← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 114

Sashe 101

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ai yanzun yana da abubuwan tsayawa yi a gidan, bale kamshin nan da nana ke hadawa ai dole ya dan zauna a gefen yar oga da ta haukace ya daki babar rigarsa ta yadda idan ya fita zai karra ba makiya haushi Baki ya tabe yana fadin" da na zama dan yesu idan da adinin musulunci ya hanna ka yiwa dayar matarka magana dan ba aikinfa bane, kin ga ji ba matsiyaci bane walahi da kudina a aljihuna yo haukanki ki gama" Juyawa ya yi wajen Muneerath da ta kalli Saudat a sanyaye ta ce" Ki ce dai irin kwatancem zuwarma mutun da kika min shine yake yiwa wasu matan ko? Kai Allah wadaran naka ya lalace!" Saudat kasa kasa ta ce" Ki yiwa Allah kar ki bari mamanki ta ji wannan maganar walahi ta hada daga ni har ke ta jinyata mu, yau na ga shirme to wai ke ina ruwanki ne?" Oga ya karra kura mata ido ya ce" Ni kamar da kayan nan Yar Oga ta yi barci kuma sune a jikinta Nana?" Mama ta tabr baki tana zuba kafin kafin a turarenta ta ce" Kiris nake jira na maka mata muciyar nan Abanta, ka duba ka ga yarinyar nan ta ci abinci ta ki ci tana zaune da wani wando da riga ta saki jiki kamar wata katarpila sai langwabar da kai take irin ka mutun nan ta saka ni a gaba in na yi ciki ta bi ni Idan na dawo ta biyo ni , wata sangartar ai bata da anfani!" Oga ya wani saki murmushi na jin sabon sunna Aban Muneerath da akai masa ya juya zai nufi wajen Muneerath din matarsa ta fito daga cikin kicin tana ta ruwan hawayen hayakin itace ta rangada buda tana kama baki ta ce" Daga sweet heart an koma azamulumi mai yiwa y'ayan mutane asiri, yau kuma Aban Muneerath aka dira? Ka ga bariki kiri kiri watau mu ba haihuwar y'ayan muka yi ba ko uban Muneerath ne ita kadai?" Oga ya kuma jan birki ya juyo yana kallon yadda take ta shirnatu abinda dan ta karro wani warin hayaki sai huci take, kai shima akoy jaraba yanzun wannan matarsa ce? Du muninsa ya fita tsari tinda shi wanka yake, a kausashe ya ce" Kin san Allah in ban yi wasan kura da ke a gidan nan ce min shege, ku ji yar bakin ciki ai ci gaba aka samu, a da bata da hankali a gaban kowa ni din nam nine swuit heart dinta, daga baya aka yi walkiya ta ganni a fili na dawo makiyinta, yau kuma ta yafe min ta kireni da sunna mai daraja zaki ji haushi dan ke kina ce min Oga? To ni du ubanda ya kuma ce min Oga ba aban Muneerath ba sai na dauke fuskarsa da mari a gidan nan ka ga iskanci ko?" Dansa ne ya shigo da sauri yana zarro ido ya ce" Kai Oga anya anguwar nan lafia kuwa ? Dazun mun ga an zagayemu da sojoji bamu damu ba dan dai kowa ya san BAZOUM da bada tsaro a kasarsa, aka dan jima motoci suka karu abin tsoron harda sojoji da gendarmomi, to kuma yanzun laluwa ke kusanto mu Oga aka shigo layinmu abin tsoron na ga ana magana da yan anguwar ana ta mayar da su gida, kar dai a je wani ya aikata laifi a gidan nan ka fa san kaf anguwar nan gidanmu ne yan kwaya" Dau ya dauke fuskarsa da mari yana kallonsa ya ce" Dan ubanka yanzu na dora dokar kirana da Oga sunnana Aban Muneerath, sannan ban gane ba har yanzu kana siyar da kwayar ne? Na shiga uku kar dai a je kun janyo min jaraba ina zaune ban sani ba?" Da sauri ya juya ya fita hakan ya sa hankalin matayen da y'ayan gidan gaba daya tashi, mai iya dauko mayafi ko hijab ta warto da gudu, wada bata iyawa kuwa a haka dinta ta nufi kofa da sauri dan gannin abinda yake faruwa ciki kuwa harda Muneerath dake sanye da wandon barci wanda da kadan ya dara gwuiwarta sai rigarsa fara kal mai siraran hannaye Tsoro ne ya darsu a zuciyoyinsu Mita daya tak ce a tsakiyar anguwar wace ta fi kusanci da kofar au Muneerath, sai ko tarin iko watau sojoji da gendarmomi da dogarai manya manya amintatun sarki cikin sababin shiga irin tasu masu digiri da digirgir watau ko a cikin dogaran masu tsafta ne, wa'inda suke da damar zartar da hukunci idan ka yi batanci ga sarautar kasarmu, sun sha rawaninsu manya manya sababi dal, cikin shigarsu irin ta dogarai sun rike sandunna irin nasu kowane a shirye yake sun layu gefen hagu da dama gaba dayansu hakan ya sa suka yi caaa kuma suka cika ido sosai Oga ne ya fara yin saranda a tsayen da yake inda gaba daya iyalansa suke bayansa irin sun labe a bayan wada ya fi kunar nan, watau kauran nasu Zufar dake goshinsa ya samu da kyar ya share a sanyaye ya ce" Inaga motar cen bom ce a ciki za'a seto mu ne a kashe mu gaba daya, oh haihuwa, haihuwa? Na haifo wanda ya je ya zagi shugaban kasa ina ga an zo a kashe ubansa da danginsa, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une" Da sauri maman su Muneerath ta riko hannunsa tana kallonsa ta ce" Aban Muneerath dan Allah ka je mana, ka je ka ji menene ka ga fa inaga mune muka yi laifin dan na kula kaf mu ake kallo" Hannunsa ya janye yana kallonta ya ce" Kaya, kaya Nana, ba zaki gane ba, dole a kalle mi, anguwar nan waye marar ji irinmu? Dan Allah ki yafe min kar na mutu da fushinki kin ji matar aljanata?" Muneerath dake bin dogarai da kallo cike da mamakin Dogarai ne birjik haka a kofar gidansu ta samu da kyar ta fito daga cikin yan uwanta ta matso gaba sosai tana karra kallonsu, da sojawan da suke tsaitsaye fuska a hade kamar masu jira a yi motsin da bai masu ba su harbe mutun Daidai lokacin da Hanja dake tura mesage a wayar Pah rai bace kamar haka" Baka ce min da dogarai a tafiata ba, wadinnan sunne fa Muneerath ke haukan so, idan fa ta kore ni saboda su? Kuma baka ce min Attahir ne zai kawo ni gidan su Muneerath ba, me yasa kake min haka be?...." A hankali ya ji dukan da zuciyarsa ta masa ya yi tsanani da yawa hakan ya sa ya dakata yana dafe gaban zuciyarsa kafin ya dago da dubansa a hankali ya sauke a gaban motar Makoloton makogwaronsa ne ya motsa ya yi sama ya kuma yi kasa lokaci daya sakamakon ganninta da ya yi tsaye tana karewa mutane kallo bata motsa ba daga inda take A hankali ya juyo bangaren Attahir ya ga sam ba wajenta yake kallo ba, sannan ya sake maidawa wajenta Idannuwansa ya rintse sakamakon jin takaicin shigarta da kuma mamakin kansa, wace irin shiga ce budurwa bata yi su fita da ita a matsayin budurwarsa bai taba damuwa ba sai yanzu wannan shigar ta Muneerath da take rufafiya a kan shigar yan matan garinsu, sai ya ji wani irin abu na dukan kirjinsa mai zafi da sana sannin kwaso mutanen nann, kai saima ya ji dama shi daya ya zo aka harbe shin da mazan nan su kare mata kallo A hankali Attahir ya kara sada kansa ya ce" She love u, ta fada tarkon sonka a lokacin da ita kanta bata shirya ba, ya dace ka rike abinka domin ita din mai aiki da fadin rai ce, ta ga damar saboda fadin rai ta yarda da waninka" Kallonsa ya yi a karro na biyu kafin ya kuma kallonta Da sauri ya zarro ido ya samu kansa da bale murfin motar da saura yaana mika hannayensa baya ya dauko flowers din da ya zo da su sakamakon gannin ta nufi wajen dogaran nan har kamar zai bar kafar daya a cikin motar dan sauri Da gagawa Oga ya daga hannayensa sama yana fadin" Ta zo, mutuwar ta zo " "MUNARAH" Ya fada a hankali yana kallonta Da sauri ta ja daga niyarta na son karasawa wajen dogaran nan ta masu tambayar shin me suka yi ne? Juyowa ta yi a hankali ta sauke idannuwanta a kan fuskarsa Wani irin tsale zuciyarta ta yi ta doka , a hankali ta nemi zubewa kada sai dai hakan bai faru ba saboda tangal tangal ta yi kafin ta yi gagawar kauce hannunsa da ya miko da nufin son tarota kar ta zube Baban dogarin Fada ne ya daga murya yana fadin" Ku sada dubanku a gaban sarauniyar Ingila, Allah ya ja da zamaninki mai farin jini, tabas ke din halita ce ta Allah wace ya hada da madaukakiyar baiwa, ku sada kawunanku a duba ga cikin duban abin duban sarkin Ingila Umarni ne daga mai girma mai martaba sarkin garinmu" Ai kam daga sojojin dake kallon mamakin dama wannan yar bak'ar ce, har zuwa dogaran da sauri suka sada dubansu, ita kuma da mamaki take kallon wanda ya yi maganar tana bukatar karin bayani A sanyaye ya kuma furta "Munarah, plz ki kale ni" Tsoron kallonsa take ji, wayo tsoro take ji ta juyo gare shi, hakan ya sa ta ki juyowar sai kallon gefe da take cike da tsoron abinfa ke iya faruwa idan ta kale shin Rigar dake sama ta suit dinsa ya cire a hankali ya kara son matse mata waje Kanshinsa da ya karra kusantota ya sa da sauri ta dube shi a haukacr ta ce" Walahi kar ka taba ni, wayo na shiga uku zai taba ni Oga, mama ku taimaka min" Kasancewar da hausa take maganar sai ya dan ja yana kallonta domin ko yaya maganar nan dai ba mai dadi bace, hakan ya da yake kallonta har ta gama ihun A hankali ya mika mata rigar tasa yana kallonta Rigar ta harara sannan ta kale shi tana jan hanci ta ce" Meye hakan kuma?" HANJA ya lumshe idannuwansa a sanyaye ya ce" Plz, ki rufe jikinki, ki rufe bana so sunna kallo" Jikin nata ta kalla sannan ta kale shi tana karra turo baki ta ki
Chapter 101 · 0% Book details