Sashe 102
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
amsa Saudat da ta fito da gudu da hijab ta karaso a hannunta tana mika mata cike da wani irin farin ciki marar misaltuwa Muneerath ta amsa ta bude ta saka tana riko hannun saudat kasa kasa ta ce" Tafi da ni, me ya kawo shi garinmu? Saudat tafi da ji ina jin ciwon nawa na neman tashi zuciyata ta fara kusanto bakina kaini fakina dan Allah na sha magani kin ji?" A hankali ya kara matsawa yana nuno mata Flowers din hannunsa da suka dan fara langwabewa saboda zafin garin yana kallonta a gabanta Flower din ta kalla ta kale shi, a sanyaye ta ce" Hanja shukar nan fa ta menene? Ni kamar baka da lafia dan Allah meye ne? Wayo Ogana zuciyata zata ballo dan Allah mu je ciki kin ji Saudat?" Saudat ta girgiza mata kai tana kallonta ta ce" Muneerath ba inda zamu je, ki saurare shi dan Allah" Muneerath ta warce hannunta cikin fada fada ta ce" Ba zan saurare shin ba, na ki na saurare shin na ce! Na tsane shi, na tsani halayansa, me yasa zan saurari mutumen da bashi da aiki sai aikata zina? Watau du matan da yake zuwarma ya auna masu ciki ko? Ba abinda zan saurara da mai hali irin nasa, gashi daga jiya zuwa yau ji nake kamar kiris ya rage na babale na mutu ba" Juyawa ta yi da niyar tafia da sauri ya damko hannunta ya juyota da karfi gabansa hakan ya sa Oga zarro ido ya shiga nufo su da gagawa yana fadin" Mun shiga uku za'a maimaita a anguwa a samu na gorantawa y'ata na ci uban mutun, ke , ke Yar oga dan ubanki ba ya biyo ki ba, meye kuma kin yafe a wuce wajen mu je na bashi duniya da kiyama a daura ku tafi ni bana son bidi'ar komai, shima dama mamansa a kwonce kawai a daura mu je ciki mu je ba sai ya rungumeki a nan ba, shin kina ga yan leke ta katanga kuwa ?" Damatsunnnan hannayenta ya rike gaba daya ya jijigata da dan karfi yana kallonta muryarsa a rikice ya ce" Kirani da dan iska, ki kireni da komai kike so, ban ki ba na aikata, kuma na yi dana sani!, Aman ba zan iya da nauyin DUTSE irin na soyaya ba, lalle soyaya itace DUTSE, bata jin rarashi, bata jin ban baki, bata jin kunya bata da kawaici sai ta halakani zata huta? Munarah I LOVE YOU.......I LOVE YOU MUNARAH" Lebunnansa take kallo, furucinsa na sauka a cikin kirjinta A hankali ta shiga neman numfashinta aman yana neman gagararta, Gaba dayanta ta ringa son kwatar ganninta dan ta karra kallon fuskarsa da jin kanshin turarensa a hancinta Lokaci daya jikinta ya saki dubanta ya rufe komai nata ya tsaya cak ya kasance ta yo gaba ta fada a jikin kirjin HANJA, watau sun aikata abinda Oga yake gudu rungume a tsakiyar titin garin malan bahaushe Sumewa ta yi Muneerath ta sume Yar oga ta tafi Yaya kuka gani?????? I'm sorry wani sa'in gaskiya na kudin kan daukan hankalina Domin samun naki ki tumtubeni ta number wayana kamar haka +22793811618 a kan farashi mai sauki in sha Allah 11/14/21, 12:54 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*