Sashe 100
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 6 A hankali ya dago dubansa da idannuwansa da suka fara dauko maganar Pah din har zuwa inda ya furta sunnan mutumen da yake jin haushinsa har ransa ya sauke a kan Pah Muryarsa a nutse ya ce" Pah dakata, ban gane komai ba plz, wacece ta tafi dan an yi me? " Pah ya hadiye yawu yana karra nuni da sam shi bai san me ya sa ba hasalima ya nuna cewar shi taimako ya yi ta hanyar fadin" Da kyar aka iya rike Muneerath tana ihun kuka, inaga ta ji maganar cewa kana mu'amalantar wasu mata tamkar na aurenka bayan ba na aurenka bane, shine take fadin zuciyarta ciwo take yo mata ba zata iya zama ta kwana ba, na kwatanta rarashinta gannin dare ne a jiyan sai abin ya gagara a dole na saka aka kaisu Niger din domin idan ka ga kukan da take sai ka tsorata kar a je ta suma ko ta kamu da wani ciwon" Tsayuwar da ya yi a gaban Darius sunna tataunawa ya ji gaba faya kafafuwansa zasu maka shi da kasa ta hanyar daukansa suka nemi zubar fa shi ba tare da ya shirya ba Kansa sai da ya amsa na dan lokaci ya sake kurawa fuskar Pah ido yana kallonsa Darius hankali tashe da ya riko hannunsa daya da dukan hannayensa da karfinsa dan taimaka masa yana fadin" Kula Sir kar ka fadi mana" Da karfi ya janye hannunsa da ya fara taurara dan bacin rai yana kallon Pah , muryarsa a kausashe ya ce" Kana nufin Bata cikin gidan nan a yanzu haka?, Ta tafi kasarsu dan ta ji wannan yar maganar? Menene damuwarta da wannan maganar koda ta jitan? Inace wa ubangijina kadai nake da damar bama dalilin aikata hakan ba wani halita ba?" Pah ya tabe baki yana daga kafadunsa ya zauna tare da sauke ajiyar zuciyar gannin bai zube din ba ya ce" Ka san dama wani lokacin ina fada maka cewa wasu matan da suka san ciwon kansu basa koda magana da masu irin halayan nan, inaga tana cikin matan ne" Gabansa sai da ya doka da karfi hakan ya sa a birkice ya ce" TaTaTana cikin matan da basa kula namijin da ya kwonta da wata macen da ba ita ba?" Pah da sauri yana kallonsu gannin su duka abin mamaki yake basu ya ce" Ba haka nake nufi ba, ina nufin musulma ce ita, sannan al'adunsu na tafia da adininsu ne, a kasarsu aikata hakan dati ne, mai aikata hakan kuma dan iska ne, basa ko garajen rike hannun junna tsakanin maza da matayensu, basa rungume junna da garaje, namijin da ya mayar da kansa mai biyan bukatarsa da macen da ba tasa ba su da kansu auke kyamatarsa domin sunai masa kallon wanda baya jin tsoron ubangijinsa" Da mamaki Darius ya ce" Kai abin mamaki, saurayi dama ana kayade masa irin macen da zai yi mu'amala da ita? Gaskiya adininku akoy takura to ita ta yaya zata ce Prince na ingila zai zauna da mace daya? Lalle tana da rigima" Pah ya dube shi, a saukake ya ce" Adinina bashi da takura, adinina mai tsafta ne, sannan bai hanna mutun auren mace daidai har hudu ba idan har yana iya kamanta adalci a tsakaninsu, kai naka adinin ai kwaya daya ya halatawa mutun, a haka kuke zaune da sunnan matayenku daya aman yan matayenku dubu wannan shine adalcin?, Darius plz ka barni na gana da yarona" Dan risinawa ya yi kansa a kasa yana mai neman afuwa idan ya bata masa sannan ya fice da sauri cike da mamakin kai kawon da Hanja yake yi, koda yake ya san ko wacece ta yiwa kanta, ya tabata prince dinsu na iya dauko dubunta Idan yana so, aman har a yiwa prnc maganar mace wace kala ce bai fede ba? Ai sai dai kar a kuma kawai A nutse Pah ya furta" Hanja ka tsaya waje daya mana" Da karfi karfi ya ce" Na tsaya waje daya? Na tsaya waje daya? Ina son tsayawar na kasa ne, na kasa tsayawa Pah, Pah me yasa ni? Me na yi nake fuskantar wannan hukuncin? Dan na kwonta da mata? Na san adinina ya hanna, aman nawa al'adun basu wani hanna ba, Pah bani da aure, shikenan sai na tsaya na mutu da ciwo a cikina shine ta yi tafiyarta? Pah ni na san ba zata taba sona ba, idan kana son mutun komai ya aikata ba zaka guje shi ba, Munarah tana soyaya da Attahir ne ba ni ba, an fada mata shi Attahir din nata bai san harkar mata bane? Shine zata shiga jirgi da shi su koma kasarta ta bar Mah kwonce ni kuma ina yawo kamar dan iska?" Pah ya sadauta muryarsa ya ce" Calm down son, ba fa abin ihu bane, ka gane ita tana aiki da hannawar Adininta, bata wasa da wannan kuma tana tsanar mai wasa da wannan, dukan musulmin kirki ya dace ya kiyate dokokin adininsa, My son Allah ya halice mu ne dan mu bauta masa fa, shin Idan ka mutu a cikin aikata zina me zaka je ka cewa ubangijin da ya maka rai, ya baka daula, ya baka lafia da hankali da dama na rayuwa? Me zaka ce masa idan ka tsaya a gabansa ya nemi dalilinka na aikata hakan bayan kana da damar ajiye macen sunnarka?" A hankali ya yi baya ya zauna saman kujerar dake kusa da shi ya saka hannayensa cikin gashin kansa ya jimka da karfi.....magangannun da yake a cikon zuciyarsa sune 'Shikenan na rasa ta?, Shikenan na yiwa kaina ilah? Shikenan na kashe kaina da kaina? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Astagfrullah, Astagfrullah, ya Allah ka sanyaya min wannan zafi da nake ji a zuciyata' A hankali Pah ya zauna kusa da shi da damin flowers sunna kamshi ya kamo tafukan hannayensa ya bude ya saka masa gindinsu a nutse ya ce" Ka tashi ka je " Juyowa ya yi da dadadan kanshin flowers din masu sirki da yelow da fari kal a hannunsa yana kallon Pah tamkar bakon Halita a gare shi Pah ya ce" Idan ka yi wasa, ina tsoron fuskantarka na baka hakurin rashinta, ka tashi ka je za'a kaika har kofar gidansu , sai dai ka sani Muneerath ba irin yan matan dake lashe didigenka bane, ita da Allah ya halicema bai saka mata tsoronka a ranta ba bale ka yi anfani da wannan damar ka sakata dole, sannan ta san kana da kyau ta kuma yarda da hakan aman bai wani damunta, haka kuma irin sarautar garinmu daria take bata , cewa take mu da bama rawani?, HANJA ban san ta yaya zata dubeka ba, abinfa na sani Idan ka samu kanka a gabanta ka bar zuciyarka ta fadi abinda yake cikin zuciyar taka" Lebensa na kasa dake rawa rawa ya samu da kyar ya iya furta" Pah, Mahna?" Pah ya yi murmushi yana dan dukan gefen kafadarsa ya ce" Mah dinka, Mah dinka tana tare da Allah, nima zan koma kwana kusa da ita, my son jira ba zai kaika ga ci ba, ka yi jinkiri da yawa, kasancewarka a nan kuma ba shi zai tashi kafadun Mah dinka ba, you see ka rigaya ka balowa kanka ruwa tunda ka fadi a gaban kanina cewar zaka hau mulki, ina so ka hau shi da darajarka, daga nan garadai zasu maka rakiya, haka kuma a cen Sarkin garin ya fada min cewa ya tara dogarai da dawakan garinsu zasu yi maka jagora, sannan president dinsu ya bani maganar cewa sojawa tuni sunna shiri, Son ka dauko abinda ka je nema plz" Idannuwansa ya sada yana jin zuciyarsa na dokawa ya kasa kwakwaran motsi har sai da Pah ya yi yar dariya ya ce" Ban taba tunanin gannin tsoronka a bayane ba sai yau, ashe kaima akoy abinda kake tsoro? Mace?" Da sauri ya kalli Pah yana hade fuska ya ce" Tsoro kuma?" Pah ya gyada kai yana fadin" Eh mana, dubi fa , kalli hannunka a jimke aman sai rawar lebe kake HANJA Sarkin ingila kake fa" Ajiyar zuciya ya sauke yana cije lebensa ya mike tsaye yana rintse idannuwansa kafin ya juya da sauri sauri ya fice yana amsa adu'ar mahaifinsa a cikin zuciyarsa ya tarda taron sojawan da aka hado sho da su, sai ya ji har wani nauyi na son kama shi ya kara cin fuska ya wuce tsakiyarsu suka nufi wajen jirgin. _____________________________________ "Wai me take faruwa a garin nan ne Nana nake gannin shiru ya yi yawa kamar an kame mutane an labe?" Oga da yake shigowa yake fada Kishiyar Maman su Muneerath dake fama da kayan miya ta dago ta masa kallon uku biye da shi da maman Rumaisae dake ta faman hade haden turaran wutarta na siyarwa wanda ta matukar kwarewa a hada shi ta ce" Aman Oga gaskiya ka fara rashin jin tsoron Allah a al'amuranka, wai me yasa komai naka ita ce? Du motsinka ita ce? Ni fa abin nan ya fara isata walahi salon na yi magana a ce bani da hakuri, haka kuka tafi kuka yi kwana biyu a ban ina ba kuka barni da jarababun y'aya uwa haihuwar cikin wuta dafe ni ne kadai basu yi ba a gidan nan kuka dawo kana ta wani budewa kana karawa, kiri kiri sojoji a kofar gidan nan sun hanna yayata shigowa ban san dalili ba oga ko dai a wajen cacar taku ka ciyo mana jaraba bincikarmu ake a kwace gidan da muke karya da shi a kashe mu?" Oga ya wani irin jan birki yana kallonta har ta gama Tun dafa kafarta har kanta ya karewa kallo, ita dai irin matan nan ne masu tsayi Masha Allah ga kira mai kyau, sai dai a rayuwarta bata san meye gyara ba, kan nan nata kamar gwuiwa a gwaguye kuma bata daura masa dan kwali, kafar nan faso ta mata kanta sosai sai a hankali, a yannayinta na mace idan ta zo gitaka sai ta bajeka da warin jiki irin na gashin hamata da zaamin gyafto, haka take, haka rayuwarta take Kawai gani ya yi walahi ba zai iya bata amsa ba gaskiya, shi kam