Sashe 106
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 6 Ba EDDITING Kafin kiran sallar magariba DUBAN al'uma suka shaida daurin Auren MUNEERATH yar gidan Oga da HANJA MUHAMAD Sarkin kasar ingila, bisa sadaki mai albarka da kyautar uwa da uba mai gigita tunanin bawa Ana daurin aure a waje ne a cen cikin gida Gimbiya da jakadiya da yan rakiya sun gama shirin zuwa dauko amarya a kawota masarautar kafin a daga da ita, domin a yanzu HANJA ya fi karfin ya kuma zuwa da kansa ko dan nauyin da ya hau kansa da irin bakin dake tare da shi Ana gama daurin Aure Oga ya fashe da kuka yana talabe haba cike da tsoron Allahn da ya darsun masa ya shiga kallon Salihu ya ce" Salihu gaskiya ne dare daya Allah kan yi bature, yau gani ni Oga nine sirikin sarki? Yarinyar nan da ta tashi da maganar sarauta munai mata gani gani ashe itace sarautar gaba daya? Ka ga yau Salihu ni ogo nine ka kawowa kujera na zauna bayan a da gware muke da kai? Kai jama'a wayo duniya" Salihu ya ce" Oga ai daukakar kennan, Allah ya baka kai dai ka gode kawai, yaya maganar boyewar yanzun mu je da makadan su shaida mijinta ta runguma dazu?" Oga ya harare shi ya ce" Ai talaka yake gudun a fadi ba Muneerath ba, dan uban mai cewa ta rungumi kato ya gwada mana ya ga ikon Allah, makadan nan ce masu su shiga gaban motocin nan da aka ce a ciki za'a maida ni gida ni oga su kada min Kun gani Kun gani a kwalelen ku, oga ne wannan, kun gani kun gani a kwalelen ku, yar oga ce wannan!" Salihu kam jirgi daya ya kawo su dan haka ya juya hankali kwonce yana baza babar riga da rawaninsa ya tafi dan isar da sakon abokinsa washagale wale dinsa ______________________________________ Tartsatsin ihun da ta saka a lokacin da gidansu ya dauki shiru domin duk masu hayaniyar nan har matar oga fitar da su aka yi waje kwata kwata cewar kar su dami sarauniya Muneerath, daga mama sai matar yayanta da ta saka aka shigo mata da ita sun saka redio gaba sai zarar ido suke, ga saudat gefe rike da waya ta buda data ta saka duka amon wayar ta zauna a kusa da Muneerath din ta ajiye tana fasarawa su Mama da suka cika da matsanancin mamakin abubuwan dake faruwa , inda Muneerath ta yi likimo tana saurare domin ba fa haukacewa ta yi ba, ba kuma a shok take ba, tana dai tsoron buda ido a mata caaaaa ne ya sakat yin likimo din nan dan ta kula idan ta nuna a hayacinta take sai mama ta fara wanka mata marin yarda kato ya rungumota ya shigo da ita daki a gaban al'uma ba kunya ba tsoron Allah, ita kanta takan rasa me yake damunta da zarar ta yarda ya tabata an kare yanzu zata yi mukus da baki Sunna sauraron ne har aka kawo inda aka kwashi maganar shaidar daurin aurenta da shi, wannan ya sakata fadowa daga kan kujerar ta saka masu ihun da ya saka Saudat sakin wayar hannunta ta mike a zabure, hakama mama ta saki redion ta fadi kasa itama ta mike tana toshe kunnayenta sunna kallon ikon Allah inda Muneerath sai da ta karasa wajen kafet sannan ta fadi kasa ta shiga shure Shure da birgima a kasa tana ihun ta mutu ta lalace ta ce" bana so, walahi bana so, kasheni zai yi, zaki ne da shi, sai son rike min hannu da rungumeni, walahi ba zan iya zuwa wani garin zaman aure ba, aikina fa? Iyayena fa? Walahi Oga da baya sona? Du cikin y'ayan nan ya rasa wa zai yiwa auren dole sai ni? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une na shiga ukuna , tsoronsa nake, tsoronsu nake yo su dukansu, kuma Iman fa da take sonsa dan ubanta? Wayo na mutu ni Muneerath kennan na cuci Freind ko? Na ci amanarsa?" Mama ta nufi wajen waya tana fadin" Aa bari dai ki shiga uku yanzu ina zuwa" Da sauri matar yayanta ta ce" Kar mu yi haka da ke Nana, kina gani fa a halin da take ciki fa, dan Allah kar ki dauko abin dukan nan, yanzu fa Muneerath ta fi karfin ko ihu ne bare duka" Mama ta zarro idannuwanta tana fadin" A kan wani dalili ta girmi duka? Dukanta zan yi na zaune yar banza na huta da sangarta da lalaci da iya shege, to kar ki so shin mana kema ubanki ba aureni ya yi bana sonsa ba? Gwarama shi ai , Muneerath ba sarkin ingila ba ko ke suka nada sarkin kece a gabana ni kuma uwarki, walahi ki mike a burgimar nan ko na fasa maki jiki yanzun nan !" Kanta ta dan dago dan gannin an dai rike maman ko? Dan walahi bata son duka a rayuwarta sai in ta kama dole, aure ne dan tace bata so sai a daketa? In ba mamanta ba harda gori? Ina ita ina Hanja fisabililahi? Saudat ta karaso da sauri tana kamata tana fadin" Ba kuka bane mafita MUNEERATH dan Allah ki tashi haka mana, Hanja ne fa, ke da kanki kin san yana son ki, ki duba ki ga irin matan dake bibiyarsa du ya saka kafa ya shure ya tardo ki har anguwar nan ya nemi soyayarki? Muneerath Hanja ne fa da muke barin jiki idan yana waje, dan kawai kina jin haushin abinda ya aikata ne wannan kuma ba ke kika isa ki hukunta shi ba, ya nemi yafiyar ubangijinsa a wuce wajen aman ki daina maganar wai bakya sonsa Cikin muryar kuka ta ce" Ai damuwar kennan saudat, damuwar kennan, a kasarsu ne ake labewa da bindiga a harbe mutun, a kasarsu ne ake tareka a kashe banza, baka yi laifi bama an kasheka bale ka yi? Na tabata daya daga cikin tsinanun yan matan nasa zata sa bindiga ta kasheni kuma ta kashe banza dan ba yanda oga zai yi da ita!" Ka zo na zo aka yi da gimbiya da makarabanta da su oga dake baza babar riga yana turo hula gaba Fitowa ya yi ya yi tsaye a anguwa ya juya ya kuma juyawa ya bada damar a fadi abinda ya faru Ai kuwa aka fada da babar murya inda dunma wanda bai ji ba ya ji, kafin ya nufi wajen jakadiya dake daria tana jiran ya iso Yana zuwa ya shaida mata cewar yana zuwa bara ya fara shiga gidan Ai kam haka ya tardo ana balin nan, dan haka ya ja ya tsaya yana karewa fuskar matarsa da furucinta fahimta, har ya gane cewar koda tana fushi da maganar daurin auren to fa bata kai wajen da zata jigatashi ba, dan haka da kwarin gwuiwa ya je ya nemi da matar yayan maman su Muneerath kan ta kau daga rike mama da take ta barta ta karasa wajen Yar ogan dan Allah Ai kuwa rana kaucewa MUNEERATH ta dago kai, Gannin da gaske an saki mama ta mike tsaye zurbat daga borin da take tana zarro ido da gudu ta zagaya bayan oga ta labe tana leken maman dake huci ta ce" Kai kuma a kan me ka daurawa y'ata aure kai tsaye haka? A kan kudi ne ko Oga?" Oga ya girgiza kai da sauri ya ce" In a kan kudi ne na zama buta nana kowa ya shiga bayi da ji a tsarta min dati!, Gani na yi abin ya yi yawa, ana rungume a gabanmu tsakani da Allah , a gabanmu an yi a cen, an kuma maimaita a nan, a matsayina na uba mai kiyaye darajar y'ayansa na ga gwara na san da fatiha ake haka ko?" Da sauri Muneerath dake bayansa ta ce" Oga Allah daya ba da wata manufa ba yake yin haka fa, asalima su gaisuwarsu ce haka walahi Oga shine dama tun a cen kake ce min haka na zama dama yar iska ce ni baka sani ba? Walahi ni ba yar iska bace Allah".....ta karashe tana fashewa da kuka tana kara labewa a bayan Oga Oga ya ce" Yanzu dai ai du gardama ta kare da tonon asiri du ya kare, inma wanene dan iskan cikin ke da shi ba shikenan ba an yi an gama, kin ga motocin gidan sarki ne suka zo daukarta, dan Allah ku rufa min asiri ku shirya ku tafi, ni kam banki zan je na zuba dukiyar cen kar a biyo dare a kashe ni, domin idan muka zauna na fada maki abinda aka kawo dukiyar auren yar nan sai kin ji kamar ki haukace walahi" Da kyar dai ya iya samu ya lalabasu da shi da su Saudat har akaiwa bakin iso suka shigo Su da kansu sunna jiran shigowa su tardo wata aljana dan kyau suka yi kicibus da Muneerath, ba wai dan tana da muni bane, no, ya kasance ne idan aka ce ga matar sarki dole ka kala kuma ka yaba Wanka kawai mama ta tsareta ta yi kafin ta saka abayar da suka zo mata da ita su luluba mata alkyaba mai masifar kyau tana walwali sannan suka aniya yi mata wanka da ruwan turare suka tarkata suka tafi aman banda mamansu domin sam ta ki binsu ta ce gaskiya ita kunya take ji ba ga matar yayarta ba, ta tafi kawai Allah ya kiyaye hanya Sosai suka rungume junna da Muneerath tana ta faman fadin dan Allah ta nutsu ta bar magana sam sai a gaban idon sani, ta yi hakuri ta karbi tata salon rayuwar a haka zata ci riba A nan ne Gombiya ta fadi maganar da ta sanyayar da gwuiwar mama ta saka mata madaukakin tsoro domin ta fada mata cewar" Bafa salama bace Hajia, kin san ba'a daura auren sarki bai kwonta shi ba, wannan ne kadai ya sa zamu mikata turaka daga nanma domin ko shirin amarya bamu yi ba tukunnan , har sai ta fito a turaka zamu dawo da ita gabanki da masu gyaranta ki shirya abinki fa kanki ku yi kyakyawar salama sannan a rakata kasar mijinta domin ko shi a yanzu ba zai so zuwa da ita kai tsaye