← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 114

Sashe 34

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 2 Murmushi Aleesa ta saki ta janyo hannun Muneerath dake biye da ita ba dan komai ba sai dan bata so ta janye hannuntada karfi ta yi mata sartse duba da laushin hannun matarsa ita kam ta janyowa kanau ya kashe su baki dayansu a kanta, aman in ba dan wannan ba ita ai so take ta yi ta koma ko zata dace da dogari daya Da sauri sir ke biye da shi da takarda yana rubuta dukan abinda ya fada a rarabe ba wani a fayace ba, shi dai burinsa su rabu lafia Sosai jikinsa ya yi sanyi a lokacin da ya ji an tashe shi a wannan waje da yake, sai dai a lokacin da ya ji cewa a gabanan aikinsa zai dawo yawo tare da hanja ne sai ya samu farin ciki maimakun bakin ciki, dan haka nan da nan ya koma office dinsa ya bugawa mahaifin Muneerath waya ya sanar masa abinda yake faruwa a ruffe, dan an shaida masa ne kawai za yi tafia da ita kasar ingila dan ta fara aikinta A mamakance ya ce" wai yar ogan? To aikin ma meye kuma? Jirgi ne yar oga zata taka ta daga?" Sir ya bashi tabacin hakan ne, mahaifinta maimakun ya zaburo ya zo ya duba, ya ga yarinyarsa sai kawai ya tayata murnar hakan ya ce a hada su a waya A lokacin da ya karaso da gagawa ya mikawa sojan dake tsaye ya kusa da motar da Aleesa ta sakata kawai tana kallonta cike da admiration ya shaida masu cewar mahaifin yarinyar ne aka bata waya ta kanga a kunnanta , abinda mahaifinta ya fada ya sakata yin tsuru tana sauraronsa Walahi, bilahi, rashin kulawar iyaye ciwo ne, du irin zumudinta da wannan aiki jin yadda mahaifinta ya mata magana sama sama da alamun yana tayata murnar cikar burinta da son sannin wai da gaske zata daga ko yayane? Sai ta ji gaba daya duniyar ta yi mata zafi, a hankali ta janye hannunta daga cikin na aleesa dake kallon yannayinta ta kwontar da kanta a gefen kujerar ta jinginar, muryarta na rawa ta ce " Oga, ina mama " A wani shanshakai ya ce" ni dai da safe da zan fito mun hade da ita zata je wajen biki yanzu ban san ba ko a ina take gaskiya" Wani irin zazafan hawaye ne suka shiga kokarin zubo mata a kan kuncinta, gaba daya sai ta dantse lebenta na kasa ta kasa ci gaba da magana dan tsoro take kar ta budi bakinta ta fashe da matsanancin kukan da kowa zai rasa gane kanta dawo amsar wayar ba a haka har sarakan suka dawo kanta a jingine da madubin mota idannuwanta lumshe bata ga lokacin da dogaran da take zumudin su hade ba suka zo kusa da motar tasu aka hanna su matsowa kusa sunna yiwa HANJA kirarin da bai san yaren da suke yi ba har ta ji motar tasu ta tashi ta buda idannuwanta da sauri tana kallon mutanen dake cikin makarantar tare da waigawa idannuwanta na karra budewa tana kallon komai wasu hawayen na zubo mata Budurwar dake tare da su ne take kallonta, ita mamakin da take irin yadda ta ga Mamansu ta rike hannun yarinyar nan, ko dai ya sarkin garinsu ce? A haka suka nufi filin jirgi, kwata kwata bata tare da wani zumudi ko yannayi na farin cikin tafiar nan, bata nuna komai ba koda ta zo shiga jirgin da take mafarki ba dare ba rana, iyaye ba abin wasa bane, a zuciyarta ta dauke su da wani irin daraja, a yadda take gannin y ya da iyayensu sunna mu mala ta kula da kaunar junna ita ba haka bane, shin iyayensu aun haife su dan dole ne ko menene? Halin ko in kula na kan mahaifinsu, ba ruwansa da abinda ka fita yi ko kake yi, shi a tunaninsa ai kauna kawai ya sakar masu mara su yi fitsari ne, ita kuwa mahaifiyarsu bata san yaya zata kwatanta irin nata abin mamakin ba, sam bata san a wani waje ya dace ta ajiye mamansu ba, Sosai take hawaye bata kula kowa ba, Aleesa kuwa sunna shiga Hanja ya kaita wajen zamanta du yadda ta so ya kawo yarinyar ya kiya ya ce da ita ta zauna har Allah ya sauke au lafia sai ta ganta A dakin da yake na hostess a nan Sir Muhammad ya laya su, kai yake yana kawowa yana hankalce da hawayen da ya ki tsayawa Muneerath da kuma Ameerah da gaba daya ta fice a hayacinta itama kan wannan koma baya da ya sameta domin koma baya ne a wajenta bayan matakin da ta taka yau a wayi gari ta ganta a wannan matakin kuma? A nutsensa ya ce" tafia ce da manya, ko bai taka matsayin babanmu a wajen aiki ba shi din baba ne a duniya, ku sani biyayar da zaku yi masa ita ce ribarku, ko me ya ce kar ku daga kawunnanku har sai ta bar wajen dan ko da abokan aikinsa baya gardama bale a yi musu da shi, ku kula ku kiyaye dukkan wani motsinsa baya korar mutun a dawo da shi ko wa ta tsaya masa sai dai iko na Allah, kuma yana da damar dakatar da kai koda a tsakiyar tafia ne bale a kasa!" Takun tafiarsa ya saka Sir M dakatar da maganarsa sannan ya koma gefe ya ja ya tsaya Kamar yadda ya saba kai kawo haka ya yi kamar sau biyu yana karewa kowace kallo kafin ya ja ya tsaya a tsakiya Muryarsa a dake ya ce" Aiki ya kawo kowace, du wace ta yi abinda ba aiki ba a tsayin tafiar nan ba zan iya tafia da ita ba, mahaifiyata bata cin abu mai zaki, haka mahaifina baya cin abu mai magi da sanyi a kiyaye" Yana gama fada ya juya ya yi dakin Pilot shima dan madaidaicin daki ne mai dauke da bayi da madubi wanda suke shiga su shirya kansu kafin su dauki jirgi Sir ne ya dawo gabansu ya shiga rabawa kowa aiki cike da kula , sai da kowa ya nufi wajen da aka bashi kafin ya maido dubansa kan Muneerath dake kallonsa tana kikifta idonnuwanta A sanyaye ya ce" me yasa kike kuka? " Kanta ta girgiza har yanzun hular na kanta , stil dai a sanyayensa ya ce" mu je na nuna maki dakinku, ki yi wanka ki zauna har mu sauka, idan kuwa barci zaki yi sai ki kwonta har mu sauka in sha Allah" Kamar ta ce da shi ba zan je ba, kamar ta saka ihun a sauketa ta koma gida, ji take kamar zata hadiyi zuciya dan damuwa sai dai bata musa din ba ta bi bayansa lokacin ne kuma ta ji an ja jirgi ya fara yar tafia hakan ya sa ta ji zara fadi, sai a lokacin ta tuna ko a cikin me suke, sai a lokacin ta yi sauri ta bi bayansa cike da tsoro suka shige dakin nasu Turus ya yi gannin sandukin da idan an yi mutuwa ake sakawa, watau a nan aka saka gawar wace ta rasun kuma aka ajiyeta a nan maimakun a kaita cen cikin da ake ajiye sandikan gawa na cikin jirgi? Juyowa ya yi da ita ya fito da ita ya nuna mara eajen zama ta zauna ya nuna mata yadda zata daure jikinta da kuma abinda idan tana son yin baci bata son haske zata sakawa idannuwanta da na kunne da safa kafin ya juya ya koma wajen aikinsa zuciyarsa cike da damuwar halin da take ciki, kwarai ya san dAmuwar ta iyayenta ce, aman kuma ya mara uzuri dan ya kula da ake cewa Allah mai fitar da kafuri a cikin musulmi, musulmi a cikin kafiri hakan ne, su suka haifeta aman halayensu ba iri daya bane Sun yi tafia mai nisa kafin suke sauka dan bai yi biye biyen ko na ba ya dauro niya sai ya ajiyeta kafin ya ci gaba Sun sauka gaba dayansu cike da gajiya, du irin halin da take ciki sai ta ringa jin idan ta daga kanta juwa zata kifata a kas, sannan ta ringa gannin abubuwan mamaki da tsoro na yannayin ginnij da idannuwanta suka iya ganni yinwar dake cikintama ta isheta dan kuwa ta nuna cikin nata ya dan fada ga juwa na damunta Kwata kwata bata gane komai har aka sakata a wani daki mai masifar sanyi da kyau a nan filin jirgin dauke da gado daya tak Bata iya tsayawa yin wata wata ba ta faa saman gadon nan bayan ta cire dan sosonta dake kafarta ta kifa kanta kafin ta fashe da wani irin kuka mai karfin gaske tana karra cusa kan nata cikin matashin kan lalausa da shi a hankali take fadin" Mama, Abanmu, shin ina rayuwar nan zata kaimu? Bayan nesan cen da na yi da ku a yanzun na yi mugun nisan da ba zan iya kai kaina inda kuke ba ko a guje na fita koda wani jirgin zan shiga ba, ya Allah ka kare ni da kariyarka, kar ka bari wani ya shiga lamarina ya lalata min rayuwata, Ya Allah kar ka bari kudi ko saurayi su rude ni na bar hanyarka, ya Allah kar ka ba talauci ko kangin rayuwa damar da zasu saka ni manta ka, Allah ka shiryar min da iyayena su gane cewa amanata ka basu zaka tambaye au a gobe kiyama, ya Allah kar ka kashe ni a nesa da dangina ta yadda ko gawata ba zasu gani ba bale au salaceni, Allahna ka.....,.," Bata karasa ba ta ji wata ya suwaiwai din murya na yi mata magana ta hanyar kiranta da mssz, Da sauri ta dago fuskarta cike da hawaye tana gogewa ta sauke dubanta a kan matar Taf, sai kawai ta saki baki da hanci tana kallonta dan kuwa budurwa ce ko na ce mace ce yar gayu iya gayu sanye da dan bintilin sket da riga mai dogon hannu yan berayen mamanta sun matsu bayin Allah gashinta daure a tsakiya ta gyara tsayuwarta da kulawa tana mamakin to a ina sir ya samo wannan yarinyar da sam bata shige da
Chapter 34 · 0% Book details