← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 114

Sashe 66

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4 Ci gaba da magana Mah ta yi wanda shi kuma ya yi shiru yana sauraronta gaba daya bakinsa ya masa nauyi yana tunanin anya zai iya dogon bayanin a yanzu kuwa? Muneerath kam idannuwanta a kan kwalin Pizzar nan da ta kula biyu ne da kuma kwalba dake dauke da jus irin na yan gayun nan A hankali ta kuma satar kallonsa, ta riga ta gama tsara cewar tana zuwa gida zata fadawa Mah abubuwan da suka faru a nan, idan ya so sai a san abin yi domin bata so ko daya a ga laifinta, sannan a gaskiya tana komawa zata nemi da a maida ita gida wajen nata iyayen ya isa hakanan yawon taburadar! A hankaki ta mike ta karasa kusa da kwalin Sai da ta kuma satar kallonsa kafin kasa kasa ta ce" Kai yinwa nake ji, shi kuma sai waya yake kamar tsohuwar karuwa yana lumshe ido, gaskiya ci zan yi ina dalili mun fito dan mu yi ciye ciyenmu ka kawoni nan kuma ka manta cewar mutun ce ni" Kwali daya ta dauka tana ta adu'ar Allah ya sa ta kaza ce, ba ta alade ba! Ai kam sai da ta idasa dubawa ta gane ta kaza ce sannan tana fara dandanawa ta ji dandanon kaza sai ta saki murmushi ta dauko ta zauna ta shiga ci tana tunanin ta wannan kampanin ba dai dadi ba Da idannuwansa yake binta da kallo, baya jin abinda take fadi idan ta yi hausarta a nan, a gida ne du ya saka abinda zai kai masa sakon kalamanta ya fasarce masa a lokacin da yake mata kallon terrorist, wanda ya yi niyar sunna komawa zai cicire dan a yanzun ya gane cewar ba terrorist bace, haka kuma ba ta makale masu bane dan ta ci dukiya ko wani abin ba, ya gane cewa hukunci ne na ubangiji kasancewarta tare da su a irin wannan lokaci, sai dai kuma dayan abin yana da tantama a kan kwakwaluwarta Irin yadda take kara gyara zamanta tana daukowa tana ci ya sak shi shagala da kallonta, kafin a hankali ya ce" I'm seek Mah " Mah dake ta jero tambayoyi kan ina yarinyar mutane, me ya sameta, menene wannan hotunnan da yanzu Iman ta kawo mata tana kuka? Me ya kai hannunsa nan dinta a waje public ? Me ya sameta? Tana ina? Ta ji amsarsa cewar bashi da lafia sai ta samu kanta da sasauta muryarta a hankali ta ce" Kana clinik ne? Me yake damunka son?" HANJA ya sauke ajiyar zuciya a hankaki ya ce" ina gidana, kuma gatanan" Mah ta kai zaune saman kujera a sanyayenta ta ce" Kana nufin kana tare da Muneerath ? Dan bani ita mana dan Allah?" Idannuwansa ya kuma saukewa a kan Muneerath , a hankali ya nuno mata wayar kafin idannuwansa cikin nata ya yi gyaran murya a lokacin da ta dago dubanta tana kallonsa a saman lebunnansa ya ce" Mah " Muneerath ta taso da sauri tana kallon bakin nasa a ranta tana ayanna 'To ko dai wani ya dakar masa leben ne?' Amsa kiran ta yi da sauri a tsaye a kansa kafin kuma lokaci daya ta shiga kai kawo , sai kuma ta ja ta tsaya tanarike da kugu da hannunta daya idan Mah na magana daga Mah ta yi shiru sai ta ciro hannun nata ta shiga bata amsa tana kai kawo tana nunawa da hannunta yadda ka san tana gabatar da wani shiri hankalinta kwonce tana kara nunuwana da hannayanta shi kuma yana biye da ita da ido yana hasko dukan abinda take fadi da irin yadda ya faru da irin nunin da take kamar Mah din na kusa da ita kafin ta kare maganarta da fadin". A gaskiya ni dai ban san ko me yake damunsa ba, idannuwansa dai kamar ya sha kuka , aman kuma bakinsa kamar yana masa ciwo dan dazun dai yana dan magana yanzu kuma ta dauke dif, sai kuma kamar ransa a bace yake, to dai abin nasa ni dai Allah ya sa kar ya motsa ina kusa, a yanzun dai da dama fushin ne ke dan nuna kansa aman Mah abinda na fada maki kaf iya gaskiyar kennan na jiyan nan kadai na san na tsero wajensa kuma ashema ba samansa na fada ba dan na farka na ganni saman kujera, na yau din nan ne kawai na kula cewar kamar bayan ya taban gefen kafada sai ni kuma na rike shi dan ya ceceni daga zakin ashema zakin na wasa ne?" Mah ta ringa sauke ajiyar zuciya tana ta adu'a a kasan zuciyarta kafin ta ce" Yarinyata kina ji?, Ki kula kin ji ko? Ki karra rike mutuncin kanki, idan ya kara tabaki ne abin zai iya tabatuwa kin ji ko? Dan Allah ki kiyaye sallah a kan lokaci, sannandaga an yi ki fada masa ya yin shima kin ji? Kuma yanzu ki sa ya nemi likita dan bashi da lafia kin ji?" Muneerath ta amsata kafin ta maida masa wayarsa ta kuma tsaya tana jira ya kare Sai da Mah ta idasa maganarta yana sauraronta a hankali ya amsa mata kafin ya kashe kiran ya daga dubansa a kan Mubeerath da ta ce" Yauwa Mah ta ce ka ga likita baka da kafia, kuma dai ka tashi ka yi sallah nima bara na gama cin nawa abincin sai ka nunan bayi " Zuwa yanzu lamarinta ya daina bashi mamaki, sai dai dam baya tunanin zai daina binta da kallo dan ya gane ita din wace irin halita ce? Yana nan zaune ta gama, ta miko masa jus din ta ja ta tsaya ya bude ya mika mata yana kallonta ta koma gefe ta saka bakin dan kwalinta wai kar ta hada baki ta sha iya shanta domin bashi da gaz haka kuma bashi da karfi sai ta ji dadinsa a bakinta sannan ta ajiye masa a kusa da shi tana fadin" ga naka " Shi da da ido ya kuma rakata har ta nufi bayi sannan ya mike yana tafe a hankali ya nufi wajen da wrdrb dinsa yake ya buda yana bin kayan da kallo dan ya dan jima rabonsa da garin Sai da ya yi adu'a sannan ya dauko wasu tufafin ya ja ya tsaya har sai da ta gama ta fito Bai kulata ba , aman kuma ya ajiye mata abin sallah ya nufi bayin Da ido ta bishi kafin ta gyara ta tada sallarta Tana saman salaya kanta sade ta gama sallar aman kuma tana ta istigfari ya fito ya fita a falon daa sauri ta bishi da kallo ta waiwaiga cikin dakin kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da adu'arta A fitar Hanja wajen motarsa ya nufa ya ciro salaya Sai da ya gabatar da sallarsa cikin nutsuwa kafin ya ninke salayar ya shige motar ya nufi kampanin da jirgin nan yake A lokacin da ya karasa aiki ya hau tukuru sannan a tsanake , hakan ya sakashi cire du wani tunanin dake damunsa, ba shi ya gama ba sai cen kusan jarfe biyun dare Daga nanma hotel din nan ya wuce ya je ya dauko abubuwansa da basu da yawa sannan ya bude nata dakin Bin dakin yake da kallo a nan dai ya dan bata lokaci domin sai da ya shiga bayi ya ga kayanta na uniform da ta wanke ta shanya a bayin, ya hado brush dinta da soson wankanta kafin ya fito ya dauki jakarta ta baya ya shiga ninke kayan yana sakawa a cikin jakar har ya zo kan pant dinta Da sauri ya dan zarro ido sai kuma ya girgiza kansa yana yatsine fuska tamkar ya ga abin kyankyami ya cusa mata shi a jakar ya zuge zif din sannan ya cire wayarta da cazarta ya nufi kofa yana dadana wayarsa ya tura kira a lokacin da ya zauna cikin motarsa A kausashe ya furta kalmomi kamar haka" tashin safe zamu yi" Daga haka ya kashe wayarsa baima gama jin ok sir din Sir baya tada motar ya nufi gidan a ransa yana fadin'Na san yanzun ta yi summa goma, yarinyar sam ba hankali a tare da ita' A lokacin da ya karaso har karfe uku ta gota A hankaki ya idasa shiga falon da yake ciki daya ne kwal sai bayi sai wajen tufafi, akoy gado aman idan ba sani ka yi ba ba zata taba sannin akoyshi ba domin a cikin bangon yake A hankaki yake takawa ba tare da ya cire takalminsa ba har ya idasa kusa da cafet din dake ahinfide fari kal Ido ya tsura mata, irin kwonciyar da ta yi da dan nadewar da ta yi A yanzu dan kwalin baya jikinta haka kuma gashin kanta ta cire ribom din jiki, a kusa da ita kuma dayar pizzar ce ta bude ta ci iya cinta ta bar sauran a nan, sai jus din da ta kara ta ajiye sauran A hankali ya duka kusa da ita ya kai hannunsa gefen wuyanta ya taba Hannun nasa ya dago yana mai karra binta da kallo, abu daya ke masa yawo a ransa.....shin bata da lafia ne? Me yasa du sanyin garuruwan nan ita kulun jikinta da dumi? Bata da lafia ne? Aman idan bata da lafia hakan na nufin tun ba yau ba fa? An samu circonstanc da yawa da hannunsa ya kai kan nata ko wani waje na jikinta ya ji dumi a jikin nata Jakarta ya ajiye mata ya karasa ya dana wajen bed dinsa Bed din ya fito mai dauke da yan gida gida a jikinsa Budewa ya yi ya ciciro zanin gado ya nufi wajen Muneerath dake kwonce A hankaki ya samu kansa da warware guda ya rufa mata shi kafin yake kara zubawa fuskarta ido sai kuma ya mike a dan zabure ya yi wajen bed din Bai cire kayansa ba ya haye saman gadon yana shafa mararsa tare da dan rintse idannuwansa ya juya bayansa ya shiga adu'ar baci kafin ya ringa bitar karatu a kasan ransa ko zai samu barcin ya dauke shi Shi ya kwonta ba da wuri ba, kuma shi ya rigayeta tashi domin motsinsa ya farkar da ita A hankali
Chapter 66 · 0% Book details