← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 114

Sashe 29

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 1 Da karfi yakarashe da yaren turanci da fadin" mai girma Prince din ingla, mai jiran gadonmu tare da mahaifinsa da mahaifiyarsa ne suka zo! Kallon kallo suka yiwa junna kafin suke kuma zuba ido sunna gannin wasu gala galan motoci irin masu nishin nan bakake kirin sunna shigowa da wani irin gudun gaske Motoci ne a kala zasu kai kwaya tara koma sama dan kuwa dauke suke da manyanmu na niger du kuwa da yadda ya so shigowarsu har fitarsu ta zama ta dan lokacin da ba wanda zai sani sai dai ina abinda ya faru ya zama dole ya ziyarci wajen nan dan ya dauki wa nda zasu maye gurbin wace ta rasun Daga cikin motocin ne manyan sojojinmu na niger manyan da ganninsu sai a TV, wa nda suke kusa da shugaban kasa , sai baban sarkin Niger tare da manyan dogaransa suka fito suka bude bangaren da sarki yake Idannuwa Muneerah ta zarro a lokacin da ta yi arba da dogarai Jikinta ne ta ji ya fara rawa rawa a dan rikice cen kasan makoshinta tace" Dogari " Bata ankara ba ta ga sarki ya fito cikin shigarsa ta alfarma gefensa wani datijo mai shigar costume bakake kansa aske tas tas ba gashi ko dis a jiki fari ne kal fuskarsa dauke da yalwataciyar fara ya kara mikawa mai girma sarki hannu wanda shima ya amshi hannunsa fuskarsa dauke da yalwataciyar fara A hankali Muneerath ta ce" Wayo Allahna dogarai ne birjik yau a gaban idannuwana tare da sarki? " Saudat ce ta riko hannunta ta ce" wai da gaske abinda ya fada ko menene? Me yakawo sarkin ingila kasarmu ? Me suka zo yi nan wajenmu? Ikon Allah" Ameerah ce ta yi saurin kallon yan matan ita kanta bata gaskata abinda kunnayenta suka jiye mAta ba, abinda dai ta sani mutanen nan da suka fito daga cikin mota na kasarmu manyan mutane ne da haka kawai ba zasu tashi su tako su zo nan ba koda kuwa makarantar babar makaranta ce da ake ji da ita a niger baki data dan tana daya daga cikin manyan abubuwan dake shigo da gunduma gunduman kudade a kasarmu, aman abu daya ne ta sani "Prince" din ingila da aka ce shine baban ogansu a cen baban kampanin jirgin air peace, shine baban matukin jirgin da kampaninika da dama ke kokowar son gannin ya zama nasu, yana daya daga cikin masu kwakwaluwar kera wannan abu mai shegen nauyin dake tashi a sararin samaniya tamkar leda, shi din nan shine mai jiran gadon mahaifinsa, ko dan aikin gidansa ka samu gani kai din kanka ka zama cele bale shi da kansa, kai baima taba saukar da jirgi a africa ba , koda ya saukar a yanzun bata tunanin idan zai dauko passinger niger, bale har a yi tunanin ganninsa a wannan waje kamar a mafarki, kai da suma sun zama cele, makarantarsu kuwa da ta gama zama babar makarantar da a gabanan gaskiya har yan kasashen ketare zasu dauko , Kasancewar sunna sanye da kayan girki ne kowace wando da riga mai dan tsayi har kusan gwuiwa da abin girki a daure a gaban rigarsu da farar hula ba komai a hannayensu bale a yatsotsunsu dan idan zasu yo girki komai cirewa suke dan samuwar tabataciyar tsafta a wajen aikin abincim nasu, da dan saurin magana ta ce" kowace ta koma dakinta ta rufe ta yi connectd ta yi abin karuwa mun yi baki idan sun tafi zan kiraku mu je wajen Sir kan maganar yarinyar nan, du wace ta so rufa mata asiri ko ta yi niyar kareta dan kar na ci galaba a kanta a koreta sai dai a kore su su biyu dan na rantse maku sai na jaza maku matsalar da ba zaku taba fitar da kanku a ciki ba! Sai na maku shari da ba zaku tana samun lafia a cikin duniya ba dan kuwa sai na saka ku a ukun da baku taba zato ba! Bale ke Saudat kin san ni ma saka hannu aka dauke ki ba dan kudin papanki ya isa ba sai dan muna mutunci da shi, a yanzuma na saka ki koma masa abu me mafi sauki a wajena idan kika min rashin mutunci!" Muneerath na kallonta hawaye aun cika mata idannuwanta muryarta a sanyaye ta ce" ke bakya taimako domin Allah? A cikinmu shin kowa ne ya iya komai yadda ake so? Da yawa sunna da matsaloli a wurare daban daban, me yasa ba zaki taimaka min na iya ba? Me yasa ba zaki talafa min na samu cikar burina ba?" Sai da Ameerah ta yatsina fuskarta kafin ta juya rai bace tace" Dan baki yi min b.........," bata kai ga karasa maganarta ba ta tsaye mata a saman harshe sakamakon gannin abinda idannuwanta ke gane mata Shin shi din ne da take gani a jaridu ko mai kama da shi ne? Dan bakin dan kwalin dake jikin mamansa yake gyara mata sai wata zukekiyar yarinya a gefensu matashiya da zata kai shekara ashirin da bakwai haka danma yannayin dadi ya boye yawan shekarunta balarabiya ce sak sai shinning take yi A bayane ta shiga fadin" what? HANJA? " Kamar a mafaki suke kallon wannan lamari, daga inda suke ba zasu iya cewa ga kamaninsa ba dan ya yi nisa da su sosai sa dai irin yadda haskensa ya kawo inda suke da irin yadda gaba daya aka aniyar kokarin kakare shi kamar wa nda suke tsoron kar kuda ya taba masa lalausar fatar jikinsa sai dai ina tsayinsa ba zai basu wannan dama ba uwa uba irin yadda ya daure fuskarsa kamar wanda yake daf da fashewa da kula mai tsanani dan kuwa ba karamin takaici ya ji a zuciyarsa ba a lokacin da mahaifinsa ya matsa sai sun gana da sarkin garin harda fadi da babar murya cewa ai tun yanzu ya dace ya saba da sarakai dan kuwa babu sarkin da zai ce ya isarma kansa sai wanda ya halici sarakai, wannan shi kadai ne ya isarma kansa A dake sannan cen kasa kasa yace " Mah, ku koma cikin mota mutane sun yi yawa, ba wani zama zan yi ba zan amshi wata ne a nan da zata mana rakiya har zuwa cen din plz Aleesa ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" Tunda ka li yarda cewar ko bamu dauki wata ba muna iya ci gaba da tafiarmu nima sai ka barni na ga yadda kuke daukan yan matan cikin jirgin nan Murmushin yake ya yi da idannuwansa ya zabgawa budurwar nan harara ya mata nuni da motar da idannuwansa ba tare da ya buda bakinsa ko ya yi anfani da hannayensa ba Da sauri ta juya har kamar zata kifa ta yi gagawar shigewa cikin motar da aka bude mata tana sauke ajiya zuciya kafin ta hangi bayansa ta kura masa ido tana kallonsa Karasawa ya yi wajen mahaifinsa, muryarsa ya rage sosai kafin yace" ya dace ka ja matarka ku koma mota sir " Mahaifinsa ya kale shi ya tabe baki ya ce " idan aka ki fa? " Dan murmushi ya yi a hankali ya ce" na sanma ba zaka ki ba, ina son na gana da su ne aiki ne fa? Murmushi ya yi yana kallon matarsa yadda take kallon mutanen wajen cike da admiration shima ya rage muryarsa sosai ya ce" ka ga kaunarta ta gama mamaye min kaf jinnin dake gudana a jikina, tun daga lokacin da zamu taso take cewa kafarta kafarka, kawai ku je ku yi aikin tare mana dan ba zan iya bata mata rai a dan lokacin da ya rage mana da junna ba Kallon mahaifin nasa yake nan da nan ya yi kici kicin da fuskarsa rai bace yace" bamu dora dokar ba zaka ringa min maganar nan ba? Mahaifinsa ya sakar masa murmushi ya ce" sorry " HANJA ya ce" ka sha maganinka?" Mahaifinsa ya kai hannunsa eajen gaban goshinsa ya sara masa ya ce" Yes sir " HANJA ya dan girgiza kansa yana kallonsu suka juya suka yi gaba tare da sarkin da dogarai kama daga masu rike lema da masu tafe sunna kirari abinsu suka nufi cen ciki dan zagayen makarantar Magana ake yi mata aman har ga Allah kunnayenta basu ji ba, a gabanta Saudat ta tsaya da sauri da murya mai amon gaske sannan tana jijiga hanayenta ta ce" Muneeraht ki wuce mu je dakin taro sun tafi sun barmu ta baya tun dazu" Firgigit ta yi cike da zabura a tsorace da jin ihun a kanta tana kallonta ta ce " Lafia?" Saudat ta juya ta fara tafia tana jan hannunta ta ce" ki wuce mu je ciki kina gannin sn shige gaba dayansu!" Biye take da ita dan janta take da sauri sauri har suka bude kofa ta baya suka sanyo kansu Muneerath tace" Saudat baki ga dogarai ba? " Kasancewar kawancensu sun san sirrin kowace wanda take da burin aure sai hakan bai ba Saudat mamaki ba , ita dai janta ta yi suka zauna a layin kujeru na biyu dan na gaban yan matan sun cike su sai Ameerah da sir da sauran manyan ma ikatan gidan da suka halarta nan da nan Daga gaba kuwa wajen kujerun alfarma sojoji ne a tsaitsaye du sun zagaye dakin taron ta yadda idan mai rabon daukan ba dadin zara iya sauka akansa Kasa kasa Muneerah ta ce " Saudat, mu yi mu tashi mu je wajen su kafin su tafi dan Allah na gaishe su" Saudat itama kasa kasa ta ce" Da alamu fadan Ameerah baya zuciyarki ko? Kina ji fa abinda ta ce maimakun mu yi tunanin abinda zai raba mu da ita lafia ke ta wani dogarim cen kike dogain banza dogarin wofi!" Muneerath ta ce " ranki ne ya bace ban sani ba? Ki yi hakuri Saudat kin ga ameerah babu abinda zan yi na birgeta, na tabata Allahn dake tsaya min shi zai tsaya min, kuma kin ga idan freind ya ji abinda ya faru in sha Allahu ba zai kore ni ba, ni na tabata yadda na samu kaina a gidan nan Allah ba zai bada damar a wulakanta
Chapter 29 · 0% Book details