Sashe 46
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 3 Ya ce" ta tashi ta tafi" Da sauri likitar ta ce" ur excellency ka yi hakuri kar k koreta da alama bata san kan aikin bane gata bakuwa sannan ba haifafiyar nan ba" HANJA da kukan ke neman hadasa masa juwa ya ce" Cewa na yi zan koreta? Ta je ta hadu da sauran a shirya su mu tafi" Wannan karron ba likitar ba, Sir kansa a mamakance ya kallo shi sai dai irin yadda ya hade rai ya juya yana mai dafe gaban goshinsa ya saka cikin gagawa likitar ta mikar da ita tana kukanta tana bata hakuri suka yi gaba da Sir suka nufi wajen da sauran suke A nutse likitar ta tsaya kusa da shi kadan ta ce" Sir " Kansa dake sade ya dago ya juyo yana fuskantarta bai amsata ba Abin aune aunen ta nuna masa a ladabce ta ce" zuwanka ne " Hanja da kansa ya dau ciwo na ihun kukan ya cije hakoransa ya zagaya ya je saman doguwar kujerar ya zauna yana mai tube rigar jikinsa ya ajiye hannayensa ya lumshe idannuwansa ana sauraronta ta shiga auna shi cikin nutsuwa da kayan aikinta tana rubutawa ta dago tana kallon wajen fuskarsa ta ce" Lafiar jikinka ingantaciya ce, abinda na ga yana kokarin damunka biyu ne, kanka da ya dauki ciwo sai kuma yannayin bukatuwarka wanda su dukansu yanzun za'a magance su" Idannuwansa dai a lumshe suke har ta dawo da magani cikin kofi ta zauna saman kujerar ta bashi ya amsa ya sha ya kuma lumshe idannuwansa na kusan minti goma bata yi magana ba sai dai tana rike da tap a hannunta mai kirar aple tana jiran ya motsa A hankali ta ce" Sir ciwon kan ya sauka? " HANJA da ransa ke bace yana ta tunanin ta inda zai samu mafitar da zai yakice yarinyar nan daga cikin ahalinsa ya dan motsa mata kansa bai amsata ba Ajiyar zuciya ta sauke cike da tunanin to wai ko dai da gaske yar maman nasa ce? To a afrika ta samu cikinta ko menene? Ita ta kasa gane yaya aka yi haka, sai dai ta yarda koma me dinsa ce tana da kusanci da shi mai karfi wanda ya zarce na maganar soyaya, hakan ya sa bata yi gigin yi masa wata tambaya a kan Muneerath ba Screen din tap din ta juyo masa bayan ta tsaya, Hotunna ne na wasu tsala tsalan yan mata na grup VIP na kasar baki daya wanda kampaninsu ya samu shiga dan samawa zaratan mazan abin bukatarsu a ringa cirewa a cikinsalarry dinsu wanda a haka kampanin ke kara wawusarsu.....hakan kuma nrmal ne nema ne A hankali take dan matsar da hoton ta sako wani, daga ringeshen da yake yanna kallo tarrr a idannuwansa ana ta wuce su yan mata ne masu fata mai sheki da tsayayu mama da dan kugu sunna cikin shiga ta tairaici sun yi kwonci irin na yan duniya ko a tsaye an wani wara kafa, ko a zaune an saka pom a baki an datsa masa hakori.....yannayiyika dai na talar abin cikin pant har sai da ya gaji da bi da kallo kafin ya maida kansa ya lumshe idannuwansa A ladabcenta ta ce" yannayinka na nuni da nan da dan lokaci mararka zata kule, lokacin bai fi yan mintunna ba sir ka fini sannin yaya ciwon mararka yake gashi zaka yi tukin awa hudu, idan kuwa ka fi so na je da gagawa na kawo maka wace ta yi sai na je yanzu yanzu na kawo " A gaskiya shi da kansa ya san a bukacen yake, sai dai wani lamarin wannan bacin rai da aka hadasa masa na yanzu ya kular da shi sosai, walahi da ace wannan yarinyar bata da daurin gindin gidansu da sai ya wanka mata mari kafin ya koreta, wannan yarinyar nan da wata uku ta saka shi hawan jinni fiye da nrml bp dinsa shi ya sani, dan dai mai hakuri ne shi ya sa yake sauka da wuri, haka kawai katuwar YA ki saka mu a gaba ki rushe mana da kuka? A kanta aka fara tambayoyin nan ko a tunaninta ita ta daban ce da za'a tsara nata? Ko tunani take sai an bi ta nan za'a iya korarta?, Dan bakin raini ta furta masu bata taba yin saurayi ba dan kawai ta basu aikin bincike na banza da wofi! Kai ba za'a yi binciken a kan nata ba dan shi yana ji a jikinsa verry soon zai tatara ya nata ya nata ya kara mata gudu, ina dalili tun bai fara haihuwar ba wata gandareriyar bak'ar y'a zata zo ta dame shi! Mikewa ya yi zaune ya shiga maida kayansa bai bata amsa ba har sai da ya gama sannan ya ce" No barshi, bana cikin mood din hakan zan sha magani ai tafiar ta yau ce kadai in sha Allah " Yana maganar ne yana tafia ya fice a office din gaba daya Ajiyar zuciya ta sauke, bata dan me zai saka ya ce bashi da ra'ayin hakan ba bayan ga yadda jikinsa ya nuna, kai su fa basa son abinda zai taba shi dan shi din adali ne a gare su, mutun ne mai kyautata masu hakan ya sa suke maraba da dukan ranar da zai shigo wajen su, irin yadda ya tsaya tsayin daka kan ma'aikatansu kuwa ya sa suke aiki da kuzarinsu domin da ace Sir HANJA ya kasance mai yin yan mata a wajen aikin nan da sun shiga uku, sai Allah ya taimake su ba ruwansa da y'a a wajen aikinsa ko yar waye, ko wata irin halita gareta, kai ko a wajen sai dai ya sayi wace ta baza hakan ya sa a irin halayan mutan garin ake respcting dinsa sosai Sir ne ya fito yana tambayar idan result dinsu sun fito Nan ta mike suka tafi dakin amsar result din suka amso suka dawo suka zauna sunna wawarewa Likitar ce ta kale shi ta ce" Ita ba'ai mata na gwajin cikin ba kar kuma ya kama ni da laifin hakan" Murmushi ya yi ya ce" a barta haka, za'ai mata zuwa gaba idan ta gama fahimtar a kan aikin ne ake mata tambayoyin ba dan ta yi wani laifi ba ko dan ana zarginta ba, kin san bata taba fuskantar haka ba shi yada ta ji tsoro" Kai ta gyada ta harhada mada komai ya juya ya tafi dan ya kai a dora a kan takardar kowace ya amso baje dinsu kafin su fito daga wajen likitar Tunda ta shigo wajen ta daina kukan tun karfi aman kuma hawayenta na dan zuba haka kuma tana ta sauke ajiyar zuciya Yan matan dake dan kara shishiryawa ne suka nufota, dama tunda ta fashe da kuka suke jiran gannin shigowa zata yi ko ita takardunta sun samu cika Wace ta fi rama a cikinsu ce tana kallonta ta ce" Korarki ya yi? " Muneerath dake kallonsu daya bayan daya ta girgiza mata kai Da mamaki dayar ta ce" ko dai kallonsa kike ta yi har ya kama ki da hakan? " Itama da mamakin ta kuma girgiza masu kai Sai suka samu kansu da kallon junnansu kafin daya ta ce" to kukan me kike? " Muneerath ta ja hanci ta ce" Gani na yi ana ta min tambayoyi kamar wata karuwa, dan Allah ina gamina da haihuwa ko ciki a yanzun ni da ko rana ba'a saka min ba kai ko saurayin bani fa shi ba'ai min auren ba za'ana cewa wai wani na tara da namiji to na cewa namiji me ya ce min me? Dama sai da Mah ta ce akoy yan iska a wajen nan na bi a hankali" A gaskiya, kwata kwata basu gane wai tana kuka dan an tambayeta idan ta tara da namiji ne bayan bata da aure, kai su sai suke son gane kawai haihuwar ce bata so dan an hadata da haihuwa take kuka, hakan ya sa suka nemi kwatanta mata cewar ba wani abu bane wannan ai Wace du ta girme su ce ta ce" Mun zata korarki ya yi kike wannan kukan, ki tashi ki share hawayenki mu idada kimtsawa mu tafi, kin san sai mun yi binciken kayan mutane bayan sun zauna dan an fara shiga da miyagun kwayoyi malesia yanzun ana cikin yin taka tsantsan ne Ita dai nan ta ringa binsu har ya dawo ya masu ja gaba baki dayansu suka tafi dakin da zasu layu ya kuma masu wani gargadin Kamar yadda Sir ya saba haka ya fada masu dukan abubuwan da ya dace su kula, su kiyaye, su yi taka tsantsan a tafia da PRINCE idan har sunna son aikinsu Sai da ya rage yan mintunna kafin ya shigo, ya cenza kayan jikinsa yanzun suturarsu ce ra matuka jirgi a jikinsa HANJA yana da sirrin kyau da kyan kallo, sai dai idan ka yarda ka kure mada kallon kana iya janyowa kanka abinda ba shikenan ba, hakan ya sa sauran yan matan da suka kwana da sannin tafiar da waye suka dukar da dubansu , banda Muneerath dake kallonsa tana hankalce da takun tafiyarsa dan bata so kwata kwata ya nufo wajenta dan a shirye take ta dankara da gudu idan ya nufota wollah, a cen kasan zuciyarta kuwa tana tana mamakin wai yanzu ace wannan mai jiran gado ne ba rawani, hm wani abin sai sarakan ingila Kamar yadda ya saba haka ya tsaya a gabansu ya gindaya masu cewar Aiki suka zo yi su nutsu su yi aikinsu idan ya kama su da wani laifin ba zai iya kyale su ba, sannan ya fara yin gaba, sir ya bi bayansa sannan suma suka bi bayansu A yaune zata yi shiga ta biyu,a yau ne take cikin hankalinta hakan ya sa tunda suka tunkaro shi ta daga kanta tana kare masa kallo Girmansa, girman tayoyinsa, girman fukafukansa biyu, gaban goshinsa da ya yi tsini, tsakiyarsa da kuma bayansa, matatakalar dake bude da sojoji da ma'aikatan dake kusa da shi gaba daya sai ta samu kanta da jinta tamkar a wata duniya daban, Wata irin connexion take ji da zuciyarta da tafkeken jirgin A hankali wani irin shauki da