Sashe 85
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kuka mai zafin gaske tana dora kanta a gefen kafadar Saudat har tana jijiga gaba dayanta dan abin daga kasan zuciyarta yake fitowa, daga cen kasan zuciyarta take jin wuyar abinda ke damun nata wanda take jin yana sakinta a hankali a hankali Karar bude Kofar ya saka su yin tsit da sauri Muneerath ta dago kanta Ido hudu suka kuma yi da mahaifiyarta dake dauke da wata babar jaka shake da dinkunnan atampopi da ta ringa dinkawa Muneerath din a lokacin da bata nan Cire dubanta ta yi a kansa ta karasa kuda da gadon Muneerath din ta yaye shinfidar sama domin ta yi dati sosai ta juyo wajensu muryarta a dan dake ta ce" Ku tashi ku yi wanka ku dauro alwallah ku gabatar da sallar la'asar kafin lokacinta ya shige, idan kun gama ku fito dakina ga abinci ku ci, so nake kuna gama cin abinci ku gyara dakin nan sosai ku wanke bayin ku cenza katifar Abdul ya tafi ya siyo sabuwa sai ku cenza wadinnan wandunnan dake jikinku ga atampa nan ku saka maza mu je saloon a maku kitso, kar na dawo na tarar da ku zaune a nan" Tana gama fada ta juya ta fice inda Muneerath ta bita da kallo cike da wani mamakin da ya kusa kasheta da farin ciki marar musaltuwa har sai da saudat ta ce" Kin ga tashi wollah kar ta dawo ranta ya baci kina zaune uwa sakarai".................................... RAYUWA KENNAN BAYAN KWANA SHIDA KASAR INGILA A tsakanin kwanakin nan sun gabatar da rayuwa cikin wani yannayin da basu saba ba sam Yaronsu dake gefensu ya zama gashi a cikin gidan aman kuma tamkar baya nan A tsakanin kwanakin nan ya yi tafia sau uku wace yake yin zuwa da dawowa bai kwana ko daya ba HANJA na acting tamkar ba abinda yake damunsa sakamakon abinda mahaifinsa ya yi masa, sai dai abinda bai sani ba bai taba gabatar da rayuwar nesanta kansa da su ba irin wannan Mah ta yi nacin bin, ta yi nacin kiran, ta yi fadan da tambayar shin lafiyarsa?, Sai dai a kulun amsar daya ce abubuwa sun sha kansa bashi da time Yakan kwatanta yin hira da Tgr sai ya samu kansa da mamakin kansa da tunanin to amsa zara bashi ko me? Sau biyu yana yarda da haduwarsa da yar gidan minista sai dai abin takaicin yarinyar sam bata da ra'ayi nata na kanta, ko zance suke abinda ya gabatar shine gaskiya koda da gangan ya gwada nuna mata akasin tunaninta takan zubar da nata tunanin ta dauki nasa, a haka ya nuna mata yana da butakar kwonciya da ita abin mamakin ita ta kama masu waje ta gyara komai sannan ta ringa zumudin irga lokacin da ya rage ya kwonta da ita Wannan lamarin ya daure masa kai, sai kawai ya girgiza kai yana saka nimbobinta a black list yana jin takaicinta tare da tuna yarinyar da koda wasa ya nemi taba mata hannu ko a cikin malagigin wuya na tsoro take in dai hankalinta na jikinta sai ta bige masa hannunsa tana jaraba Kai koda da gangan take yi hakan na birge shi, hakan na nufin ba zata iya gagawar yarda da namiji ba koda kuwa saurayinta ne Aman ita gashi soyayar bai rigaya ya furta mata ba, yana dan kulata ne yana auna magangannun soyayarta da take nuna masa aman a haka ya nuna mata zai kai keyarta kasa ya yi wasan kura a jikinta ta aminta harma take zumudi? Walahi sai KYANKYAMIN HALAYA IRIN NA MAZINATA ya darsu a zuciyarsa, watau su basa kyamar wutsiyar kowa kuma basa auna da wa zasu kasance da irin lokacin da ya kama a gabatar da abin? Burinsu a taba su kadan su bude sket kowani kazami ya danna kansa a ciki? Su basu da fid ? Kowama nasu ne, a kan yan kudade sai su yi, haka kuma a kyauta sai su yi? A yanzu da yake zaune saman bed dinsa karfe bakwai ne na dare yana kallon waje daya ba tare da ya san wa yake kallo ba Tunani ya yi masa yawa, ya kasance mai yawan tunanin abinda bai san dalilinsa ba A hankali ya dauki katuwar wayarsa ya shiga wajen vidio dan ya yi kallo ko zai samu abinda zai dauke masa damuwarsa duda shi din ba mutun bane mai son yawan kalle kalle Vidio din da ake ta turo masa sunna bude kansu ta whatsup ya shiga bi daya bayan daya wa'inda ba wani mahinmanci sai kawai ya goge A haka har ya sauka kan vidion birthday dinsa da Mah ta yiwa su Muneerath ta tura masa A hankali yake kallon abinda suka yi, wani lalausan murmushi ya samu damar sauka a kan lalausan lebensa a lokacin da suke dirkar rawa , inda rawar ta fi yawa a kanta Wajen da ta kykyace da dariyatana shafawa sauda crem ya samu kansa da maidowa koda ya wuce A hankali ya ringa murmushin shima yana dafe daidai zuciyarsa Idannuwansa ya lumshe yana tunanin idan bai ganta suka yi rigima ba ba zai iya rintsawa ba Zai iya rantsewa bai taba jin missng din mutun irin yadda yake missing din yarinyar nan Ba shi kadai ba har a wajen aikinsa sunna missing din yarinyar bale a nan gidansu Da murmushi ya yi a bayane ya ce" kanwar da nake son samu ce ta fito min daga africa, me take yi? A ina take kwonci? Me take ci? Da wa take hira?, Ya zama wajibi na saka a sakata cikin masu tahowa zuwa indonesia" A hankali ya mike daga zaunen da yake da wayarsa ya fito Yana saukowa ya hango su zaune saman diner, a kan dole ya nufe su domin sun rigaya sun ganshi Da kallon kula suke binsa har ya zauna a gefensu Fuskarsa ba fara'a a yanzunma haka kuma da Mah ta gabatar masa da abinci sai ya nuna a koshe yake Pah da yannayin taurin kan yaron nasa ke damunsa tamkar wani DUTSE yana jin duka ya ki ya rugurguje ne ya ce" Dazun mun yi vidio call da Muneerath" Da sauri ya dago da dubansa, cikin gagawar magana ya samu kansa da fadin" yaya take, a ina take, me take, su waye suke tsaronta, tare da su wa take, Attahir dai yana kasar nan shin yana damunta da kira ko?............." Sai kuma ya yi zuru zuru yana kallonsu , sai da ya gama magangannun ya ringa aunawa a ma'auni Jikinsa a mace, idannuwansa sun dauki launin ja ya samu kansa da furta" NA SHIGA UKU" *SAKO ZUWA GAREKU MAKARANTAN DUTSE, IN SHA ALLAH POSTING ZAI DAWO SAU BIYU A SATI, WATAU LITININ DA ALHAMIS SAKAMAKON NOVEL DINA NA KUDI MAI SUNNA WATA KOKOWAR DA ZAN FARA POSTING RANAR LITININ IDAN ALLAH YA AMINCE, NA GODE SOSAI DA KULAWA.....DOMIN SAMUN NAKI KO NAKA KA TUNTUBENI A NUMBER WAYATA KAMAR HAKA +22793811618, A FARASHI MAI SAUKI NAIRA DARI BIYU 200...... IN SHA ALLAH ZAKA SAMU NISHADI DOMIN SALON NA DABAN NE* DAGA YAR MUTAN NIGER sajida 11/14/21, 12:53 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*