← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 114

Sashe 95

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
6
Muryarta a sanyaye tana kallon saudat ta ce" Sai ina jin gaba daya magangannunki basu dace ba, yanzu tsakani da Allah ina hadin wannan tsigigiyar yarinyar da a jikinta hancinta da farinta da idannuwanta sai shagwabarta ne kadai abin so?, Ke kin kuwa taba gannin Hanja da kyau? Kai ina ga baki taba kure masa kallo mai sunnan kallo ba wollah, Saudat Hanja sai da mace daidai shi, gaskiya ni bana son hade haden nan da kike masa"
Saudat ta saki murmushi tana kallonta ta ce" Wace mace? Ke baki san nasarun nan, bale masu kudin nan, na kai maki karshe sarakin nam, masu kyan nan, masu farin nan, masu daukan karfen nan sun fi son mace yar sharshara irin wannan ta kwoncen ba?, Yaya kike maganar basu dace ba bayan a gabanki da ya bata runguma ta shige jikinsa gwannin kyau tamkar indiyawa ba?"
"Ke itace fa ta rungume shi ba shine ya rungumeta ba, ke baki san kanwarsa bace?" Ta fada a dan zazafe dan gaba daya ji take abin na bata haushi har a kasan zuciyarta
Saudat ta kebe bakinta ta nemi ratsawa ta gefen Muneerath din ta shige, sai dai bata bata damar hakan ba ta dakatar da ita da hannayenta tana fadin" ki tsaya ki fada min dan Allah mana, ki tsaya ki yarda da maganata dan kar ki sa hakan a ranki bayan ba haka bane, kin ga fa yarinyar cen kanwarsa ce, shi kuma yayanta ne, kuma a zamantakewarsu Mah ita ce mamansu Pah kuma abansu ko? Ina maganar soyaya a nan in ba shirmen irin naki ba saudat"
Saudat ta ringa danne dariyarta a ranta tana fadin ' walahi sai kin kawo kanki da kanki in dai soyaya ce, idan ta barki kika gama haukan boyen zata falasaki ne, mu dai je zuwa ni da ke ma ga mai taurin kai' a bayane kuma sai ta ce" kin ga inace cewa aka yi du mu je mu yi sallah mu sakata a adu'a ba zaki wani tsayar da mu a nan muna maganar da ba ita ba?, Yo in ba abinki ba Muneerath dan kawai tsakanin ya zamo haka to ko Mah ta haifeta ta zo gidan da ita ai akoy soyaya tsakaninsu bale kin manta yar riko ce ita din? Yo kema Pah din da Mah din ai iyayenki ne, yanzun idan aka ce kece budurwarsa sai ace ba kyau?"
Zuwa yanzu so take kawai su yi balaki da Saudat, Allah ma kuwa haka zuciyarta ke fada mata Saudat ba mai kaunarta bace sam, to me yasa zata ringa neman fada da ita? A kan me zata tsaya gata ga ita tana son rikita mata magangannu? Me yasa ba zata bar maganar a yadda ita ta barta ba?
Tana shirin yin magana ta ga mota bak'a na karasowa sojoji na gudu da kafafuwansu haka droon na yawo a saman kan motar, hakan na shedar Hanja na cikin motar
Gabanta ne ya yanke ya fadin mata a lokacin da suka yi ido hudu da shi ya kureta da duba , duban da ba zata ce na meye ba sam
A hankali ta samu kanta da sakar masa harara mai zafi cike da jin haushinsa, wai shi dama gaba daya a nan ya tile? Soyaya da Iman , lallema
Bakinta ta murguda bata iya tsayawa ta ga fitowarsa ba, hasalima bata kula da Pah suke tare ba, shi kadai idannuwanta suka nuna mata ta juya rai bace ta shige ciki tana hada matatakalar ko kula cewar akoy wasu hakimtatum mataye larabawa a dayan falon na kusa da baban falon gidan bata yi ba ta shige lft ta danna tana ta cika tana batsewa
Oga da matarsa da suke zaune suma a falon gefen matayen nan da sam basa jin wani yare face larabci da turanci shi yasa ake zaman kurame dan kowa na son kauce zargin kar wani ya yi tunanin yine ake yi da shi ya kalli Matarsa a hankali ya ce" Kuma yanzu komawa zamu yi hala? Tunda an ce da sauki ko?"
Kallonsa ta yi, irin kallon nan na tsarewa da ido hakan ya saka shi shima kureta da duba, ba irin duban nan na balaki ba, ba kuma irin duba na raini ba, wani duba ne ya mata wanda duda jan idannuwansa sai da ta ga rauninsu
A hankali ta sada kanta muryarta sanyaye ta ce" Nima ban sani ba, yar ogan ce tunda ta bace mana ban ganta ba sai dazun nan a hanya ita da kawarta, ni kam abin na yar oga ya fara bani tsoro, ban san yaushe ta zama haka ba"
Oga ya karra kallonta yana son gane wai ta kula ko da wa kuwa take magana har ta masa a sanyaye haka? Rabonsa da gannin ta masa magana a sanyaye tunda ta dawo hayacinta
Yana shirin yi mata tambayar wani tafkeken soja ya shigo ya tsaya muryarsa sama sama ya shaida shigowar sarkin da Yaransa hakan ya sa larabawan nan mikewa gaba dayansu du suka daidaita hannayensu suka sada dubansu
A hankali Oga ya ce" Toh fah me hakan ke nufi kuma?"
Mamansu Muneerath da bata gane ba itama ta ga shigowar HANJA
A hankali ta karra kallonsa da kyau cike da mamakin yannayinsa
A yanzu jikinsa sanye ne da wandon suit din kadai sai riga ruwan toka mai duhu wace ta dan rike shi daga sama har zuwa kasa kasa kusa da abdo din da ya ninninke ya nuna kansa wajen cikinsa
Hannayensa dake da kauri wajen damatsunnan da jijiya birde birde da irin yadda kasa kasa wajen jimkaken hannun ya nuna kakarfan jiki irin nasa, har zuwa baki sidik din gashin kansa da yake caje gaba gaba ne kadai ya nuna ya dan fara hargitsewa kadan irin cajewar da akai masa ta fara hadewa kadan , har zuwa idannuwansa da jajayen lebunnansa
Da sauri ta cire dubanta a kansa gannin bayan ya gaba gaisar da larabawan nan da yaren larabci radau a bakinsa kamar wajensu ne ya juyo, gabanta na faduwa cike da tsoron me ya kai Muneerath jikin dan sarkin kasar nan?
Pah da ya gama amsawa mutane masu tambayar jikin matarsa yan uwanta na kusa sosai da suka fantsamo dan gannin jikinta da kulawa ya shigo shima ciki wajen Yayar matarsa, da mahaifiyarta, da kuma dayar matar mahaifinta marigayi sarkin Makkah
Cike da mutuntawa ya gaishe su, kafin a nutse ya basu bayanin komai bayan sun yi gaisuwa irin ta larabawan nan
Oga da yake kallon komai sai ya samu kansa da fadin" Nana, inaga wannan runguma da aka yiwa Muneerath ba komai bace, tunda dai kin ga da farko da shi wannan katon ya rungume mutanen nan jira nake ace su dinma yan matan nasa ne? Dan kuwa kin ga su Idan sunna soyaya ba ruwansu da shekaru, sai kuma ga ubansa ma ya aikata, garin nan so suke au karar min da man kaina kaf, walahi so auke du hargitsa min tunanina ta hanyar nunan idan iskanci nake ji su a rubuce suka shanye shi, kin ga mu yake nunowa uban kardai muma su rungume mun mun shiga uku"
Harare ta so sakar masa, sai dai gannin sun nufo su har matan ya sakata mikewa tsaye tana jan lulubinta da tunane tunanen ta yaya zasu gane yaren junna? Ko dai ba'a zama a nan suka zauna?
A mutunce Pah ya fara magana, ga mamakinta sai ta ji Freinch radau a harshen Hanja a lokacin da Pah ya shiga gabatar da su yana dan murmushi kan cewa iyayen yarinyar da suka dauko ne a africa wace Aleesa ta daukota , tana son yarinyar sosai
Sannan ya gabatar masu da matayen suma yana murmushin inda Mamansu su Muneerath ke kara fasarawa Oga wanda freinch din nasa sama sama ne ba wai ya kware bane
Pah ya yi wani murmushin yana fadin" Yarinyar itace yaronku ya haikace a kanta"
Wannan kam sai Hanja ya samu kansa da kasa fasarcewa su mama dukda ya kula fasarar suke jira sai kawai ya dan sosa keyarsa ya dan juya a hankali ya nufi hanyar ficewa yana ayana' Ai fa na shiga uku tunda na ba Pah amanar haka ne, sai ya kuncen wando a ko'ina'
11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 95 · 0% Book details