Sashe 39
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ba aman an tiso ni da bindiga an tare min hanya bayan an gama cin kaniyata, wayo na shiga ukunna garin nacin son zama Hostess zan zama gawa a garin arnawan da basa sallah bale au salaceni au kilaceni irin na musulmai, wayo ni wayo Allahna ni ta dogari yau kuma a nan na tsinci kaina? " Hannayenta ta dora saman kanta sosai ta langwabar da kan ta dora da fadin" du wannan wulakancin kaine sanadi, dogari da ka nuna kana ra'ayina da na wuce wulakancin kowani namiji, aman sai ka tashi ka saka kafa ka haure ni ka kasa tunkaro ni ka kasa nuna min so, haka nake hakuri ina kallonka dan ba zan yi irin na yayata ba na nunawa namiji so ya dawo yana wulakanta ni ba, aman ba komai na tabata adu'a nake watarana zaka dube ni, idan kuma ka dube ni wannan garjejen sai ya yi dana sannin sanina, dan daraja ce da ni, ni ba kanwar lasa bace!" Daga inda yake zaune gaban computer dukan bayananta yana ta saurare ne ba tare da yana gane yarenta ba, daga kasa kuwa dankareriya zakanyarsa ce ke kai kawo tana kada bindinta irin yau a farin ciki take ga wanda ya ajiyeta ya dawo daga yawace yawacensa Da sauri ya shiga dadana computern nasa yana ta aikin neman yarikan kasar Niger Nana da nan aka gabatar masa da yarika na kasar niger kwaya takwas daidai HAUSA ZABARMANCI FILATANCI BUZANCI TUBANCI BARBARCI GURMANCI Larabci A nutse ya ci gaba da aikinsa ya nemi translate app na yare kala daban daban Kasancewar duniya ta ci gaba, abubuwan ci gaba na duniya sun rigaya sun cika duniya, ya sa a zaune da yake a saukake ya samu mai amon murya cikin kwarewa da iya aiki da computer da bincike bincike ya saka wannan yare nata a layin translate na yarukan nan banda larabci domin ya tabata ba shine take yi ba kafin ya mike ya nufi ciki dan ya samu ya yi wanka ya dan taba wani abin Hankali kwonce ya yi dukan abinda ya saba ga zakin nan du inda ya bi yana biye da shi haka kuma yana mata hira yana dan murmushi itama takan dira ta ringa markayarsa tamkar ta samu jikin dan uwanta zaki, shi'q hankali kwonce ba da tsoro ba yake biye mata har ya cenza kayan nan zuwa sweet maau ruwan Ash ya daure da nekti mai ruwan blue da baki baki ya saka bakar safa da bakin takalmi ya caje gashin kansa ya saka bindigarsa yana aikin mika ta ainahin abinda yake missing wanda rabonsa da mace a kadan ya dauki wata biyu sakamakon irin tafiar da suke yi shi da iyayensa inda mamansa ke mugun saka masa ido da nasihohi kala daban daban Tsayawa ya yi yana daura agogo ya saki murmushi gannin zakanyarsa ta nufi wajen kofar fita tana kai kawo kafin ya girgiza kansa a ransa yana ayana 'wai dabama ta san ra'ayin kanta' Tsayawa ya yi facing din tankamemen madubin falonsa haka kawai ya zo wucewa ta wajen A hankali ya dan gyara gashin kan nasa kafin ya lumshe idannuwansa ya saki dan murmushi a fili ya furta" Aure zan je nema" Sai kuma ya dan daga kafada ya nufi wajen computern dan ya tabata zuwa yanzun dukan bayanan da ya dace ace ta yi ta kwatanta zai saurara ya ji yanda ya kamaya yi da ita, ya gama mata shirinta ne idan har dan ta cuci mamansa ne ta biyo su a yau a nan zai harbeta kowama ya huta, idan ya so ya turawa kasarta labarin ta mace, in kuwa bai ga haka ba dole zai kaiwa Mah ita a yau, daga baya ya ci gaba da bin dukan motsinta dan shi sam baya da saurin yarda da kowa a duniya! Kasakai ya yi da baki yana sauraron shirmen da computer ke fadi a lokacin da ya dana ta karanta masa abinda ake fada, sai dai bata fasara sunnan dogari ba, hakan ya sa ya dafe goshinsa cike da jin haushin bata lokacinsa ya nufi waje da zakanyarsa yana furta "Yanzu haka bata da hankali ganewa ne ba'a yi ba" Ido ta kwalalo gaba daya a lokacin da taga yadda zakanyar nan ke ta makalkalarsa tana juyi a jikinsa Idasa sauka ta yi kasa tana rike fitsarin daya gama fara fitowa a mararta tana zarar ido ta ce" shikenan zaki ne ajalina............ 11/14/21, 12:48 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*