← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 114

Sashe 88

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ta ci gaba da tafia ta fara zufa sosai na irin murdawar da cikinta ke yi mata a hankali ta ce" Dole zai yi fushi, dama yana cikin bacin rai da rudani na zuciya, Baby he is in love but ya kasa admettre harma ya kai ga abin sonsa" Haka kawai ta ji jikinta ya karra yin kalau tana kallon yadda mamanta da Saudat ke kallonta domin tun cenzawar yannayinta mamanta ta rage gaz sosai suke kallonta sai kuma irin maganar da ta yi cewar Pah ba lafia ya saka Saudat fahimta ta dan kwatantawa mama a sanyaye shine suke jira ta gama wayar A hankali Muneerath ta kuma cewa" Mah da me zan iya taimaka maki?, Idan ina yin koma menene dan na taimaka maki ki sanar da ni ba tare da jin wani abu ba, domin a rayuwata kin min rana, Mah kin ga kafin na hadu da ke ban san dadin uwa ba, ban san komai na mahaifiya ba, Mah a kanki na fara sannin kula, da nasiha irin na uwa, Mah a dawowata na tarar da mamana ta dawo hayacinta har yanzu nima wai nice na iya dafa shinkafa na iya abubuwa irin na mata? Mah kin ga.........." Sai kuma muryarta ta sarke ta dan fara shashekar kuka ta ce" A dawowana mamana ta ce min Haba Muneerath ki ringa adu'ar samun dace da miji na gari ba wai ki ringa adu'ar Allah karkato da hankalin dogari a kanki, Mah a da fa ita ce ta ce min dama dama dogari ko zai so ni?, Daga ranar nan na san cewa bawa baya yanke rai da rahamar ubangijinsa" Mah ta lumshe ido tana sakin murmushi da bayanan Muneerath, a hankali ta ce" Ina murna da murnarki my Daughter, ina matukar farin ciki da farin cikinki, plz ki daina kuka kin ji?" Muneerath ta gyada kai tana ta murmushi a hankali tana jin yadda Mah ke shasheka kamar ta yi gudu ta ce" Mah wai motsa jiki kike?" Mah ta ja numfashi ta sharce zufa da kyar ta idasa hawa gaba daya ta kara dakatawa tana lumshe ido kafin ta nufi dakin Pah a hankali muryarta ta yi kasa sosai ta ce" Baby, zaki min wata alfarma?, Plz zaki taimakeni ki min wata alfarma?" Muneerath ta amsata tana sauraron tana dan kwankwasa dakin Pah, sai kuma ta ji shiru da dan mosti kadan Dan jim kadan sai kuma wani bugawar da karfin gaske ya shiga kunnenta wanda ya sakata saurin cire wayar a kunnenta Mah da ta juyo a figice ta sauke dubanta a fuskar yaronta ta gansa da wani irin bacin ran da bata taba ganninsa da shi ba kafin ta ankara ya daga hannunsa rai bace ya kuma mugun doka kofar mahaifinsa wanda ya zo zai bude jin bugawar da karfi ya saka shi budewa a hanzarce dan sannin cewa lafia ba wanda zai matsa mugun bugu irin haka Da sauri ya bude yana bayana gaba dayansa yana sharce ruwan alwallar da ya dauro ya sauke dubansa a kan yaronsa wanda sai da ya ji gabansa ya fadi da yannayin yaron nasa da kuma matarsa dake gefe wada ya kasa fahimtar halin da ita take ciki Rai Bace HANJA ya dube shi ido cikin ido a kausashe ya ce" A kan wani dalili zaka dauki irin matakin nan da rayuwata?" DOMIN SAMUN NAKI LABARINA MAI SUNNA WATA KOKOWAR KI TUMTUBENI TA NUMBER WAYATA KAMAR HAKA +22793811618. A KAN FARASHI MAI SAUKI IN SHA ALLAH 200 DARI BIYU TA TRANSFER KO KATIN MTN.........na gode masoyana sai kun zo 11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 88 · 0% Book details