← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 114

Sashe 42

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
2
Gaba dayanta ta yi wajen da Hanja yake zaune domin nan table din ya wurgar da ita
Ido ta rintse tare da fasa ihu cike da tunanin ta kade har buzunta idan har ta idasa sauka a jikinsa, hakama shayin sai ta nemi azamar neman wurgar da shi gefe daya dan ba zata ao hasaso irin abinda zai iya samunta idan har ta dira kansa da wannan ruwan zafin ta tabata sai dai wata ba ita ba
Mahaifinsa ne ya fara mikewa yana furta" Subahannalah "
Mah da ta rintse ido gabanta na dak dak dak ta bude a hankali dan gannin mai afkuwa ta afku nan ta ga ikon Allah, HANJA ya tareta da abin dake hannunta na dan sekwani ita kuwa tar dubanta a kan fuskarsa tamkar kallon jaraba ta kasa cire duban nata a haka har ya cire butar a hankali kafin ya saketa daga kwonto masan da ta yi sakamakon shagalar da ta yi da kallon fuskarsa ta zube kasa gaba dayanta
Sai a lokacin ta ankare da irin kallon da take masa, lamari na zuciya mai saka bawa yin abu irin na rashin sannin ciwon kai ko mai kamun hauka sai ta kuma raka fafadan bayansa da kallo a lokacin da kama hannun Mahaifinsa ya mayar da shi zaune sannan ya dan rage tsayinsa ya mikawa mamansa butar shayin ya sakar masu murmushi ya juya ya fice a falon baki daya
Sai da ya bacewa ganninta kafin da sauri ta kai dubanta kan Mah da Pah
Bata san lokacin da ta mike da gudu gudu ta bar wajen ba cike da jin kunyar irin kallon nan, cen kasan zuciyarta kuwa cike da begen wannan bawan Allah, walahi har ajiyar zuciya kwace mata take idan har tana kallonsa, bata gajiya da kallonsa a kowani lokaci...................................................................
Barci Muneerath ta sha cike da nutsuwa, duda cenjin waje bata kasa rintsawa ba domin dama ba wai koshi ta yi da barcin nata ba dole aka tasheta
Kiran salar da ya sauka a dodon kunnenta ya sakata farkawa cike da matsanancin mamaki ta je wajen Windows tana lekawa sai dai bata ga inda masalacin yake ba hakan ya sa ta yi bayi da dan sauri da daura alwallah
Sai a lokacin ta ga an shanya kayanta a nan cikin bayin, ita dai ta dauro alwalarta ta fito da sauri ta dauki hijab din da ta yi sallar dazu ta gyara ta kabarta sallah
Tana gamawa ta ci gaba da zama tana adu'a idannuwanta lumshe hakan ya sa sam bata ji shigowa ba har sai da ta gama adu'o'inta ta shafa sannan ta buda idannuwanta dan cikinta fa kiran ciroma yake domin a dazun bata ci abinda aka kawo mata ba dan ita ba sanninsa ta yi ba tsakani da Allah, gashi yanzun bata da tumbi ba zata ringa fadawa komai ba ta yi tumbi haka kawai
Murmushin da Mah ke yi mata ya sakata dan yin sakalau a ranta ta ayana' ta ina ta shigo? Na shiga uku ita kuma wannan sai fara'a kamar wace bata da damuwa a dunia? Koda yake ina ita ina damuwa matar dake rayuwa a wannan gidan ai ko ita da ta shigo dazun ta sha barci sai da ta farka ne oga da mamansu da Dogari suka fado mata a rai'
A hankali ta ce" Ina yini "
Mah ta kuma sakar mata murmushi ta mike ta karaso inda Muneerath ke zaune sakalau da baki tana kallonta
Hannunta ta mika mata ta ce" Tashi mu tafi falo, ke kadai a daki ga abanku cen da kawarki a zaune "
Ido Munnerath ta kuma kiftawa a bayane ta ce" Wata sabuwa "
Mikewar dai ta yi dan bata iya saurin musu ba tana biye da ita tana shakar wani siritacen kamshi da take bazawa har suka ratsa wani corridor din kafin suka fito wata duniyar da ta saka Muneerath idasa sarewa rayuwa, kai jama'a ina ne nan? Wayo Allah ina ne nan? Sai ta ji gudun zuciyarta ya fara fin bugun normal, da sauri ta ringa saisaita numfashinta tana kale kale kafin ta sauke dubanta a kan datijon dake zaune d jalabiya fara tas shi din kansa fari kal da shi sannan fuskarsa dauke da yalwatacen murmushi da alkur'ani a hannunsa mai girma ya bude yana karantawa a bayane shigowarsu ya dasa aya ya bisu da murmushi kafin ya budi bakinsa a nutse ya ce" Marhababuki yar Mah "
Muneerath ja ta yi ta tsaya a hankali ta ce" Ina ne nan? Ku din su wanene ku? Dan Allah ki sanar min ko zan samu nutsuwa "
Iman dake kallonta cike da mamakin kokari irin na mamansu haka kawai daga gannin yarinya ta kwasota yanzun har falon Sarki yanzu ta mayar da ita kamar yar gida dan rashin tsoron mugwayen mutane, ita kawai haka take tunaninta yadda take haka kowama yake
Mah ta nuna mata wajen zama kusa da Iman dake zaune a saman lalausan kafet din kafin ta karasa kusa da mijinta ta zauna sosai ta ce" Wannan da kike ganni shine sarkin garin nan baki daya, ni kuma matarsa ce, wannan kuwa yar yar uwata ce, yaronmu kuwa shine wanda kika ce ya kawo ki watau HANJA"
Muneerath ta kwalalo ido tana kallonta kafin ta kuma bin su da kallo ta dire a kan Iman dake kallonta
Kaii ta gyada a bayane cike da mamaki ta ce" Sarki kuma? , Sarauniya ce ita? Aman sarki a gansa haka a dasha? Kai ko a garinmu sai a ce ana takama kamar wani sarkin ingila............"
Shiru ta yi ta kuma dubansu gaba dayansu kafin ta dafe gaban goshinta tana girgizawa wannan karron da yaren su watau turanci ta ce" Dama sarautar kasarku haka take? To ina ahalin gidan sarki? Ina su dogarai? Ina dawakai? "
Mah ta ce" Ahalin gidan nan sunna nan cike , basa zuwa nan ne dan basu da wannan damar, dawakai kuwa sunna bangarensu watau ranch, Dogari kuma ban san mene haka ba"
Sai a lokacin ta tuna dogari ta ce da hausa dan haka da sauri ta fada mata cewa masu gadin gidan sarki
Mah ta yi murmushi , sam bata ajiye haka a matsayin kauyanci ba domin idan ba zata manta ba a lokacin da suka je niger ta ga abubuwa da yawa da suka bata mamaki harma ta yi ta tambaye tambaye ana bata amsa a bayane, hakan ya sa ta ajiye Munnerath a matsayin wace ke tambaya dan ta karra sani, sannan ta ringa bata amsa a bayane ta yada zata fahimta, daga karshe dai ta mike da kanta ta kuma kashe Muneerath da wani mamakin a lokacin da ta umarce su kan su tafi kicin
Bata yi kasa da gwuiwa ba sai da ta samu kanta a wani dakin mai dauke da abubuwan aikin kicin wanda ake mata nufin cewa kicin ne duniya guda , sannan ta kuma zubawa wannan mata mai mukami da daraja a duniya baki daya tana kallo ta zagine tana yanka wata kalar albasa ba irin tamu ba domin wannan tasun wata jajawur ce da hannayen nan nata masu laushin na jariri bayan ta saka gan sannan wannan balarabiyar yar tata yar zumunta mai shegen kyau tana yanka mata tomatiri ita kuwa aka miko mata nata gan din da leda mai dauke da zabi fara kal ledar da kwano kan ta gyara sai ta ji wani takaici da zuciya irin ta mata sun motsa, haba ina ai nan da nan ta ji idanma aka bar mata zara iya dafe komai dan kuwa in dai wadinnan larabawan suka iya girki suka barta ta ji kunya ta dirko kasa ba nauyi ta ba batan africa kunya ( ehem )
Kamar da gaske ta zagine ta gyara zama a saman kujerar dake kusa da dogon table din ta saka wukar nan ta cira ledar
Zabuwar daya ta ciro tana binta da kallo, ita dai ba gashi a jikinta ko dis, sannan ba abin nan mai saka karnin miya a jiki, aman gaba daya sai ta mata girma fiye da tamu ta gida, ta zama kamar wata dan jariri ,
Kai ta dai samu ta karasata cikin kwanon ta kuma rike wukar ta zuba mata ido tana kallonta, walahi bata san ta inda zata fara sukar zabuwar nan ba, asalima bata san idan har ta yankata bata bata miyar ba......a hankali sai ta afka duniyar tunanin aminiyarta Amina, da kuma Kawarta saudat kafin murmushi ya bayana a kan lebenta tana ayana inama ace sunna tare, yau da an sha miya alkur'an
"Munnerath ?" Mah ta kuma fada tana kallonta
Firgigit ta yi ita dinma tana kallonta kafin ta mika mata wukar da kwanon da ledar domin hannu ta miko dan ta gama karantar bata iyan bane har yanzu,duda da wuya a koya mata dafa kaza aman ai mace iya girki ne kau? Ita kam zata yi iya kokarinta har Allah ya raba su dan gannin ta iya girki, hakan ya sa da zata juya ta koma gefe ta tsayar da ita ta shiga yanka zabuwar nan tana mata bayani cike da murmushi da fara'a har ta yanke su sannan ta hada su percil da su celerik da garlic aka zuba cikin wani inji inji ya zubo su a dake luf sannan aka cakuda da au mutarde da dan gishiri aka cakudewa zabin nan kafin suke zama su dukansu au dora yar hira, inda hirar gaba dayanta Mah ce ke janta su tsakaninki basu yi sabon da zasu yi hira ba sai dai su yi murmushi kawai
A kadan ta dauki kwana goma tare da wannan ahali bata leka ko nan da kofa ba tana gannin wata irin rayuwa ta mamaki
Soyaya bayananiya da ta badini ke wanzuwa a tsakanin ahalin nan , irin kulawar, irin yadda matar gidan ke tsaye kan kafafuwanta, da irin yadda wanda yake sarki ne ke tafiar da tasa mu'amalar da dukan wani wanda ya kwana ya tashi a cikin gidan bake wanda matarsa ta kira da yaronta shima zai kire shi ne da yaronta, a lokacin ta ringa tunanin wai dama haka sarakan suke ko menene? A lokacin ta ringa tambayar kanta shin sunna da wani boyayan hali ne da suke boyewa a gabanta ko menene domin wannan zaman lafia da kwonciyar hankali na bata mamaki fiye da tunanin mai karatu, shin su basu da damuwa ne? Menene sirrin haduwar kan ahalinsu? , Komai na ba Muneerath mamaki a wannan gida domin a nasu ba haka ta saba ganni ba, a anguwarsu kuwa yayan gidansu idan suka fita har daga kai da tinkaho suke ana kada masu taken yayan mai kudi dan kawai Oga ya kekyara gini ya zuba su ba tarbiya!, Tabas idan ta ga Mah na girkin abinda su yan matan zasu ci takan ji wani iri domin ba abinda suke ci Sarki ke ci ba, shi nasa girkin tana girka shi ne da sinadarai na magungunnansa sai an zo ci a yi ta daru ya ce sai dai ya ci nasu mai dandanon kayan dadi ita kuwa tamkar jaririn goye ta ringa lalaba shi kan ba zai ci nasun ba a saman makeken table din cin abincin gidan
A kwana goman nan kadai da ta yi da su ita da kanta ta dafa shayi wai ita Muneerath ya kuwa yi mata mahaukacin dadi a bakinta duda Mah ta ce kayan hadin sun yi yawa, watau kayan dafa shayin sun yi yawa ita dai dandano ta ji ram
A kwanakin bata hadu da kyama, ko hantara ba, bata hadu da lukucin dansu ba, aljana ce ta duniya ta samu wace bata hannata tuna gidansu a dukan motsinta ba, wannan yannayi na rayuwar nan ya bata sha'awar da idan ta tuna nata iyayen sai ta labe ta fashe da kuka, akan tambayi kanta anya a yanzu Mah zata iya wuni bata ganta ba bata nemeta ba? Aman gashi wa'inda suka fi kowa sannin ciwonta suka kawota duniya sun manta da labarinta, tana da buri a rayuwarta bayan na dogari da zama hostess wanda suka haifar mata, shine ta ganta a gaban Oga da Mamansu, tana so ta masu tambayoyin da take da bukatar amsoshi, gaba daya ta kasa ajiye tunaninta waje daya, shin matan oga da aure da aure su?, Shin da gaske su suke haifo y'ayan su?, Shin da gaske musulman suke har yanzu ?, A in malsarar take a zamantakewar ne ko a tubalin zamantakewar ne? Watau ginnin auren.................. Da yaya oga yake neman aure?, Shin ya yi koyi ne da fadar ma'aiki kafin ya sama masu iyaye ko ya gani ya kyasa yake yi? Da wannan zulumin ta kwonta da kuma zumudin wai gobe zata fara aiki
Hakan ya sa tun karfe biyar ta farka a barci ta yi wankanta na mamaki ta kuma gabatar da salarta sannan ta dauki man da take
11/14/21, 12:49 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 42 · 0% Book details