Sashe 17
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
daina yi kina barin min na maki, kar abin ya maki yawa ga haukan dogari ga fadace fadace, yanzun dai jeki daki na sayi fadan kyaleni da su yau in sun rintsa shege nake" Da wani irin inda inda ya karasa maganar yana wawurar ice a gefe hakan ya sa da ihu du suka dare masu ridar daki na yi masu yin waje na yi, fadi suke kurman gidansu abin ya tashi Haka gidan su MUNEERATH yake, a kowani lokaci cikin tashin bom yake kashe wutarsa kuwa sai Allah ......................................... Kwonci tashi, Muneerath na gannin rayuwa ta kowani fanni, a kadan ta dauki wata daya tana haduwa da abokananta filani masu iyo yayan sarkin ruwa gaba da baya, sun dauki lokacinsu sun kashe aiyukansu sunna koyar da ita yin iyo da soyayar abin a rayukansu, sau kusan hudu sunna gwada nutsewa ciki da ita, na farko da na biyun kusan a sume suke fitar da ita a na ukun ba karamin mamaki ta basu ba, na hudun kuwa sai suka sara mata kawai, ya zamana har gidansu ta sani wajen da mahaifiyarta ke zama aman bata taba haduwa da mahaifinsu ba, sukan kama kifaye su kasa , nata sai dai ta je ta bayar dan ita dai ba iya gyaransa ta yi ba A cikin haka ta ringa neman wajen da zata koyi girki, sai dai abin ya gagara, sam ta kasa samu, sai a gidan su Amina ake koyar da su abinda kamar ana zubawa ana wankewa ne a kanta, du yadda amina ta kware ita ta kasa dafa abin kirki, ta kasa dafa abu ya dahu ya yi dadi sai dai ta kona ko ta cika wani abin da zai kasa ciyiwa A haka yayanta ya kawo mata journal din da aka fadi bayanin za'a dauki sababin HOTTESTE a babar makarantar da ake horar da su Ta jima tana jin juwa, makarantar tsakaninta da gidansu tafia ce mai nisan gaske wace ake cin kusan rawa biyu da rabi a mota, kuma a cikin garin take Bayan wannan irin tsarabe tsaraben da za'a kawo kafin a samu shiga, uwa uba gwamnati na biya maka rabi ka biya rabin da ta tabata ko ita aka siyar ba zata yi kudin aikin nan ba Kamar yadda ta saba kadaice kanta a gaban matsala dan ta sanar da wanda ta san shi kadai ke fitar da ita, shi kadai ke bata hanya, shi kadai ke rufa mata asiri ta yi, takan raba dare tana hawaye a cikin sujadarta ta fada masa ta sanar masa ga abinda take so, aman idan alkhairinta ne Ta mayar da yin azumi abu mafi sauki a duniyarta, ba rana kulun yi take Ta kwatanta yiwa oga zancen ya ce bata da hankali Ta tunakari Mama ta ce da ita" Munne in dai ba so kike na fita yawon banza ba na tara kudin nan, ke ko karuwanci muke ai yanzun ba tsada bale mu iya tarawa dan Allah ki raba kanki da shirmen banza , yo ni ko dudin nan gareni ai ba zan zuba ba domin abin nan ba lale ne ka samu ci ba, kana oya zuwa ka fadi shikenan an yi asara" Haka ta dawo ta kara kusanta kanta da Allah, tuni Amina ta fara karantun likitanci kuma tana jiranta ta tardota dan ko ita bata bata kwarin gwuiwar wannan shirmen Tana ji tana gani ranar da aka saka ta zo ta wuce, wace ta tabata da an yi an gama, hakan ya sa ta yi kuka, kukan rashin rabo ne ko na gannin mafarkinta ya barta ne? A haka ta dawo ta ci gaba da rayuwa shiru shiru da ita Da yawan yan cikin gidansu kan yi daria su ce ta dogari yanzun aljannun shiru shiru ta dauko Yayan nan nata daya kwal shi ya san me take ciki, kuma abin na damunsa, ba dan komai ba sai dan ya san a kan sannin ciwon kanta take damuwa ba a banza ba Shawarar ta je zuwa University bya bata, ta tafi ta yi karatunta ya bata, a dole ta harhada ya nata ya nata ta fara tafia jami'a Abinka da abinda baka so, baka yi niyar yinsa ba gaba daya ba gane komai take yi ba, a UIT din idan ta je tana yin jeka ka dawo ne kawai, gashi wataran abinda zai maidota kadai tashin hankali ne dan har labe take dan kar a rage mata hanya, gashi babu yan anguwarsu a nan bake su ringa yin hanya daya Da yawan lokuta takan yi wani tunani , sai ta basar ta yi murmushi kawai idan ta tuna cewa ba lalene abinda bawa ke so ya zamo alkhairi a rayuwarsa ba, ba lale ne Allah ya bata burikanta duka biyu ba, ta tabata rashin wannan aiki na nufin zata samu Dogari ne Ta kasance mai fitowa da jakar makarantarta a baya, a cikin jakar nan tana dauke ne sa takardunta kaf na anfani harta da na Bac dinta dan bata barin takardunta na anfani dan gudun a shiga a cicira mata su Tafe take sanye sa doguwar riga irin yar kanti din nan, du yadda rigar ta kai da budewa daga kasa sai dai idan iska bata kado ba sai ta nuna abinda bata so a gani din Kanta sanye da farin dan kwali bata yane shi ba, sai farin silifas mai tudu Tafiarta take tana shawagi kamar wata tauraruwa duba da safia ce karfe takwas ne da kwata Bim bim bim................... motar dake biye da ita sai kara yi mata oder take aman sam ta ki ta tsaya ko ta kula shi Danewa ya yi da karfin da ya sakata juyiwa rai bace ta zo wajen motar Tana zuwa gannin ya tsaya sai da ta fara dukan tayar da kafarta kafin ta leka rai bace ta ce" Kai wai meye? " Jan buzun dake zaune ya tsume abinsa ya ga kalaci da safiar nan sai ya sakar mata murmushi da hausarsa irin ta bugaje ya ce" Sannu yan mata, yi hakuri yar budurwa shigo mana na kaiki inda zaki je" Kallonsa ta yi gannin bama wani baba bane sosai aman sai wani abu yake wai shi ya ga mace , da gatse ta samu kanta da fadin" Baka da isashen man da zai kaini har gidan Hottest " Gannin ba wani yannayi na yayan da zasu iya shiga wajen ta yi ba sai ya yi tunanin ko aiki take a cen na iirn wanke wanken bayinsu, ko kuwa gidansu a wajen yake, Cike da shakiyancin koma menene shi fa gidan hutu ya gani ya ce mata" Shigo mana ki gani idan ba zai kaimu ba"