← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 114

Sashe 43

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
2
Shafawa ta shafa cikin nutsuwa ta warware gashin kanta a hankali ta shiga binsa da kumb tana caje shi
Sai da ta gama caje shi ta dauki ribom zata saka Mah ta shigo hakan ya sa ta gaisheta bayan ta rage tsayinta sosai
Wannan gaisuwa a kulun itama mah din sai ta birgeta, ta kula irin nasu ladabin ba'a gaishe da baba a tsaye kikam, hakan sai ya birgeta sosai ita kuwa sai ta matso ta yi mata irin nasu na larabawa watau ta rungumeta
Ribom din ta amsa ta nuna mata wajen zama, hakan ya saka Muneerath zuwa ta zauna ta dan hade jikinta tana jiran gannin abinda zai faru
Ai kam Mah ta hade gashinta ta kame mata shi a tsakiya sannan ta tufke mata shi simple ba da wata kwaliya ba ta nade mata shi a kanta
Kwali ta ciro sabo ta fitar da shi tana kallonta ta ciro tsinken ta kamata ta zira mata shi
Ai kam ido ya kama ruwa ya ki ya bude sai rawa yake da kyar ta daina murzarsa Mah na mata daria har ta daina jin mugun zafin sannan ta saka tissu du ta goge mata bakin kwalin kafin ta umarceta kan ta saka suturar ta ma'aikatarta
Sai da kwallah ta zubo mata a lokacin da ta saka wando kalar fari da dan sket a samansa ta saka rigar ta saka safa ta saka takalmin kafa ciki mai dan karamin tsini sannan ta kalli madubi
Mah ta juyo tana murmushi ta dauki dan abin na wuya ta zagaya ta daura mata shi sannan ta dauki dan karamin fari kal din dan kwalin ta nade mata gashin kanta da shi
Murmushi ta yi mata a hankali ta ce" Masha Allah "
Muneerath ta kalli Mah sai kawai ta fashe da kuka ta dora kanta a saman kirjinta tana yi , ita kuwa Mah na dan tapping din bayanta sai da ta yi ta more sannan ta dago da dubanta tana kallon Mah
Mah ta ce" Ki ce Alhamdulilah"
Munnerath ta gyada kai a hankali ta ce" Alhamdulilh "
Mah ta ja hannunta kusa da bed ta zaunar da ita, itama ta zauna kafin ta ce" Muneerath, a kowace ma'aikata akoy bata gari, akoy na kirki, a cikin manyanku akoy wa'inda sunna nan ne dan su lalata rayuwar yayan mutane ba tare da jin komai ba, basu da haram fa, Muneerath basu da haram domin sunna iya nuna maki soyaya ce suke maki sunna sonki ne zaku yi soyaya ne dan su samu ku yi kyakyawan karshe irin na aure , aman kuma abin takaici karya suke,karya suke yi maki Muneerath ba abinda suke so sai su cinma abinda ke boye a cikin pant dinki, baban burinsu su mayar da ke karamar karuwarsu wace idan sun zo office gaki a kusa sunna iya zubar maki da datin su, Muneerath baban abin takaicin ba dagake zasu tsaya ba domin ba a kanki suka fara ba, kema zaki zamo ne hanyar da zasu hau su bi cikin garaje da iko ba tare da sun biya ko sisin dalarsu ba..............."
Ta kamo hannayenta ta rike ta ce" Hakan na saka mu iyaye a cikin zulumi da tashin hankali, da ace zamu iya hanna aikin da mun hanna harta mazan fita nema........., Sai dai hakan ba zai yiwu ba dan kuwa a yau ilimi anfani ne da shi koda na iya zama da mutane ne,"
Habarta ta kama ta dan dago da dubanta ta ce" Muneerath, zaki hadu da mutane kala daban daban a aikin ki, zaki hadu da na kirki da na banza, aikin ki na iya sakawa ki kwana a wata kasar, wani sa'in kina iya yin kwana biyar ko sama da haka, kin ga idan ke din mai sake ce komai zai iya faruwa da ke................"
Hannayen nata ta kuma jimkewa sosai tana kallonta ta ce" sai dai ina so ki kasance wace ta san ciwon kanta first, ki ringa tunanin cewa idan har kika yarda aka lalata maki rayuwa da farkon fari kanki kika yiwa, Muneerath kanki kika fara wulakantawa, rayuwarki kika tozarta , Muneerath zai bi har yayanki, zai bi gaba daya ahalinki har jikokin jikokinki domin daraja na shafar iyali,.......... sannan idan namijin nan ne kika biya ya rude ki ki sani alherin dake tare dake yake yiwa zai gama da shi ya kuma damki na wata kina ji kina gani namijin da ya gama sukuwa a kanki yana murmushi gaisuwar kirki zata gagare ku domin zai dawo kyamatarki ke ya ga damar ya zageki da ke din mazinaciya ce yar iska ce bayan shi ne ya iskantar da ke, harma zaki kula da kunya yake a ga yana maki magana.......wannan shine shari irin na mugun aikin nan, ya fi bibiyar rayuwar ya mace Muneerath, sannan sai ki tuna wanda ya halice ki, shin a rayuwar da ya baki, da lafia, da hankali, da wadata ya cencenci ki saka masa ta haka? Shin idan kina da bukatar namiji ba aure ya fi cencenta ki yi ba?, Idan kuwa wani abin duniyar ne akoy wanda ya isa ya baki ba tare da gori ba bayan shi? Kin roke shi bai baki bane? Ko bakya iya rokarsa ne?......idan kika mutu me zaki ce da shi? Idan bakya jin kunyar kowa ki ji tasa!,
Sai kuma iyayenki, Muneerath sunna da haki a kanki, shin kina so ki yi abinda Allah zai kama su da shi sannan duniya ta yi ala wadai da su?, Daga su a gangaro kan wa'inda suka amshi amanar horar da ke aikin nan....har zuwa kaina da na amshe ki kike hannuna, Mubeerath muma muna rokon ki da ki rufawa kanki asiri ki kame mutuncin kanki na y'a mace ki yi aikin ki domin Allah domin aiki kika je yi a duniyar jirgi ba yawon ta zubar ba, Muneerath aiki kika tafi yi ba wulakanta kai na, Muneerath burinki muka baki damar cikawa ba banzatar da kai ba, domin ke din mutun ce mai daraja, mace kike uwar al'umah, wace muke so muke fatan gannin mun wanketa cikin salama mun mikata da dumbin daraja Muneerath ki ji tausayin ahalinki, ki tausayawa marikanki ki taya mijin da zai aure ki kishin kanki, ki kare mutuncin y'ayanki kin ji?"
Hawaye ne masu dumin gaske masu tafe da dumbin kauna da bege da madaukakin gannin girma da darajar Mah suka gama wanke fuskarta, bakinta ya mata nauyi ta kasa furta komai, bata taba jinta a matsayin mutun cikakiya ba irin na yau, yau gata itama mutun ce ana mata nasiha irin wannan mai daraja da girma? Ashe dama haka mu'amala take tsakanin datijan kwarai da yara? Ashe ana yiwa mutun fadan ya gyara kayansa?
Ta kasa cire dubanta a kan Mah a lokacin da suka fito kusa da Katon Falon Pah bayan sun masa salama ya gama tsokanarta sannan ya dora mata da tasa nasihar suka rakota harda iman kusa da wuleliyar limozine din dake dauke da direba da soja daya za'a kaita wajen aikinta ita MUNEERATH YAR OGA sai kawai ta samu kanta ta sumbatar bayan hannun Mah kafin a sanyaye ta ce" NA GODE"
Wannan kalma ita kadai ce ta fara fito mata daga bakinta domin ita ce ta fi cencenta da ta furta a wannan lokacin, ta tabata sai ta zauna zata iya gane a wani hali take ciki hakan ya sa ta shige bayan motar da aka bude mata ta zauna ta limshe idannuwanta suka harba hanya zasu sadata da baban a
roport din da OGA HANJA ke janye da ragamomi masi yawa a ciki harda tukin da zai yi na yau dan zuwa kasar malesia
Malamai to wai ba'a hutu hala
11/14/21, 12:49 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 43 · 0% Book details