Sashe 8
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
5 A hankali ta karasa inda yake zaune, lalausar alkyabar dake jikinta ta Veloor mai ruwan baki da duwatsu farare kal kal kal ce ta jata sosai a jikinta ta gyara ta zauna tana kara kallon lalausan gashin jikinsa kafin ta saka hannayenta ta janyo shi jikinta sosai ta dora kansa saman cinyarta Gashin kansa take ta shafawa a hankali kafin ta ci gaba da fadin" Haramun ne aikata zina, Allah ya yi alkawarin azaba ga mazinaci idan bai tuna ya daina ba, ina matukar mamakin kasarku da ake yinta a bayane, harma gidanku gida mai daraja, shin baku da kyankyami ne?" Idannuwansa dake lumshe kamar ba zai taba buda bakinsa ya yi magana ba da kyar ya iya budawar a sanyaye ya ce" Me na yi?" Ajiyar zuciya ta sauke cike da kwarin gwuiwar son gannin ya cenza ya dawo mutun sak irin na kowa ta ce" Abinda na tarar da kai kana shirin yi" Lebensa na kasa ya cije a hankali ya ce" Khalb, i'm sorry to say ts aman yaya zan yi ne? Aikina ne " Muryarta still a nutse ta ce" Aikin da ba kowa ne yake sonka da shi ba? Wai yanzu du darajarka ka gwamace ka je ka yiwa wasu karti aiki? Kai fa Allah ya haliceka ne da darajarka , HANJA kana kwonce sai a yi maka komai, ka bar aikin nan ka yi aure ka dauki lamarin sarautar dake rataye a wuyanka" Idannuwansa yake lumshewa ya mata shiru bai bata amsa ba hakan ya sa ta dora da fadin" Zina mugun aiki ce , mai cinye alkhairi, Zina na hanna sukuni tana saka bakin fuska komai hasken mutun, zina na bin dangi , idan ka yi da y'ar wani sai an yi da taka, idan da matar wani ne za'a yi da taka, aya ce, shin yaya zaka yi da ranka idan ka wayi gari ka ga ya faru da matarka?" Still idannuwansa a lumshe suke cen kasan makoshinsa ya ce" Khalb, idan ta zabi bin wasu bayan gani ba shikenan ba ai yancinta ne sai ta je ta yi dan kanta" A dan rikice ta ce" Baka da kishi ne? " Kansa ya dago yana kallonta, a hankali ya saki dan lebensa da ya cije a sanyaye ya ce" Ta ina ake jinsa? Ni na kasa ganewa, kin ga fa kika ce idan na yi budurwar da nake so na ganta da wani nan dina za yana min zafi na ji kamar zan kama da wuta dan azaba, ai nan na zo na ce maki na kama su Rozario a hotel sunna hvng sex aman ni komai ban ji ba, da ta bani hakurima nu mantawa na yi sai dai na bara masu soyayarsu ita da shi dan na ga ya fini sonta ko? To wai ko dai ana haihuwar mutun ba kishi ne? KHALb ni ban ga abin damuwa a irin abin nan ba, abu ne na ra'ayi, ka yi da wace ya kama ka ji kana ra'ayin, kuma ni ban taba zuwa na kwata ba, su suke zuwa sunna rawar jiki su kawo min, sannan maganar aure ni yanzun idan na ce zan yi aure har ba zaki hanna ba? Kin fa san meye yake jira, jira yake na ce ai zan yi aure ya nemi sakani a harkar sarautarsa, ba zan iya ba, na fada maku idan har na zauna to fa babu jirgi a duniya!" Shirun da ta yi a hankali tana ta shafa gashin kansa dan ta ga ya fara caza ne ya saka shi kara komawa a hankali ya kara kwontar da kan nasa kafin ya ringa sauke ajiyar zuciya wata na korar wata har yana jin makogwaronsa na masa zafi dan maganar da ya zuba mata Bata karaya ba a sanyaye ta ce" Sai na ji tsoro na kama min zuciya, sai na ji kamar zan fashe da kuka, ka kuwa san meye rashin kishi? Du namijin da baya kishin iyalinsa ba zai shiga aljana ba, Khalb me yake damunka ne? Ko dai a gaba ka san shi ainahin kishin kansa ne? A hankali ya ce" Kamar yaya?" Itama a hankalin ta ce" Ina nufin a gaba ka samu wace zaka yi kishinta " Da dan murmushi ya dago gaba dayansa ya mike tsaye kafin ya dan rankwafo a hankali ya rike hannunta na dama ya manawa bayansa kisss a sanyaye ya ce" Na kula yau horon da kika yi niyar bani shine hadani da ciwon kai, zan he office now plz ki ce masa na yi tafia kin ji? " Yana gama fada ya juya ya yi gaba ita kuwa ta raka shi da kallo kafin ta dan dafe habarta ta yi wani yannayi na tagumi a hankali ta ce" Ya Allah, ka karra jadada rahama ga abokiyar zamana mahaifiyar yaron nan, ka shiryar min da shi" Mikewa ta yi ta gyara gadonsa da kanta ta dauke rigar da yarinyar ta cire tana girgiza kanta cike da jin tausayi da kuma haushin tarbiyar yarenmu, shin ina zamu je? Ta sani a wajenta wannan ba wani abu bane domin ba musulma bace ita yarinyar, aman duda haka shin ina akida? Jikinta dai a sanyaye ta fito nan aka amshi abin hannunta ana rike da kayanta suka juya suka shiga watsetsiyar motar da ta kawota nan din suka kama hanyar baban bangarenta A lokacin da ta fito bayan an bude mata ana ta gyara mata hanyar wucewarta suka yi ido hudu da kanwar tata A kasan zuciyarta take ayana.....' Lalle ita kanta zata so gannin yarinyar da zara motsa zuciyar yaronta, wace kala ce bata kawo bukatarta da harinta ba, farar ce, yelow din ce, fararenma irin mai dau din nan ba wai sama sama ba, kai ba'a maganar kyan aman cikin ikon Allah cikin biyu ne ki zabi daya ko ku ga walen junna ko ki kama gabanki ba abinda ya dada shi da kas, shin wacece? A ina take? An halitota ko a gaba?.......' ................................................ "Kwana biyun nan kina cikin yannayi na rashin karfin jiki Muneerath, me yake damunki ne dan Allah? Kin ki ki fada min gashi ana ganninki za'a gane cewar kina cikin damuwa, me yasa kike da zurfin ciki mai tsanani a gareni? Ko kamar yadda kika saba ce min ba zaki taba fada min abinda ya shafi cikin gidankun bane?" Amina ta karasa fadi tana kallon Muneerath Murmushi mai ciwo Muneerath ta yi tana kallonta ta ce" Ba zaki gane bane Amina, ina cikin tsaka mai wuya, na tambayo nawa ake koyar da iya ruwa na garin nan an ce du awa daya jaka uku, Amina idan na ce zan saka kaina a wannan sha'ani ai sai a yi tunanin ko na fara rashin jin magana ne, waye zai bani kudin nan? Ta ina zan samu na cika burina?" Amina ta zauna kusa da ita itama jikin nata ya yi sanyi sosai da wannan lamari na kawar tata, dunia na fadar abubuwa a kan gidan nasu, ana fadar lamari marar dadi, fadi ake ko a wajen cin abinci kowa ta kansa yake yi, ana fada cewa komai na gidansu tamkar na mutanen da kowa ke ikon kansa, irin gidan yan barikin nan, gida ne da iyayen kansu basu da tarbiya bale y'ayan, aman ita sam bata yarda da wannan magangannun ba domin kawar tata ko kudi ta bata bata amsa, ko wajen cin abinci idan ta zo gidansu in sukai mata tayi bata ci kiri kiri take nuna ta ci a gida, bale a rayuwarta ta ki jinnin ta yi hirar gidansu, mugun zurfin cikinta baya iya barinta ta budi baki ta yi bayanin damuwarta, wani lokacin haka kawai zaka ga ta fashe da kuka mai tsanani idan an taru anai mata tambayar lafia? Sai ta ce mutuwa ta tuna, daga haka kuma waye zai ce wani abu? Mutuwa ai ta isa idan aka tunata a yi kuka ga mai tunanin makomarsa A sanyaye ta ce" Me yasa irin naki ra'ayiyikan suka kasance masu tsauri ne? Me yasa idan Allah ya cida mu muka samu bac din nan mu je mu karanci fannin likitanci ko fannin koyarwa ko abubuwa da yawa gasunan wa'inda mun tabata koda iyayenmu basu da karfin talafa mana idan muna karatu a Niger zamu kai ga ci har mu zama wasu gobe? MUNEERATH ni bana hangowa mace musulma mai tunanin yin aure da haihuwa a kusa yin irin aikin nan, bama wannan ba ki duba fa ki gani ko a y'ayan masu kudin da suka samu damar shiga makarantar nan sai masu gagarumin ilimi da kuma tsari kamar an zana su, Muneerath ba raina halitar da Allah ya maki ko nasabarki na yi ba, ko daya matakan da ya dace a taka a hau a kai wajen da kike so din nan ne ya fi karfinmu nesa ba kusa ba, waye zai tsaya maki? Ta ina zaki samu shiga makarantar da ko ka shiga ba yana nufin ka samu bane aa yana nufin ka je ka sha gwagwarmaya ne idan da rabonka ka wuce idan babu kima ka bata shekaru ka dawo gida?" Muneerah ta mike daga zaunen da take tana kade sket din dake jikinta mai ruwan blue budade da ta siya a wajen gumama ta ce" Amina, zan je na ci gaba da fadawa Allah, zai tsaya min, na tabata alkhairi ne domin du idan na yi sallah fada masa nake idan ba alkhairi bane ya cire min a raina, aman kasancewar kulun karuwa yake a cikin ran nawa inaga idan na zauna na zuba ido zan kasance cikin masu fada nan gaba ina karkata kai cewar a da fa burina shine na zamo hottest, idan akai min tambayar shin yaya aka yi ban zama ba, cike da mutuwar zuciya sai na tabatarwa wanda ya tambayenin cewa dan ya fi karfina banma kwatanta ba!, na fi son na fadi cewa ban zama bane dan haka Allah ya hukunta domin na gwada dukan damata Allah ne bai yi ba" Cike da tausayi Amina ta rakata da kallo har ta yi gaba Shigar Muneerah ba shiga bace ta y'ayan masu kudi, domin a jikinta riga ce bak'a ta gwonjo da blue din sket shima na gwonjo wa'inda ta siya da kudinta abinta, sai blue din