← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 114

Sashe 69

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 4 Kasa kasa ta ce" Ke dillah ki saki jikinki kin wani kankame mu je mu runringume sun, wai a nan fa sai ka rungume mutun, aman walahi kar ki rungumi maza ni dai ba ruwana sai mu je dakina na fada maki abinda Mah ta ce da lamarin maza" Ita dai Saudat, kiri kiri take kallon ikon Allah, a lokacin da tana tsate Muneerath ta idasa jikin Mah da farin ciki ta rungumeta a cikin jikinta ta bata peck tana mai farin ciki da fada mata ta yi kewarta kafin ta zana mata irin salar da aka yiwa HANJA a cen, ta karashe da fadin ita kam yanzun kuma bata san wa ya bata masa rai yake fada ba Tana nan tsaye ta ga irin bahagumen rungumar da ta ba Iman ta rada mata cewar fatan dai yanzun an daina iskanci? Sannan ta karasa ta duka har kasa ta gaishe da Pah wanda abin mamakin ya dafa kanta ya saka mata albarka yana ta sakin murmushin da ta rasa ko na meye kafin ta tashi tana kallon hannun Iman da ta yi kici kicin gaba daya yannayi na bacin rai da tashin hankali sun tataru sun nuna kansu a tare da ita ta tabe baki ta ce da Maj zasu ke da kawarta aminiyarta ce tun niger sai yau Allah ya sada su ta fito itama yanzun Hostess ce, inda Mah ta gyada mata kai domin gaba daya hankalinta a kan rigimamenta da ya zama kamar status kawai bin Muneerath din yake da kallo har abin na bata tausayi Har sun fara tafia Muneerath ta daka birki ta dawo tana murmushi ta kalli wannan ta kalli wancen, a hankali ta kara kunnenta a kusa da Mah wadda ta yi tsai dan sauraronta , sai dai dama Muneerath ko rage murya ta yi ba wai iya rada ta yi ba domin bata iya yinta cen kasa ba ta ce" Mah wayo Allahna, Mah sir dinmu wannan freind din nawa da na fada maki shi kadai ne abokina namiji a duniya wai yace wai wai......." Sai ta rufe fuska tana ta murmushi kafin ta juya da gudu ta ja hannun Saudat ta nufi lft da ita ta danna suka shige inda Mah ta saki dan murmushi bayan ta raka su Muneerath da kallo cike da sha'awar sakalcinta da yarintarta har suka gushewa ganninta kafin a hankali ta maido dubanta kan HANJA Sai da gabanta ya fadi, Gaba daya fuskarsa ta gama hadewa tsaf haka kuma fuskar ta yi wani irin ja Huci yake fitarwa wanda yake nuni har gaban kirjinsa A hankali ta kara mika hannunta ta matso shi sosai ta roke hannunsa da hannunta guda kafin ta kai dayan hannun nata wajen kirjinsa cike da tausayawa ta ce" Son, kalle ni, plz ka kalle ni, dan Allah ka sasautawa kanka fushin nan, Son so kake a maidata ne? Idan har a kasan zuciyarka so kake ta fita daga nan zan yi hakuri son, zan yi, dama bana so ace bata rigaya ta idasa cika burinta na son zama Hostess mun barota a cen an koreta ne, domin D'a na kowa ne, aman idan har yanzun so kake ta tafi shikenan ka shirya mata tafiyar sai na yi mata rakiya in sha Allah, dan Allah ka bari haka ka ji? Yau fa birthday dinka ne, ranar da take baba a wajenka da mu baki daya, ka ga kuwa cake dinka? Na maka girki da kaina...... plz ka dube ni Son?". .......ta katashe tana kara sado dubansa kanta domin idannuwan nasa a kan hanyar da suka shige A hankali ya lumshe idannuwansa , hannunta dake cikin nasa ya kawo wajen kirjin nasa a hankali ya danna kafin ya rintse idannuwansa Muryarsa wannan karron ba da babatun ihun da ya shigo da farko ba, ba da fadan da ya shigo ba, a hankali sannan a sanyaye lafuzan wani na korar wani a hankali ya ce" Mah i'm seek " Gabanta ne ya fadi da yannayinsa, da kuma furucinsa, Haka ya fada a jiyama a cikin waya kuma daga baya ya ce wai ya warke Aman a yanzun itama irin bugun zuciyarsa da irin yadda idannuwansa suka rikide sai ta tsorata, dan haka da sauri ta umarci Iman kan ta kira mata docter kafin su yi ciki tana rike da hannunsa gaba daya hankalinta ba a kwonce ba ta tsaya kisa da Pah tana gannin yadda hankalinsa kwonce shi ko a ka bai wani nuna damuwa da yannayin Hanja dinba sai ta ji haushin hakan ta idasa jan hannun yaronta da nufin kaishi bangarensa sai kuma suka dawo domin tunawar da ta yi akoy tgr ta taimaka masa ya kwonta saman kujera ta shiga cire masa takalmansa da safa da komai kafin ta zauna tana rike da hannunsa tana cika tana batsewa da yannayin Pah, kuma har kasan zuciyarta a yanzun kam ta hakura da rike Muneerath din tunda dai haka zaman Muneerath din ke rikita shi, ta hakura, Allah yana ganni dama yarinyar ce ta shiga zuciyarta , irin hakurin yarinyar da courage dinta kuma ya sakata sakawa ranta abubuwa da yawa Jinninsa aka diba, bayan aune aune likitan ya tafi da sauri da kayan dan dubawa A hankali ta talabe shi da dan jus din da ta zuba a dan kofi ta kafa masa a bakinsa ya dan surba ta maida kan nasa tana shafawa ta kalli Pah dake dadana Computer yannayin fuskarta na nuni da fushi take ta ce" Aman me yasa zaka yi zamanka kana kallon halin da son yake ciki ko magana ba zaka matso ka masa na ji dadi ba?" Pah ya dakata ya dago ya zubawa HANJA ido, irin kwoncin da ya yi fuskar nan tasa a hade tamkar wanda aka watsawa kashi, ya yi wani irin kwonci gaba daya ya yi ja hakan na nuni da abinda ke damunsa na nukurkusarsa daga cen kasan zuciyarsa ne Abin tausayin shine shi kansa bai gama gane me yake ciki ba, ko kuma baban girman kan dake damunsa ya hanna masa ganewar Ya kasa gane cewar yana cikin bacin ran tunanin ta yi magana da waninsa ne? Ya kasa gane cewar dariyar da take saka shi bai shirya ba a cikin tsarin abinda ya rike masa wuya ne Uwa uba ya kasa gane cewar babu halitar da aka halita ba kishi a jinsin dan adam ko wani iri ne sai dai idan bai hadu da ainahin abinda zai yiwa kishin ba.....ko kuma ya gane baya so a gane ya afka dan gudun kar a masa dariar shi mai fadin bai san KISHI ba? Ko kuma yaron nasa na cikin duhu ne? Idan kuwa yanna cikin duhu har haka lalle yana tsoron yaron nasa ya fada a mugun halin da ba zai iya ciro shi ba A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Hurul ayn, yaya kike so na masa ne? Ni da na yi nawa wa ya kama min?" Tsatsareshi ta yi da ido kamar zata dauke shi da su , a hankali ta cire dubanta tana ta kokarin fasara maganarsa, rashin lafiar da yake ciki ko me yake nufi? Mikewa ta je yi dan ta karasa kusa da shi ta samu gamsashiyar amsar da take son sani ta ji an rike mata hannu A hankali ta juyo tana kallon HANJA kafin ta duka kadan tana kallonsa a hankali ta ce" Son, yanzu za'a kawo maka magani ka ji? Ko na kira wajen aikinku ne na sanar masu?" Idannuwansa ya rintse da abinfa yake kasan ransa wanda ya ki gushewa, a rarabe ya iya budar bakinsa ya ce" Me ya ce mata?" Ita har ga Allah ta manta cewar Muneerath ta mata maganar cewa Sir ya ce mata wani abin aman bata idasa fada masu ba, hakan ya sa ta rasa me aka cema wa? Da sauri ta kara kai hannunta tana taba jikinsa hankalinta tashe ta ce" Khalb, dan Allah ka duba bashi da lafia fa?" Pah ya dafe gaban goshinsa yana kallonta kamar wata yar baby du ta rikice ta kasa gane cutar dan nata ba wani abu bane sai na kokowar watsar da abinda ke damunsa da yake yi tun karfinsa ya girgiza kai ya rufe computer ya mike ya karaso inda suke A hankali ya kai hannunsa jikin Hanja ya taba kafin ya kaleta Dan murmushi ya sakar mata a hankali ya kalli Hanja da ya lumshe idannuwansa tamkar mai yin barci bayan idannuwansa biyu kawai abu ne ke nukurkusarsa ya ce" Cewa ya yi yana sonta " Hanja da idannuwansa ke rintse bai san lokacin da ya bude su a kan Pah ba Dama tunda ya zo ya fara fada ya kula Pah sai wani murmushi yake yana kada kai, bai san yaushe Pah ya fara fifita yarinyar nan akansa ba, gashi dai yanzu kuma yana fadin haka? A hankali ya nemi tashi zaune hakan ya sa Mah da sauri ta so taimaka masa sai dai Pah ya rikota a jikinsa yana tatare mata goshinsa da yannayin kamar zai yi fada sai kuma ya kane mata ido daya yana mata murmushin da ya kara dulmiyar da ita a duhu Hanja ya idasa zama da kyau a hankali ya ce" So kuma? " Pah ya gyada kai da sauri yana dan daga kafadunsa kafin ya saki murmushi ya ce" Kuma da alama itama tana sin nasa dan ka ga kunya ta ji ta fada, ashe dai ka kusa zama yayan ango ka daura mata aure abinta" HANJA har wani duhu duhu yake ganni na bacin rai, abu ne da bai saba ba, abu ne da bai taba tsintar kansa a ciki ba, ransa bace ya ce" A kan me zan daura mata aure ni kuma? Bama za'a yi mata ba walahi ba wanda za'a aurama ita!" Pah ya ce" a kan wani dalili fa?" Hanja ya kalli Mah dake kallonsa ya kuma kalli Pah, sasautowa ya yi daga saman kujerar ya hade hannayensa ya furzo da wata iska daga bakinsa ya ce" Aman ai amanarta muka dauko ko?" Da wani irin mamakin jin a yau ya ce da shi a dauko amanar Muneerath Mah ta kara tsatsareshi da ido A hankali ta samu
Chapter 69 · 0% Book details