← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 114

Sashe 77

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
4
Sarai kunnayensa sun jiye masa dukan abinda ta fada, sai dai ga mamakinta shiru tamkar ba kowa a dakin, hakan ya sa ta yi tunanin kawai bai jita bane dan haka sai ta kara gyara tsayuwarta sosai tana kara dan shafa gefen fuskar Mah da hannunta na hagu dake kusa da shi, da dayan hannun kuwa na dama tana dan susar gefen duwawunta irin na ka rasa me zaka yin nan kana neman fitinar nan a hankali ta ce" Cewa na yi cika kallo ba halayan mutanen kirki bane, kai kuma sai ka wani tsatsare mutun da ido ko me yasa kake haka? ?"
Wannan karron ma shirun ne hakan ya sa a hankali ta dago zarra zarran eylach dinta ta sauke dubanta a kan fuskarsa dan ta fara tunanin ko dai barci ya yi yana jinta tana magana ya wani shareta bayan ta san ba halinsa bane barin sai ta kwana?
Ga mamakinta kallon nata yake, kuma dai a yadda ta fahimta ba suma ya yi ba domin ai yana numfashi, hakan ya sa ta dan yi gaba kadan ta dawo, ta kuma yi gefe kadan ta dawo, gannin kwayar idannuwansa na binta ya sa ta kuma yarda cewa ba a sume yake ba
A kasan zuciyarta kuma ta ce' Na shiga ukunna , to ni yanzun yaya zan yi da shi kar dai ya fashe min da kuka a wajen nan dan mamansa ba lafia, to wai dama shi Pah yana zuwa yawo ne gashi sun shagwaba yaro sun barshi a gida bata da lafia zai haukace min? In ba mutane ba yanzun du kudin nan na Pah kuma yake neman wasu kamar wada zai shiga kabari da kudi?, Wani lokacin sai na kasa kasa gane son kudi irin na masu kudi walahi' a bayane kuma sai ta yi kalar tausayi tana dan kallonsa aman sai ta cire dubanta daga ta hada ido da shi domin sai kawai ta ji kamar zata kifa masaa kansa, a sanyaye ta ce" Ka yi hakuri ka ji? Ka ga fa cuta ce ai ba mutuwa ba kau?, Nawa suke yi sunna tashi mai lafiyar kuma idan lokacinsa ya yi sai ka ga ya mace murus har lahira ba wanda ya isa ya hanna, ka daina yi mata kuka ka mata adu'a ka ji? Kuka ba magani bane, idanma baka iya ba mu je na kokoya maka ka dawo ka ringa mata dan walahi ni din nan a islamiyarmu har jira ake na fara kira'a, yanzunma sauke mata kanta a samanka kali fa ai sai ta kage baiwar Allah"
Abinda ya gama sani game da wannan yarinya shine ba zata taba daina bashi mamaki ba, ya rab wai irin idan aka ga yaro na rigima na mamansa da ake masa wayo a rarashe shi ne take son masa wai ya bar kuka ko a ina ta ga yana kuka??, Sai dai wani al'amari sai haka din ya rage masa kuncin zuciya, haka kawai ya ji yana son yin abinda ta fada, magangannun nata sai suka samu muhali a cikin kwakwaluwarsa harma ya samu umarni daga kwakwaluwar tasa kan ya sauke kan na Mah kar a je ta kage din ne, dan haka a hankali ya saka hannayensa biyu ya sauke kan Mah ya mike ya karra gyara mata kwoncinta sannan ya mike gaba dayansa hakan ya kasance fuskar Muneerath na daidai kirjinsa ya kuwa tsaya mata kikam a saman kanta, hakan ya sa dan dole ta kauce kadan tana lumshe ido dalilin kamshin nan nasa da ta rasa shin wani irin turare ne mai irin sansayen Kamshi da naci haka a jikinsa
A hankali ta kai zaune a wajen da ya tashi kanta a kasa tana jin yadda hancinta ya karra cika da kamshin turaran nasa
A hankali ta dan dago dan kallonsa, sai ta ga ita yake kallo hakan ya sa ta karra tura bakinta aman kuma ta kasa furta masa komai
Idannuwansa ya lumshe kafin ya juya ya kama hanyar fita
Har ya kusa fitar ya juyo yana kallonta , hannunsa na dama ya dago a lokacin da suka yi ido hudu ya kai wajen lebunnansa
Cikin yannayi na sanyin jiki da iya sarafa karatun kurma ya yi mata alamu na zif wa bakinta, sannan ya nuna mata Mah dake kwonta ya kuma maida hannun wajen bakinsa ya yi mata alamu da kar ta mata hayaniya kafin ya lumshe ido ya kai hannayen biyu gefen fuskarsa ya mata alamun ta barta ta huta, sai kuma ya dan fitar da idannuwansa da yannayi irin na ta fahimta? Kafin ya kai wajen kunnensa ya dan ja sai kuma ya dantse hakorinsa a kan lebensa na kasa wanda Muneerath dake bin dukkan motsinsa a saman lebenta take fasarawa kanta abubuwan da yake nunawa da yarenta watau hausa har ta dire kan' Idan kika ki zan cije maki lebe'
Ido ta dan fitar, a nata fahimtar kennan kafin ta yatsina fuska ta cire kanta shi kuwa ya juya da dan sauri ya fice dan amsa kiran karamar wayar da Pah ke kiransa da ita
Yana tafia ta bi bayan kofar da ya rufo da kallo
Ajiyar zuciya ce ta kwace mata kafin ta mike ta kara dan yaye bargon Mah ta tataba jikinta
Jin jikin ba zafi, ga kuma karrin ruwanta na tafia daidai sai kawai ta yi bismillah a hankali ta haye saman bed din na Mah ta kwonta daga saman bargonta kasancewar lubukeke ne, ta dora kanta a kusan gashin na Mah a hankali ta ce" Kin ga, kece mamana fa, ke ce Ogana a garin nan, kin ga Allah ne gatana kuma ke ce gatana a garin nan, dan Allah ki rufa min asiri ki mike daga cutar nan taku ta yan gayu kar ki sheka yaronki ya sheke ni ya ba zakinsa ya cinye banza ya yarda kasusuwana kin fa fi kowa sannin irin tsanar da ya yi min kau? Ban san me na masa ba ko yanzu nunan ya yi zai cije ni, wai ko dai maye ne shi? Mi ya kawo cizo a lebe?"
Ta dan yi murmushi ita kadai ta ce" Wai shi mai leben nan uwa na jarirai da wasu hakoransa masu laushi yana tunanin zai iya karawa da hakorana ne?, Yo idan na dantsa masa cizo ba sai a asibiti za'a iya bambareni daga jikinsa ba?, Da wasu girarsa kamar na yan gayun yan matan garinmu, namiji da shi yana aske gira"
Sai kuma ta lumshe idannuwanta a bayane aman kuma kasa kasa sosai ta shiga yiwa Mah adu'ar da duka ta zo bakinta tana tofa mata ta bayanta, ta yi dare dare a saman bed dinta sai ga barci ya kwasheta mai dadi irin na safiyar nan gata a saman lalausan bargo abinta
Rike yake da hannun mahaifinsa, sosai yake jinjina soyaya irin ta iyayensa, a yanzu haka sai da ya jajirce ya rintse ido ya tsaya gaban mahaifinsa ya shaida masa bata da lafia ne, cikin ikon Allah ya yi luuu zai zube masa domin juwa ce ta kwashe shi da hanzari ya rike shi a jikinsa yana mai yi masa magana da dan karfin da zai wartsake ya nuna masa cewar rashin lafiyarta ne ciwon cikinta ne, kuma a yanzun baya bukatar su zube masa su biyu, idan suka zube masa yaya suke so ya yi ne?,, Hakan ya saka Pah ya jure ya daure ya ringa sauke ajiyar zuciya har ya samu nutsuwa kafin ya kama hannun HANJA su nufo wajen da aka rike Mah din watau dakin hutunta
A lokacin da suka shigo dakin, abinda ya gani ne ya saka shi yin turus da mahaukacin mamakin da ya saka shi bude baki da ido yana kallonta
Mah da ta buda idannuwanta ta samu kanta da sakin murmushin yannayinsa, a hankali ta mikawa mijinta hannu da ya nufeta da sauri stlll tana murmushin Hanja din da ya yi mutuwar tsaye a wajen shigowar yana kallon Muneerath dake barci a saman gadon Sarauniyar ingila a bayanta a irin wannan lokacin da take rashin lafiya, ta wani lafe abinta har an luluba mata bargo gashinta dake daure ya karra yin lumbuk a jikinta
Da kallon mamaki yake bin Mah da ta kama hannayen Pah ya taimaka mata a hankali ta sauko kafafuwanta ne masu sanye da dogon sakaken wandon asibitin da kuma safa dinta kafin ta maida hannunta a hankali ta gyara mata rufarta ta juyo tana murmushi ta dora tafin hannunta a gefen fuskar Pah da idannuwansa suka tsumu da kauanar da kuma tausayin matar tasa a sanyaye ta ce" Khalb, yaushe ka dawo?"
Maimakun Pah ya bata amsa sai ya yi gagawar rungumeta a jikinsa tsam idannuwansa a rintse yana jin yadda zuciyarsa ke kadawa
A hankali take dan tapping din bayansa itama nata idannuwan a rintsen a hankali ta ce" na ji sauki fa "
Pah ya dan girgiza kansa a sanyaye sannan muryarsa cen ciki ya ce" sai da na matsa ciwon ya motsa?, Wani irin ciwo ne wannan da ba zai barmin mata ta huta ba? Da ace na ga wannan dan aiken ciwon da na kama shi ban san yaya zamu kaya ba, ALEESA lafia fa na barki"
Murmushi ne ya kwace mata, sai kuma wani irin tausayin kansu ya kamata, a hankali ta ce" haba khalb, idan da karar kwana kuma fa?"
Da sauri ya ringa girgiza mata kai tamkar matashin saurayi yama rasa me zai ce mata, sai da ya nisa kafin ya ce" Kin manta wa aka fadawa sauran kwanakin da suka rage masa a duniya?"
Murmushi kai ciwo ta yi ta ce" Ka manta ba su ke da wannan ikon ba?, Sai wanda ba'a gane masa wani ciwon dake iya kaishi ga kushewar ba ya mace ya bar marar lafiyan"
Hanja dake jingine yana kallonsu dukkan bayanansu a cikin kunnayensa duda a hankali suke yi aman dakin kai amsa amo ne komai kankantar magana kunnayenka na iya ji
So yake ya karasa ya ce da su dan Allah su daina wahalar masa da zuciya, shin me yasa suka dauki maganar mutuwa hira mai dadi a tsakaninsu? , Sai dai haka kawai kafafuwansa sun masa nauyi , jima yake kamar idan ya matsa kusa da gadon cen akoy abinda ke iya kama shi
Daidai lokacin Muneerath ta farka a barcinta,
Murginawa ta yi dan yaye bargon da aka luluba mata tana cuno bakin an hanna mata jin sanyi bayan yanzun ita din nan ta rigaya ta saba da sanyi
Hannayenta ta daga sama ta bankarro kirjinta tana mika tare da adu'ar farkawa a barci
A hankali ya janye dubansa daga kanta yana mai jin gabansa na dukan tara tara daidai lokacin Muneerath da farin cikin gannin Mah ta farka da kuma Pah ya dawo ta ce"
*ALHAMDULILAH, ALHAMDULILAH YA RAB*
11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 77 · 0% Book details