketa" Pah dake daria a hankali ya ce" Ba zai iya dukanta ba" Mah da bata gamsu da maganarsa ba ta ce" Ka fa san zafin ran son idan ransa ya baci, abu kalilan yake zartarwar da hukunci mai tsanani, bana so ya taba lafiyar yar mutane kafin na maida ita wa ahalinta" Pah ya karra yin daria domin shi rabonsa da gannin nishadi irin wannan har ya manta, wai shine yau da idannuwansa da ransa da lafiyarsa ya gama gannin sc ne din kishin yaronsa? Ya ce" Ya yiwa wa duka? Ni sai kawai na ga idan abu ya shafi yaronki ne sai ki rikice ki kasa gannin komai, ai Muneerath ta fi karfin dukansa sai dai ta dake shi! Kuma idan kika yi gigin mayar da ita wa iyayenta a yanzun a awani kusa zaki zama wada zai yiwa kallon mai son raba shi da numfashinsa.......yaronki ya yi wasa ya zurma da yawa, ya yi sake ya zurma a duniyar da bata damu da shi ba, ina mai taya ku da adu'ar kar ku yi wani wasan da zaku haukace ku rikice ku rasa gane yarenku!, Kin ga barni na gama bincikena a kan lamarin Muneerath" Jikin Mah a mace, cike da rashin karfin jiki ta dora kanta a gefen kafadar Pah a sanyaye ta ce" Ya Allah ka kama masa, yarona karami ne, bai iya kokowa a kan abu ba, Allah ka bashi , ka sasauta masa ya rab, ka sa wannan rigimar ta zama mai sauki a tare da shi, ka sa yarinyar nan yi masa kallo irin wanda yake mata...." Murmushi kawai Pah yake ya kurawa hanyar da ya bi yana jiran gannin saukowarsa a haukace Hauka suke zubawa tuburan Gaba daya Saudat ta kasa yarda cewar wai da gaske dakin nan na Munnerath ne Ihu suke na arziki sunna bude bude da ciro dogayen rigunna Kida na wakar hausa suka saka sunna casu abinsu tare da kyakyata dariar shirmensu Saudat ta ce" Muneerath, girman ubangiji ya fi gaban tunanin bawa, wai da gaske baki da shamaki a palace din nan? Muneerath kina kallo Sir HANJA gamu ga shi a gidansu yana kallonmu? Munnee wai kuma baya maku fada a nan?" Muneerath ta zauna saman gadon da yar rigar dake jikinta sai dogon wando ta talabe habarta ta ce" ke sangarta ce fa irin ta yan baci, wollah a nanma bini bini yana fada, bini bini mamansa na rarashi har mamaki nake, yo da gidanmu ne oga da matansa ba sai dai su idasa haukata zuciyarka ba dan ka kasance mai fushi wollah matsalarka!, Aman a nan kin ga idan ya shigo an kama kamo shi, ana wani shafar kansa, ana wani zabura ana kawo masa abin tabawa, kai kudi jaraba ne, kamar wani sarki saima kinnga yadda wannan yar uwar tasa take masa haukan so? Sonsa take kamar ta mutu" Saudat ta zarro ido ta ce" Tap, aman ta dauko ruwan dafa kanta, baki ga wata rantsatsiyar budurwa da ta shigo da bakar riga a jikinta ba? Wannan budurwar ni nan ni nake kallonta ina karawa baki ga kyau ba, luwai luwai da ita, yar wannan mahaukacin mai kudin ce kuma ita kadai ya malaka a duniya, ke itace fa budurwarsa ita ta bada makudan kudade wa kampanin aka shiga shirya masa karya karyar nan, daga baya da kampani ya nuna na zai amshi kudinta ba ta nuna wannan kadan ne ta shirya masa wata salar ta birthday dinsa a wani wajen wannan tana so ne ta ga yaya zai dauki lamarin, ke kin ga abin wai? To Allah sai ta yankata a kan Hanja, kuma da kike cewa kamar sarki an fada maki ba sarki bane? Shi fa zai gaji abansa" Muneerath ta yatsina baki tana girgiza kai ta ce" lale, to ita tsakani da Allah kashe kashen kudin na menene? Ni mamaki suke bani da suke nunawa kato so, yo Allah na tuba ka ja zarenkama yaya ka kare da namiji bale ka nuna zakewa? Da hakuri ta yi har ya nuna yana sonta sai ta yarda, kuma ni du in kika ce sarki daria kike bani kali fa kin taba gannin sarkin garinmu fuskarsa a bude? Ji fa shi wannan fuskar tasa kulun a bude take gashi dan kyakyawa da shi sai fada kulun kulun" Saudat ta yi daria tana bude computern Muneerath ta zauna gefen bed din ta ce" Ba zaki gane ba, bara na shigar maki tarihin masarautar kasar nan sai kin haukace Tankwashe kafafuwansu suka yi inda Saudat ta shiga duniyar yanar gizo dan ta nunawa Muneerath me ake kira da sarauta , ta kuma ganar da ita cewa Allah ne ya tsaya mata ba kowa ba da har ta samu arzikin nan, ta ganar da ita cewa Hanja sarki ne mai mulkar saraki, ta kuma ganar da ita cewa ba wai rawanin bane shedar sarautar domin da rawanin ne da kowama ya naa ya kirayi kansa da sarki Sunna shirin fara afkawa duniyar saraki aka shiga dukan kofar tamkar za'a karyata, karan da take ke iya nuna maka cewar ba mai karamin karfi ke dukanta ba A tare suka zabura sunna kallon kofar Saudat ta ce" Mun shiga uku waye?" Muneerath ta diro da sauri ta je ta dan buda ya kofar da kake lekawa dan gannin mai bugawa dannita kanta tunda ta zo gidan nan ba'a taba buga mata kofa a haka ba, hakan ya sa ta tsorata da jin dukan kofar na yanxu Da sauri ta dora hannunta saman kanta ta kallo saudat ta budi baki ta ce" Ubanmu zai ci walahi zaki ne da shi min shiga uku" Saudat ta fita kidimewa domin ita cen dama tsoronsa take din, duda baa gane waye din ba kalmar ubansu za'a ci ya sakaa rikicewa ta duka tana kokarin fashewa da kuka , sai dai bata yi ba gannin Muneerath ta nufi kofar kuma da nufin budewa a haukace ta ce" 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 70 · 0% Book details