Sashe 79
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 5 Bayan kwana biyu Kula ta musaman, jinya mai girman daraja Mah ke gabatarwa a gefen mijinta, hakan ya saka Hanja fita dukkan wasu taro na Pah da kuma jagorar da yawa a cikin Palas a baban dakin taro Wannan al'amari ya dauki hankalinsa sosai harma ya yi kwanakin nan ba tare da ya saka kafarsa a filin jirgi ba, hakan ya matukar bashi mamaki da tunanin dama akoy abinda zai hanna masa leka tsuntsu marar numfashinsa? Sai dai wani abin ya fi gaban wani, watau a yanzu da ya tsaya ya fuskanci mecece matsayin gadon da ya tabata ko ba dade ko ba jima idan dai da ransa da lafiyarsa ko da ran mahaifinsa ko babu ya zame masa dole da karfi da yaji ya mulki kasar sai wani dari dari ya kama shi Shin yaya Pah yake yi yake walwala?, Kai gani yake da shine harta walwala rasawa zai yi, ko dan shi din farin shiga ne? Yaya Pah yake yana samun time isashen da yake ganninsa zaune a falo? Yaya Pah yake har yake gane iyalinsa nada matsala ko sunna cikin farin ciki harma ya basu lokacinsa? Tabas a yanzu ya yarda cewa shi din bako ne kuma yaro ne karami a duniyar nan wanda yake da bukatar a kama hannunsa Gefe guda ga wannan nataciyar yarinyar da tunda sunnansa ya fara yawo kan Media a matsayin wanda yake gabatar da aikin babansa harma sunnan da ake kiran mahaifin nasa maimakun prnc kamar yarda ya saba ya hau kansa aka fadi dalilin cewa yana cikin hutun kula da lafiyar matarsa ne take aiko da takardar neman izinin samun damar shiga Palas din dan ta ga jikin Mah da ita da iyayenta Ba dare ba rana sai an sanar masa da nata sakon a cikin sakwani hakan ya sa yau ya yi croi samanta dan ya gama da tata matsalar kafin ya fuskanci yan hutun nan su amshi kasarsu su rufa masa asiri, tsakani da Allah tunanin da kwakwaluwarsa da zuciyarsa take cikima ta fi komai adabarsa a irin lokutan nan Tunda ya sauko daga matatakalar gidan tare da Tgr dake tafia ta kasaita yake jiyo muryarsu da yar dariyarta A hankali ya jinginar da bayansa a jikin garu ya samu kansa da saurin lumshe idannuwansa yana mai bin hirar da take yi tana gaurayawa da yarenta da bai iya ba domin a yanzun tana french ne da kuma ainahin hausa tamu gangariyarta abinta sunna labaru irin na tsegumi da kuma hirar dangi ita da aminiyarta a saman table sunna cin ganima sunna kora jus , iman kuwa na kwonce a saman doguwar kujerar Falo tana sanye da earpc a kunne tana sauraron wata tsumamiyar wakar larabawa tana lumshe ido Sai da ya gaji dan kansa Tgr kuwa tana kai kawo a daidai wajensa kafin ya sauke dubansa a kan Tgr Haka kawai ya samu kansa da sakin murmushi yana mai son gannin tsererenta idan ta ga Tgr A hankali ya ci gaba da takawa ya idasa fitowa gaba dayansa direct ya nufi wajen Dinern hankali kwonce Sansanyan kamshin turaransa ya saka an lumahe idannuwanta kafin ta dago dubanta a hankali, sai dai abinda ta gani ya sakata saurin maida kan nata jikinta na rawa ta yi shiru tamkar gawa danma kar a ji motsinta a wajen har suka wuceta suka fara taka yar matatakalar hawa wajen table din Yar shewa Muneerath ta saki tana kai hannunta kusa da kafadar Saudat ta ce" Ke dillah ki bari, yanzun dan zai zo zance sai ya shigar da takarda?, Ai yau yau zan saka a kawo shi zance gidan nan ya kuma shigo har falon nan mu zanta mu fafata abinmu, ai dai zaki zauna a kusa da ni ko?" Saudatma ta yi yar dariyarta ta ce" ai kece fafatawar, kin ga a yadda ya damu kan yana so ya ganki gashi kwana biyu cif tunda muka shigo bamu ga waje ba ya dace mu dan sama masa dan time dinsa , kin ga fa soyaya ciyar da ita ake ba mantawa ake yi da ita ba fa" Muneerath ta dan talabe habarta ta yi luuuu da idannuwanta a hankali cikin yaren turanci wannan karron ta ce" Ban san zan so wani halitar da ba dogari ba Saudat, wani sa'in sai na ji ina son Sir sosai bale idan kina koda min shi sai na ga ai shima da nasa ikon a inda yake, ya Allah ka yaye min matsalar sarauta dake zuciyata na fuskanci abin sona mu so junna mu yi aure" Saudat ta girgiza kanta da dan kari kari ta ce" Dogari?, Wai dan girman Allah su rasa ina zasu sauko ki sai nan?, Dogari mutun ne mai daraja aman a kan me zasu sauko maki burinki na son zama sarauniya?, Ai ba'a sacewa bawa gwuiwa komai kaskancinsa domin ba'a san meye Allah ya boye a tare da shi ba, waye ya san gobe ne?, Kin wani damu dogari dogari kin kuwa gane ainahin aikin dogari? Dogari irin na kasarmu?" Muneerath ta mike daga zaunen da take, hakan ya sa doguwar rigar dake jikinta fara ta idasa sauka tana rawa a jikinta ta dan watsa hannayenta ta ce" Ba zaki gane ba, ni fa ba wai kudinsa ko wani yannayin rayuwarsa bane damuwata, Saudat buri ne da mafarki da na tashi da shi yake bani wahala, ki duba ki ga irin wh....................." Katsewa maganarta ta yi a lokacin da idannuwanta suka sauka a kan fuskarsa Sajen fuskarsa mai kyalin baki da lebunnansa zuwa uwa uba fitinanun idannuwansa masu kallon wuce ka'ida da ya zuba mata Sanye yake da suit ash color masu farar riga a ciki mai duhun haske Gashin kan nan nasa ya sha mahaukacin gyara sai kyali yake Da farko a kansa dubanta ya tsaya, ta yi ta yi ta cire ta kasa aiwatar da hakan , hakan ya sa ta samu da kyar ta lumshe idannuwanta tana jin wasu kwala sun cika mata su masu zafin da suka hadasa mata jin ciwon ido kafin kunnayenta su jiyo mata amon muryarsa ba ihu ko kadan cen kasa kasa ya amsa kira a wayar dake hannunsa ya ce" Ka sanyo su baban falo nan da awa guda idan na gama karyawa" Yana gama wannan ya danna wani kiran wanda yana dagowa ya kuma saukewa a kan furkarta da yannayinta kafin ya saci kallon Saudat da ta mike itama ta sada kai jikinta na dan bari tamkar yadda suke mada a wajen aikin nan, ya kuma maidawa kan Muneerath wace bata taba yin barin nan dan yana waje ba ya karra zuba mata ido, dan siririn dan kwali fari ne a yane a zagayen lakausan dogon gashin kanta mai cika daga gabam goshi sosai, sai yar siririyar agogo fara A sanyaye ya ce" Ka zo ka dauki Tgr " Daga haka ya katse kiran yana kallon lokacin da ta kalli Saudat a dan zabure wanda ga dukan alamu a yanzu ta fara gane tare yake da tgr din A hankali cikin dabara ta ringa kallon kasa kasa har idannuwanta suka sauka a kan Tgr dake zagaye shi tana kada bindi Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke a bayane kuma kasa kasa sosai ta ce" Wayo Allahna, ta yau dinma ta kirkin ce, kuma gashi ba Mah ba Pah a kusa, ga yar mutane tana tare da ni , gashi inaga haushina yake ji dan sai hararena yake..... innalilahi Saudat Zaki.........." Ta idasa maganarta da dan daga murya wajen ambatar sunnan Zakin da hausa tana kwalalo ido ta nunawa saudat da idannuwanta.......... Saudat gaba daya ji ta yi tamkar zata suma, haka jikinta ke rawa ta rasa yaya zata yi daga tsayen da take A hankali ya dagakafarsa ya kara taku daya dan karra kusanta kansa da Muneerath, sai dai abin daria yana yin taku dayagaba tana yin daya baya idannuwan nan kuwa tamkar zata dauke shi da su Sai da ya gama murmushinsa na yannayinsa a cikin zuciyarsa kafin da hannayensa ya nuna masu wajen zama da yatsarsa daya ya kuma nuna cewar su zauna , ya kuma dan nuna alamun idan ba haka ba........ya karasa da dantse lebensa, daidai lokacin kuma mai kula da bangaren Mah ta same shi ta waya da tambayar idan har yanzu su Mah zasu sauko su gaisa da bakin?, Ya shaida mata lokaci kafin ya kara sauke masu kakausan kallo a kansu wanda ya saka a birkice du suka samu matsugunni suka tsuguna duwawunsu A hankali Muneerath ta saka hannunta tana ture dan kwalinta da hannayenta kuwa tana firfita tana satar kallon yadda Saudat ke share hawaye kanta a sade baiwar Allah Karasawa ya yi ya ja kujera ya hau ya zauna kafin ya shiga shafa bayan Tgr dake daf da kafarsa yana hankalce da yadda Muneerath ta nade kafafuwanta kawarta kuwa sai hawaye take Dan gyaran murya ya yi ya nuna mata abincin da idannuwansa sannan ya nuna plat olat din dake ajiye A sanyaye ta ce" Toh " Ta mike tana sarar kallon Tgr ta bubude abincin Bata tsaya tambayarsa ra'ayinsa ba ta zuzuba masa abincin ta ajiye da cokali sannan ta tura masa mg din jus din ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya Da gaya, da neman fitina, da ba bawa wahala ya ringa takalar abincin kadan kadan su kuwa sunna zaune zuciyoyinsu na dukan tara tara inda Muneerath ke bin hannunsa idan ya dauko abincin a kasan zuciyarta tana ta ayanna dama ba Tgr a kusa Allah yau da sai ta kwaba masa abincin nan idan yana so ya yankata!, To dan dai Tgr dai daba ce, daba kuma mai cinye mutun murus wace ita nama shine abincinta danye ba dafafe ba, hakan ya sa ta nutsu ta yi shiru tana sauraro har daidai lokacin da wayarta ta dauki ringin cikin wakar hausa mai taken tatausan lafazi A hankali ta kai hannunta ta dauki wayar tana duba sunnan dake sama baro baro an rubuta Freind Dan murmushi ta saki hade da sauke ajiyar zuciya a hankali ta daga idannuwanta a kasa kafin ta dan dago da dubanta ta sauke a gefen da yake A karro na hudu idannuwansu suka kuma sarkewa da junna, da sauri