← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 114

Sashe 75

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a nuna maka kauna ake maka hakan ba, sai dan a nunawa duniya in masifar take nema ta tardo gidan, shi yasa ni bana kai masu fadana, idan na ga an fi karfinama sai in yi Allah ya isa walahi,.......aman abinda yake bani mamaki Saudat shiru ba Oga ba Mamanmu ba kowa nawa harda shi mai son na yi karatun ko bai san bana gidan bane? Daga wannan ranar ta ringa yiwa lamarin Muneerath uzuri, daga nan ta ringa fahimtar dukan wani abin na gabonci, irin na mamakin nan idan Muneerath ta aikata daga mahaifiyarta ne, iyaye mata sune masu koyar da y'ayansu lamarin rayuwa, uwa mahaifiya ita ce zata bambancewa yarta komai , ciki kuwa garda karatun da ake basu a rufe a islamiya, yawanci malamanmu ba zasu fito maka a mutun dan su ganar da kai wane ake nufi ba, hakan kuma ya dauko asali ne daga irin yadda y'ayan na yanzu kyar sun san me ake nufi dan an basu magana a rufe to fa tabas sun san ina ta nufa sai dai a kalli junna, aman kuma sunna mance cewa akoy masu hali irin na Muneerath, inda Allah ya taimaketa ita Muneerath din, ya kasance yarinya ce mai masifar tsoron harkar D'a namiji, kai ko fadan fa Muneerath ba wani karfi ne da ita ba, ita dai barta a wajen harkar kin tsoron waje, kai magana fa idan ta yo niyar fitar da ita fitarwa take ko a gaban waye! Munnerath da ta mike tana juya kugunta shima duka a cikin yannayin dan motsa jikin da take ne ta dakata da sauri ta ce" Ke ban fada maki abinda Mah ta ce ba, ta ce walahi talahi du yarinyar da ta yarda namiji ya zo mata sai ciki kawai, na ce wai wani iri sai Mah ta ce ko hannuna na yarda ya taba, kin ga yaron nan nata ko? Sau biyu yana rukunkume min jiki, dan Allah dan na tsorata na yo wajenka ai sai ka wankan mari na ankara namiji ne kai, sai kawai na duba da kyau sai na ganni a jikinsa, Allahma ya sa Mah ta ce sau biyu kawai ba abinda zai samu aman ina yarda na uku ya faru an kare" Zuwa yanzu tsakani da Allah tausayin kawar tata take sosai , duda idan ta dauki wani wajen kasantuwar Muneerath a haka shi ya fi daidai da rayuwarta duba da irin kirar da Allah ya yi mata da ace ita din mai kwaramniya ce da maza sun gama sukuta a kan dokin nan nata sun kara bude shi ta yadda zata zama dokin yan duniya, domin namiji karya kake ka ce zaka iya zagaye shi, idan ka ci riba a kan wani, a kan waninsa ba zaka kai labari ba, sai dai kuma idan ta bi wani bangaren na idan fa akaiwa Muneerath aure aka kaita a haka mijin ya nuna manufarsa da abinda zai kai hannunsa wanda ya zarce runguma za'a kwashi diyan kallo, may be ta sume masa ta yadda ba zai iya anfani da ita a haka ba, ko kuma ta haukace gaba dayama da kuka, ko a zaman gidan horon Hosteesss da suka yi irin tsakaninsu yan mata wani lokacin baka jin kunyar cire rigarka ka saka wata a saman bra dinka, ita bata taba haka ba, saima kowa ya bar dakin take cire nata kayan a labe ta cenza, to ina da namiji ya ce ga abinda zai taba? Kallonta take tana ta kokowa da tunaninta, shin ta sanar mata abinda yake faruwa asalin meye yake iya faruwa da ita a lokacin da ta auri namiji ko kuma ta barta idan aka ce yau an daura aurenta koda tana nesa ne ta sanar mata? Ko kuma a yanzu take zaunar da ita ta yi mata ainahin karatun fari fari ta yadda zata san me ake nufi da kalmar *YA ZO MIN?* Tana kallonta ta ce" Muneerath zauna mana mu yi magana?" Muneerath ta juyo ta ga yadda Saudat ta yi kala irin na serieus tana kallonta watau jira take su yi magana da alamu mai mahinmanci ce Kokarin zama take aka yi knowkng din kofarta Da sauri ta juya tana murmushi ta ce" Yau dai Mah ta makara, kin san tun dazu idan na kalli agogon cen mamaki nake har yanzu shiru? Mah ba dai sabko ba yau ta makara zan kuwa yi mata daria na ce Mah na yi sallahta a kan lokaci, ian zuwa Saudat sai mu yi maganar" Tana fada ne tana karasawa ta bude kofar Abinda aka fada mata ne ya rikitata, ko dakatwa ta yiwa Saudat magana bata yi ba ta shiga bin Likitar doctern mace suka nufi ainahin asibitin dake Palas din wace take nan domin kula da lafiyarsu Har gani take sun kasa karasawa duda a mota aka dauketa, gaba daya ta rikice Tambaya take yaushe ? Wa ya kaita asibiti ? Pah ya dawo ne? Kwata kwata Muneerath ta manta shigar dake jikinta ta kayan barci na roba masu bin jiki masu kananan gannaye kanta kuma ba hula a kame a tsakiyar kai sai takalmin dake kusa da bed dinta wanda yake kafarra wanda Mah ta hannata taka tiles din gidan nan ba takalmi, sai farar safar dake kafarta wace yanzun saka safa ya zame mata jiki sam bata zama ba safa a kafarta Tambayoyi take ma likitar tana bata amsa har suka isa suka fita Iman ta ganni zaune tana hawaye hancin nan ya yi jajir hakan ya sa gabanta ya yanke ya fadi da gudu ta nufi iman tana tambayarta ina Mah din ne? Ko ta mutu ne take kuka haka?" Rai bace ta mata nuni da dakin da manyan dakarun sojoji ke tsaye wa'inda ita bata taba kula da su a gidan ba wa'inda har ga Allah sai da ta ji gabanta ya fadi na tsoronsu da ta gansu , aman da yake a yadda iman ta fada mata bata mutu ba da haushi ta ce" Shine kike yiwa mutane kukan iskanci a nan, ki yi mata adu'a mana Allah bata lafia haka kawai ki saka ni faduwar gaba karfe tara na safe ko karyawa ban yi ba?, " Sai kuma ta sasauta muryarta ta ce" Iman dan Allah raka ni mana na ganta wa'innan na tsayan da alama basa son iskanci, kin gansu kar na he su mareni su kurumtani kin ji?" Iman ta kauda kanta tana gunguni da tunanin lale Muneerath ta raina mata wayo, Bodyguard din na HANJA na dare ne bata sani ba? Mutanen da idan dare ya yi ko Pah basa bari ya shigo kai tsaye bangaren Hanja sai sun tabatar da Pah din ne ita da take tafia da shi kusa da kusa har sunna fada zata nuna bata sansu ba? Munnerath gannin dibar akbarkar ta iman ta tashi sai ta kebe bakinta ta mike tana kade gefen cinyarta ta kale su ta yi adu'a ta nufe su dan ta tabata Mah na ciki idan kuwa tana farke ba zata so ace ta zo bata shiga ba, ta ga damar ana sakinta ta kama yi mata nasihar zumunci da kula da kwadaita mata lada a gannin marar lafia Da ta tsaya a gabansu sai da ta raina tsayinta da kibarta, 'kamar yan tagwayen d'an Mah' haka take fada a zuciyarta Sai da suka dubata da wani abu a hannun su har fuskarta da kyau kafin su bata hanya ta shiga , dama Iman ce ta bada umarnin a daukota domin itama da ta shiga ta tarda Mah a haka shine fa ta sanar da Hanja kafin ta sanar da likitocin , a yanzu da aka gama treatmen din Mah sai ta saka a kawota dan ta tabata idan Mah ta farka bata ganta a tare da su ba tana iya bata rai Tunda Muneerath ta sanyo kafarta ya dago kansa daga zaunen da yake dare dare a saman bed din asibitin mai daukan mutun har biyu domin yana da fadi gaskiya ba irin matsatsen bed din nan bane , ya yi irin zaman nan kan Mah a saman cinyarsa hannunta kuma a cikin nasa , kanta sanye da hular mararsa lafiyan mai hade da kayanta, jikinta kuma rufe da bargo sai wajen fuskarta da kanta ne suke bude, ga dukan Alamu barci take yi Da farko da dan karfi karfin tafiyarta ta shigo wajen, sai dai cikin ikon Allah daga bakin lokacin da ya dago da idannuwansa masu duhun haske ya sauke a saman fuskarta ya tsayar da dubansa kyam a cikin nata idannuwan da fuskarsa da ta yi ja, wace ta kula da zarar hankalinsa ya dan tashi daga fari tas sai ya dawo ja , sai ya zamana tafiar tata na rage sauri, har ta dawo tamkar an zare mata lakhah ne take neman tabulewa ta rufta kasa dan gaba daya sai ta nemi karfin jiki ta rasa kuma dan wani balaki ta ki cire duban nata a cikin idannuwansa har ta idasa kusa da su daf da daf tana mai kai hannunta na dama ta rike abin gadon dan ji take kamar wace ake jijigawa anai mata juwa , yannayi dai kamar na wace ta kurba bayan ita din nan ko goro bata ci A hankali ta cire nata duban daga nasa dan ta kula HANJA mutun ne mai irin kallon nan da ake cewa ba kyau, watau haramtacen kallon nan da aka hanna a musulunci, irin kallon nan na a kafe mutun har a gano muninsa, kai in ba hanja ba ni kuma munina ai a bayane yake kau? So dai yake ya samu na cewa na masa bayan mamanshi ba lafia, koda yake ai aibun sangarta yaro kennan, sai mutun ya sangarta yaro yanzu haka kuka ne yake dan mamansa bata da lafia da ya ji motsina ya fuske, a banza bayan na gama sannin kai din dan akoke ne a gaban Mah da Pah' A hankali kuma a lokacin da ta shafa gefen fuskar Mah ta ji ba zafi jikin ta kuma ga yadda take barci, ta kasan ido ta kuma lura da fa ita yake kallo walahi sai ta samu kanta da tunanin me yasa ya cika kallo?, Du abinta ta gane cewar shi din mai yawan kallo ne uwa namijin
Chapter 75 · 0% Book details