Sashe 64
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
yanzunma a tsanake ya kuma cewa" Yaya aka yi kika samu kanki a ciki?" Muneerath ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Abinda na fara rikewa shine Allah, na san cewa shi kadai ya isa ya tsaya min, na san da cewa ikonsa na kan kowa, kuma yana iya yi min a lokacin da ban aune ba, shi yada kawai na dukufa ba dare ba rana ina fada masa....Ya Allah ka bani DOGARI sannan ka bani damar zama Hostess" Dan dakatawa ta yi tana kallonsa kafin ta kara sada kanta tana wasa da hannunta ta dora da fada masa irin yadda aka yi ta koyi ruwa, irin yadda ta fara koyan girki aman kulun abin na gagararta, kamar an kunna redio tas ta kwashe masa yadda ta tsinci kanta a wajen horon Hostess Ta idasa da dafe habarta tana yarfe hannunta ta ce" Wannan labari nawa akoy abin mamaki ko baka gane ba kai?" HANJA bai taba gannin mutumen da yake hira a sake a gabansa irin yarinyar nan ba , ciki kuwa harda Mah dinsa, domin Mah tana magana da shi ne da sigar rarashi da yannayi na son ta lalaba shi, aman yarinyar nan hira ne take da shi kamar na sako da sako, kanta tsaye hankalinta kwonce ta gama bashi labari da sunnayen mutane kala daban daban da a ciki bai san meye Oga, meye hajia baba watau hostess dinsu baba, sunnaye dai kala daban daban da ta ambata da hausa ba da turanci ba ta krashe da koda labarinta irin abin dai a ranta yake Sannan bai taba gannin yarinyar dake magana zuuuuuuuuuuuuuuu kamar wata redio abinta daki daki har sai a ta dasa aya ba sai wannan yarinyar Kansa ya cire a kanta a hankali yana jin kamar zai saki murmushi a bayane sai dai ya hanna kansa hakan Muneerath ta kuma rafka tagumi ta ce" Yanzu ko yaya makomata take? A islamiya ake cewa karmace ta yarda da namiji ya zo mata idan ba mijinta ba, idan ta yarda da haka har namiji ya tabata to fa ta aikata zina....... hakama Mah ke cewa namiji na taba mu muna iya daukan ciki,shikenan mutuncinmu ya zube idan har muka yi wasa da suturarmu.......Dan girman Allah yanzun hannuna ka riko ka kuma riken jikina fa? Da wani irin mamaki yake kallonta, kai shi kwata kwatama sai ya ji ya rasa me zai yi tunani da yarinyar nan, gashi dai yanzu sunna maganar fahimta kuma tana son fara sako masa rainin wayon, ko me yasa take irin haka? Ko a tunaninta shi HANJA zai iya wata mu'amala da ita ne? Bata san cewa a cikin tsarinsa shi yana da haram bane? Bata san cewa baya zuwarma macen da bata fito ta nuna sana'arta bane? Bayan wannan bata san cewa baya haikewa yan shila bane? Dan tana ganninta bukekiya ai girman jiki ne ko a tunaninta shi zai iya wani abu da abinda bai nuna ba? Kansa ta cire yana dan girgizawa kafin ya mike tsaye ya ce" Kin ga magana nake so na maki ina so ki fahimce ni kin gane?" Muneerath ta yi gagawar gyada kanta tana binsa da kallo, willah kamar wani balarabe Allah, kawai shi kuma haka farinsa yake fas? Kamar mai shafe shafe ita mamakin laushin fatarsa take, yanzun dai dan tana tsoron a wajen nan ya hada mata jinni da kwakwaluwa ya sa bata kireshi da sunnan da ya dace da shi ba, kai tsaye ya ringa tabata dan yana dan......... "kin ga, a gabanki ta ce wai ga amana nan na rike mata yarta, ban san yaushe ta min kishiya take kiranki kai tsaye yarta ba, abinda na sani ita din mutun ce mai kafa kafa da mutuncinta, kin ga idan halinki ne kuka kowani namiji ki bari idan kika fita daga gaban Mah sai ki dora daga inda kika tsaya, aman a yanzun ki kula, ki kiyaye, ki ajiye komai ki yi hakuri da komai, Bani da damuwa da MU'AMALARKI da MAZA, domin ba hurumina bane, aman inada da damuwa da damuwar mamana.......Shin zaki kiyaye harkar maza a zamantakewarki a kusa da ita kafin ta bani damar na mayar da ke gaban iyayenki?". Ya fada da yannayi na serius, ya fada yana kallonta tare da tsatsareta da idannuwansa yana jiran amsarta a kusa dan ya kara gaba Cike da mamaki Muneerath da ta fara jin haushin maganarsa tana tunanin to a mema ya dauketa ne kwata kwata tunanin kar ya ilatata ya shige mata ta turo baki ta dan saki harare ta ce" To tsakani da Allah a mema ka dauke ni? Hala ni yar iska ce? Inace kai ka rike min hannu da nan dina kau?".......ta karashe tana mai nuna kugunta cike da jin haushin furucinsa "Ikon Allah" shine abinda ya kubce daga bakinsa yana kallonta Fara tatare naman gaban goshinsa ya yi yana hada rai dan fa ya kuka yar nan ba'a zaman kalau da ita sai ana rashin mutunci da ita, yanzun ko dan wannan dogon sharhin da ya mata ba dan yana tsoronta ba ai ya ci ta masa biyaya, maimakun ta amsa shi sai ta shiga fadin wannan kalma tata ta rainin wayo? Wata tsawa ce ya sakar mata wace ta sakata zabura tana kiki fiki da ido tana kallon ,yama karra hade fuska ya ce" ( *AKOY SU, WALAHI AKOY SU, YAN MATAN DA SUKE TAFIA ISLAMIYAR SUKE KUMA TAFIA BOKO DIN AMAN BASU SAN AINAHIN ME HAKAN YAKE NUFI BA KUMA BASU GANE MEYE AINAHIN MANUFAR ABIN BA, A WAJEN MUTANEN DA YA DACE TA SANI SUNE KAWAYENTA, IRIN KAWAYEN NAN NA ZAMANI MASU ABIN TSORO WA'INDA IDANNUWANSU KE BUDE TARRR SUN SAN KOMAI, TO IDAN NATA KAWARMA NA HAKAN TA SANI BA SAI A KARE A TUTAR BABU, YA KASANCE A ANGUWA TAKAN JI AN CE WANCE TA YI CIKIN SHEGE, WAYE YA YI MATA? WANE NE YA LALATA TA.........IDAN BA HADUWA TA YI DA LALATACIYAR DA TA FEDEMATA BIRI DA ABAWA CEWAR GA NUFIN LALATAR BA ZATA GANE BA, ABINDA DAI ZATA GINU A KANSA SHINE TSORON KAR A MATA CIKIN SHEGEN, SAI NA GABA TANA IYA KASANCEWA IRIN HALITUN NAN DA U MAGANA IDAN BA KARARA AKA FITO MASU DA ITA BA, BA GANEWA SUKE YI BA SHI YASA TAKE TAFE A BAIBAI KUMA KOMA ME AKA CE MATA TAKR YARDA, IDAN KUN KULA TANA RAYUWA NE A TSAKANIN GIDA BIYU, GIDAN SU KAWARTA DA TAKE MANGARIN RAYUWARSU HAR TAKE FATAN ITAMA TA ZAMA IRIN HAKA BALEMA IDAN SUNNA MAGANA DA ITA DA KAWAR TATA TANA FADA MATA MAMANTA TA HANNA SU ZAGI A GIDANSU, SAI ABIN YANA BATA MAMAKI DUBA DA NASU GIDAN ASHAR BA KOMAI BANE! SAI UWA UBA KARIYA IRIN TA UBANGIJI, ALLAH SHI KE KAREWA ......SAI KA RAYU A ANGUWA TA BADALA AMAN IDAN ALLAH YA TSAREKA BA ABINDA ZAI FARU DA KAI HAR KA YI KA GAMA RAYUWARKA A TARE DA SU........................abinda baya kasancewa cen dama ba kasamracen bane watau baya cikin rubutacen al'amari* ) 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*