← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 114

Sashe 87

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

5 Murmushi ne kwonce a kan fuskar Pah, inda damuwa ta bayana a kan fuskar Mah A hankali ta kamo hannunsa tana kallonsa da kula ta ce" ba fa faduwa bane dan ka yarda cewar kana cikin soyaya, Son ba faduwa bane dan ka yi kokarin gyara soyayarka, sam bana so ka zamo mai wasa da damarka , Son idan ka yi sake da maganar Muneerath bana tunanin in ta juyar da muradinta ta yarda da shi a kan wani in zaka iya karkatota ta dawo gareka, ka ga , ga number mamanta wace na samu tun a daren da na yi rashin lafia da kuma number mahaifinta, numberta ta cen ce a wahen Pah dinka na yi na yi ya bani ya kiya ya ce sai ka nuna kana so da kanka, plz Son kar ka rikita ni , damuwarka na damuna fiye da tunaninka" Idannuwansa dake lumshe yana jin gaba daya magangannun mamansa na samun matsuguni a cikin zuciyarsa kafin ya kaleta a hankali yana karra karantarta Kansa ya maida kan mahaifinsa da ya ga shi yake kallo kafin ya dan yi gyaran murya a nutse ya ce" Pah, maganar taron nan naku da Allah ka halarci abinka, ka ga inada tafia a satin nan mai yawa plz" Hankalinsa ya bashi kacokam duba da magana ce mai mahinmanci wace yake so ya halarta taro ne na manyan sarakai da matansu da zasu halarta a cikin satin nan , tunima sunna kasar shine bai basu lokacin zama da su ba, kuma so yake a yi zaman da Hanja aman yake son kara zile masa kamar yadda ya saba, shi kam bai san dalilin da ya sa HANJA ke zilewa sarauta ba, wannan abin na hadasa masa ciwon kai da zafin kai mai tsanani, Hanja shine kadai gareshi kuma da shi kadai yake takama, shin yaya zai yi ya taro shi ne? Dukkan hanyar da zai bi dan ya ginar da shi ita yake bi, ko ba maganar rashin lafiyarsa dole zai bashi kujera ya hau ya gabatar da nasa zamanin, shi yasa daga ranar da ya ga yarinyar nan ta saka shi magana ya ringa farin ciki A yanzu haka idan abu ya shafeta irin yadda yake magana fiye da misalin yadda ya saba ke saka shi tunanin tabas wannan itace wace zata budi bakin birkitacen yaronsa ta koya masa magana da kowa , ba halaya na yadda ya ga dama ba bayan ahi din sarki ne wanda dole zai saurari al'uma, a yi mulki a yi isar a kuma tausayawa talakawa Dan haka yau zai cenza masa ya fara zuwar masa a kaisashe dan ya ga kuma yaya zata bada, dan haka sai ya kure shi da duba a kausashe ya ce" Saurara Hanja, wannan tarron ba shawararka nake na ba, umarni ne na baka kan kai zaka halarce shi! Dole ne kuma kai zaka halarce shi, idan kana so ba a satin nan ba kana iya saka rana ka halarce shin, fa wayata nan ka cire numbobinsu su hudu ne, idan ka saka rana sai ka sanar masu da wajen da kake ra'ayin ku yi tarron!" Yana gama fada ya ajiye wayar ya mike fuska a hade ya yi gaba Da kallo suka bi shi su dukansu kafin Mah ta dubi Hanja Sai da gabanta ya fadi gannin irin bacin ran dake kwonce a saman fuskarsa Ta budi baki zata yi magana ya mike a fusace ya juya ya nufi kofa hakan ya sa ta mike tsaye da sauri tana kallonsa har ya bar falon gaba daya A hankali ta zauna tana dan dafe cikinta dake mugun murda mata kasa kasa sai kuma ya saka tana lumshe idannuwanta A hankali ta bi hanyar da Pah ya bi da kallo tana mai tunanin Me ya yi haka? Me yasa bai bari ta lalaba shi ba kamar yadda ta fada masa cewar ya barsu ta lalaba abinta zai halarci tarron? Me kuma ya sa ya ce da ita tare zasu gabatar kuma yanzu ya nuna Hanja kadai zai gabatar? Kanta ta sada tana dan barin jiki na irin murdawar da cikinta ke yi har ya lafa kafin ta mike a sanyaye tana jin yadda jikinta du ya mata wani irin nauyi Hannunta ta mika ta dauki wayar mijin nata a hankali ta shiga contact dinsa Sunnan da ya yi svng din number Muneerath ta kuma maimaitawa tana murmushi watau shi har ya ganta a matsayin matar yaron nasa ko? Domin da Wife LION ya saka sunnan A hankali ta dannawa number kira ta karra a kunnenta Maimakun ta bi ta lft sai kawai ta bi ta wajen matatakalar tana takawa a hankali har aka daga kiran Salamar da Munnerath ta yi ya saka Mah dan zarro ido tana murmushi ta ciro wayar daga kunnenta ta kuma maidawa a sanyaye ta dakata ta amsa salamar kafin ta ringa sakin murmushi na irin murnar da ta ji Munnerath na yi tana ta tambayarta yaya gidan me suke yi? Tana missing dinsu, sai dai sam bata ji ta tambayeta mutumen da take so ta fara tambayarta shi kafin ta tambayeta kowa A sanyaye Mah ta ce" My baby, yaya gida, ina mamanki, ina Abunki da yan uwanki? Ina kowa da komai? Yaya garinku?" Muneerath dake kallon mamanta tana murmushi wace ta tsaya a kanta da muciya kan walahi idan bata murje miyar yodon da ta kada mata ta kadu da kyau ba sai ta muka mata muciyar nan, inda Saudat ke kwasar dariyar scene din, domin a yau a kicin din mamansu Muneerath din suka kusan wuni a kan girkin tukakiyar shinkafa da miyar yodo, ana yi ana sakewa ta sha dunguri da rankwashi, ta sha wani irin daurin zani sai zufa take tana ihun ta kone maman nata kuwa tana tsaye ta yi murmushi ta sha murrr sunna girkin su uku , sai yan kannenta yan mata biyu da aka saka barar tafarnuwa ne, gyaran daki da wankin bayi Amsawa take tana cewa mamanta " Mamanmu Mah dina ce " Murmushi ta saki tana kallonta, domin labarin Mah , da Pah, da Iman, da HANJA har gajiya take da sauraro ba dare ba rana Wayar ta mika mata sai dai ita bata iya turanci ba, Mah kuwa french din nata ba mai tsayi bane hakan ya sa sai gaisawa kawai suka yi a rarabe kafin Munnerath din ta amsa Mamanta na cike da mamakin wai dama da gasken da sarauniyar ingila suka gaisa? Da gaske sunne suka rike mata yarta haka? A hankali Muneerath dake daria ta dan fara ragewa tana sauraron Mah A hankali yannayin tashin hankali ya fara bayana a kan fuskarta a raunane ta ce" Mah, dama Pah bashi da lafia aman na zauna da ku ban taba fahimtar hakan ba?, Mah dama kuma kunna da damuwa bayan kun malaki komai na rayuwa dama kunna iya neman wani farin ciki ku rasa?" Mah ta yi dan murmushi tana lumshe idannuwanta domin ji take cikin ya fara motsa mata Sai da ya sasauta mata a hankali ta ce" Muneerath kowani bawa da tasa irin kadarar, You see my baby a haka da muke ciki da za'a ce mu miko komai mu wayi gari Pah ya samu lafia, my boy ya ajiye aikin tukin JIRGI ya dawo ya yi aure ya haifa min yan jikokina da zan iya rantse maki ko baya ba zamu duba ba zamu saki sarautar Ingila" Da wani mamakin Muneerath ta ce" Mah, dama bakwa So sir na tukin jirgi? Tukin jirgi fa mafarkinsa ne, abu ne da ya fi kwarewa a cikinsa, aiki ne wanda idan yana yinsa yake cikin farin ciki, idan ya bar aikin nan wane kuke so ya kama?, Kuma aure yana da yan mata fa ku masa jan ido ya fitar da mace ko ku masa na dole" Mah ta yi murmushi a sanyaye ta ce" Baby kin san wanenen HANJA?, Allah ya yi shi mai daraja a cikin bayinsa, domin sarakai sunna da daraja sosai yarinyata, HANJA shine yaro daya kwal da ahalin sarautar babar masarauta ta duniya watau Ingila ta malaka, babu maganar tirsasa Hanja a aikata komai sai dai mu rarashe shi, Hanja yana da dama , yana da mulki mai girma wanda ubangiji ya halice shi a cikinsa, Tuki, aikin karfi ko wani iri ne dan nema ko dan sha'awar hakan ba na HANJA bane, HANJA yana da obligation na al'umar kasarsa, Hanja yana da abubuwan da suka zame masa tilas wa'inda suka daki burinsa, da sha'awarsa suka shigo a duniyar dolensa, My girl HANJA bashi da zabi yana aikin tukin jirgi ne dan mahaifinsa na so ya cakudu da al'uma ya koyi rayuwa da su, Sai dai kashhhh a yanzu haka maganar da nake maki mahaifinsa a yau ya taka da kafarsa ya je ya buga takarda da tambarin masarauta da sunnansa a matsayin wanda ya saka hannu dan dakatar da shi aikinsa, ba zai kuma yin aikin da ba nasa ba, komai sonsa da tuka jirgi ba zai iya fita daga gidan nan ba, baby i'm afrd, ina cike da tsoron abinda ke iya faruwa a yai a cikin gidana, Pah dinku ya dauki zafi sosai ya dadauki matakai masu tsaurin gaske wa'inda na so ya barni na lalashi Son na dora masa nauyin da ba zai iya zubar da mu ba, sai dai bai bani damar ba ya karra dora masa wani hawan jinnin wanda nake cike da tsoron abinda ke iya faruwa, kina gani wai fa ya bada dokar kar a bar Son ya fita daga PALACE" Muneerath dake saurare kanta ya daure, ta kasa gane me yasa Mah ke mata hira irin wannan ta sirrin gidansu kai tsaye, ta rasa gane me yasa mahaifinsa ke son tirsasa shi, lalle ta ji bashi da lafiya shi yasa yake aon hora ahi zama sarki aman a ganninta a barshi ya yi tukinsa mana?, Lalle yau akoy rigima a gidan nan, ita da kanta ta sani, aman kuma maganar sai ta mata nauyi sosai ta kasa tantance ita me zata ce a nan? Aman kula da ta yi cewar kamar Mah na mata hirar ne dan ta ji sanyi sai a sanyaye ta ce" Mah, in sha Allah ba zai tada hankalinsa ba" Mah da
Chapter 87 · 0% Book details