Sashe 40
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 2 Tsabar firgicewar da ta yi, da kuma lafiyayiyar hanya irin ta kasar ingila, da babar mota watau mota mai sunnan mota ba moto ba ya saka sam bata san cewa sun motsa daga inda suke ba, sannan bata san cewa sun dauki lokaci sunna tafia ba, sai jin budewar motar da ta yi lokaci daya cikinta ya juya wani lafiyayen gudawa ya faa hada kansa wanda ta gama tabatawa cewar yana kusa , idan aka yi wasa a nan take zai bale mata ta kai dubanta a kan fuskar Mah da fuskarta ta kasa boye farin cikin da take ciki sai washe fararan hakoranta take kafin ta karaso wajen da direba ya budewa Muneerath motar kan ta fito ta miko mata hannunta tana murmushi ta ce" Marhababuki daughter" Ido Muneerath ta zuba mata cike da mamakin ina ne nan kuma yaya aka yi suka zo nan da kuma matar nan , Sai kuma ta karra ido jin tana ce mata daughter, nan take ta shiga tunanin to ko da yarensu wani abun yake nufi ne? Ita fa sam bata gannin tsufan matar walahi hasalima matar ba wani jiki ne da ita ba sannan koda yaushe cikin shiga ta kamala take wace ko dis din gashinta ba'a gani bale a ga wani yannayi na tsufan, fuskarta kuwa bata kai wajen fara yaba ba ko shegen gyara ne d hutu? Aman tsufan bai gama nuna kansa sosai ba bale ga Muneerath da ba wani fahimta ne da ita ba, ita sam bata ga datijuwa a gabanta ba wollah, to ina wannan ina amsa kiran mama? Sam bata kawowa ranta ba shi yasa take kallon hannunta da kuma ita da bayanta dan so take ta hango wannan kumurcin da zakin da ya kawo dan ya kasheta Cikinta ne ya fara kartawa alamun zai kuma juya mata hakan ya sa muryarta cen ciki ta ce" Ina zakin? " Mah ta kaleta da kyau dan son fahimtar wani zaki take tambaya ? , Da sauri ta juya dan gannin Hanja ya bata karrin bayani, sai dai ba shi ba alamunsa da alamu ko ya shige ciki ko kuwa ga yi tafiyarsa abinsa hakan ya sa ta juyo ta dan watsa hannayenta ta ce" Wani zaki? " Muneerath ta kikifta ido a sanyaye ta ce" Shi zakin da ya kawo ya cinye ni, sunna ina?" Sai a lokacin Mah ta fara dago zancen, sai a yanzu ta karra lura da irin tsabar firgicin dake tare da Muneerath, lebenta na kasa ta dan cije tana girgiza kanta a hankali ta karra mikaea muneerath hannunta ta ce" Babu zakin da zai cinye ki, kin baro zakin a cen gidansa, taho mu shiga ciki " Muneerath ta ringa sauke ajiyar zuciya zuciyarta cike da mamakin irin ci gaban da duniya ta yi, dan har ga Allah a tunaninta wannan mota mai kama da dan daki bacewa ta yi ta bayana da ita a nan A hankali ta dora hannunta cikin na Mah kafin ta zirro kafarta waje ta karasa fitowa gaba dayanta tana dan zarar ido Da sauri ta rike hannun Mah tana karra bin irin tarin matan da suke tsaitsaye da kallo , muryarta cen kasa ta ce" Ina ne bayi? Ina son zagayawa" Mah ta dubeta, kasamcewar mace ce kuma yarinyar da ta tabata ta haifi kamarta sai ta bi jikinta da kallo gannin rigarta fa a jike daga kasa Cire dubanta ta yi ta jata suka shiga tankamemen falon da sanyinsa kadai ya saka Muneerath jin dan lisilama danma shi oga zawayi ba ruwansa da sanyi ko zafi , idan fa ya karta a kaishi a zubar ko ya fito da kansa dan kuwa shi bai san wata kalma ba wai hakuri ko kunya ba hakan ya sa ta ringa bin Mah da sauri sauri sosai har suka shiga accenceur ya yi sama da su suka kuma mika dan dogon coridor kafin su shiga wani dakin da bata iya gane komai ba zuwa lokacin dan ogan ya fara dan tsartuwa a guje ta nufi bayin da aka nuna mata kan shine wanda zata shiga ta aiwatar da uzurin da ya kamata a yanzu yanzu Wollah, da ba dan ta jima a garin ba, ta kuma iya gane ramin masai a zamanta da su ba, da babu abinda zai sakata hawa wannan waje mai walwali ta zubar da dati Kai jama'a, mutane duniya na inda take, yo wannan abin idan musulmi nada hankali an ce aljannah ta fi karfin tunanin bawa ai zai dage dukkan karfinsa ya ringa ibada dan ya ga wannan iko na Allah, haka kuma wanda ke cikin irin wannan idan ya yi wasa ko sallah ba zai yi ba, zai shagala da shagalalan wajen nan ne har sai ya ji guduma a saman kansa ya jishi a matsatsen rami kafin ya gane cewa da gaske fa mutuwa zai yi Ido ta lumshe tana amayar da ogan mai kukan tsiya wanda yake tafe da damuwarta, A hankali ta ringa jin sansanyar iska na kadata a lokacin da ta samu nutsuwa hakan ya sa ta ringa buda idannuwanta dan gannin ko a nanma akoy AC ne? Ai kau akoy din sai dai ba a kunne ba, kawai nutsuwa ce irin ta idan ka gama zubar da wahalar nan hakan ya sakata sakin sansanyan murmushi tana yiwa Allah godiya da bata yi a jikinta ba A hankali ta gama , nan fa tsaftar ta tashi domin bayan ta wanke da sabulu ta kara wankewa da ruwan dumi sai ta kasa mayar da komai nata daga pant din har rigar, gaba daya sai kyankyamin kayan ya sakata jin tamkar zata kelaya amai Da sauri sauri ta tara ruwa ta shiga wanke su ba tare da ta tuna komai ba, har sai da ta masu ruwa hudu sannan ta matse su ta karasa ta cire tawul din da ta daura a kugunta ta wanke wajen tas sannan ta shige ciki ta tara ruwa masu dumi sosai ta zauna ta dauki sabulun nan ta shiga darzar fatarta da shi kadai mr spcly wajen da dan fitsarin nan ya bata mata na jikinta du ta wanke har sai da ta ji tana kanshi sanann zuciyarta ta aminta da tsaftar jikinta kafin ta fito tana mamakin kanta irin yadda ta yi wankan nan a wajen nan ba tare da ta wanke ba bayan du tsaftar waje sai ta tisa masa kafin take anfani da wajen Kafadunta ta daga irin na oho din nan kafin ta dauki wani tawul din kuma ta ja ta tsaya cike da tunanin yaya zata yi ta fita Mah dake zaune cikin zulumi take Zulumin da take cikinsa na gannin kanta ba dan kwali da kuma fitsarin dake jikinta Lale ta san na lalura ne, ba da gangan zata yi fitsari a jikinta ba, abinda ya fi damunta daya ne irin yadfa zata fito mata, shin da rigar zata fito a jikinta ko babu? Ita mah a duniyarta abu daya ke wahalar da ita shine tsafta, mace ce mai kuguwar tsafta, sannan mace ce mai riko da adinninta, du irin yadda dunia ta rikice ita ta ki ta dauki maganar cewa wai yanzun yan mata basa son saka dan kwali ba, sosai ta zauna cikin tunani bayan ta dauko mata wasu suturun da dan kwali tana jiran fitowarta, Babar damuwarta shine bata san ta yadda zata zauna da kazamar yarinya ba Na biyu kuma shine sam bata iya zama da mutumen da baya son rufe suturarsa ba, duda yaronta ba mazaunin gidan bane idan ya ga dama yake zuwa in ya ki kuma baya ko leko su sai dai ita ta je, aman sam bata so ta ga ana yawo ba dan kwali dan ko christocin gid an da yan dan kwalayensu a kawunnansu idan sun hau aiki, idan sunna so in sun tafi gidajenau su cire abinsu Da sando ta fito da sauri ta ja shinfidar gadon ta aniya cikwuikuyewa a jikinta cike da jin kunyar matar nan wai dama tana nan? Allah sai yanzu ihun kukan abinda ta zubar a masai din cen ya ringa dawo mata hakan ya hadasa mata matsananciyar kunya har ya kasa dago kanta da kyar daga tsayen da ta cuimuimuye ta samu ta dan fitar da fuskarta ta kai dubanta kan Mah da fatan ta bar dakin Ido hudu suka yi, hakan ya sa Muneerath rintse nata idannuwan a sanyaye da yaren turanci ta ce" Ki yi hakuri, ba da gangan ya kubce min ba, nama wanke kayan na matse su, kuma na yarda mayafina a cen makarantar da mijinki ya dauko ni, dan Allah ku yi hakuri idan wani laifin na maku" Mah ta saki murmushi tana jin gamsuwa da nutsuwa da bayanan Muneerath kafin ta kuma yin murmushi ta mike ta nufota rike da kayan nan ta tsaya a gabanta kafin ta ajiye a saman bed din dan shinfidar ta zannin gado hudu ce na saman kadai ta yayuma Dubanta ta yi ta kuma sakar mata murmushi ta ce" Ki cenza kayan ki, ki yi sallah, za'a kawo maki abinci ki ci, sai ki kwonta ki huta kin ji? " Muneerath na kallonta da mamaki bata iya cewa komai ba Har ta juya ta dawo ta kama hannunta ta cikin zanin gadon ta ce" Bama kisa, sannan d'ana ne ba mijina ba " Tana gama fada ta sakar mata hannu ta juya ta tafi tana murmushi Sakalau munnerath ta yi da bakicike da mamakin dake nemn kasheta kafin ta shiga tafa hannu a bayane ta ce" To ko dai da aka ce a inji ake kyankyashe su hakan ne? Ko kuma irin y'ayan nan ne na kwalba shi din shi yasa ya yi saurin girma?".......karshe dai a hakan ta ajiye ta gyada kanta kafin ta girgiza ta shiga saka suturar ta abaya fara ta kuma furta" Gaske yannayinsa sam ba na mutun bane, ashe shi din mutumen nasara ne gaske hannaye kamar an busa balan balan an saka masa ga karfi irin na aljannu.....Allah dai zai saka min yanzu haka na girme shi a haife ya shake ni munahiki kawai!"............................................... ________________________________ "Dama har haka suke da iko? Aman ko shi ya kawota a kasar nan na