Sashe 37
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
2
A gagauce ta gama shiryawa, ba kwaliya a fuskarta ko dis domin ba kwali aka koya mata sakawa ba , haka kuma lebunan nata bata shafa masu jan baki ko man lebe ba, abinda ta yi shine saka pant da doguwar riga har kasa wace ta dame mata kirjinta da ya dan yi tudu abinsa itama ta yi mama irin na mata
Rigar kalar orang ce, aman mai duhu bata da kwaliyar komai a jikinta sannan ta auduga ce watau coton hakan ya sa ta lafe mata a jikinta ta bi jikinta har kusan duwawunta kafin ta dan saki kadan ta yi cen kasa
Takalmi ta ciro baki sidik kafa ciki sannan ba mai tsini bane mai dan tudu ne dai kasansa na kwalba
Sai turare da ta wanke jikinta da shi a nutse ta juya ta ajiye laptoo dinta da ta daidaita ta dauki hoto da shi ta ajiye ta juya bayan ta dora bakin dan kwali siriri a kanta hankali kwonce ta nufi wajen da aka ce mata ta je
Kicibis suka yi da daya daga cikin masu basu horo ta damko hannunta bayan ta wara ido gannin riga da ta saka tamkar an zana abinda ba'a so ya fito din ya fito radau da shi gaba dayanta bombe ce yarinyar ko mace tana birgewa bale maza aman sun tabata yau sir sai ya ci ubansu baki dayansu
Ita kanta madame ido ta zarro, da sauri ta kalli wajen da camera ke hasko motocinsa sunna shigowa , bata san lokacin da ta dora hannu daya saman kanta ba ta ce" Yanzu du a cikin kayanki kika rasa wanda zaki sa sai wannan rigar dake maki kyau?"
Rigar ta bi da kallo ta kalli madame din , gani ta yi kaf a kayan wannan itace ta fi sutura kuma suke nuna a kan me ta saka ta? Ita ba zata saka wadinnan dingilalun sket din ba ta fito ko kuma ta saka wandunnan nan nasu matsatsu sun matse mata cinya idan ta wuce mazan cen sunna rakata da kalo haka kawai ba, ita da a niger ne wannan rigarma ba zata saka ba dan ta san sai an ci uwata da ihu rigar fa tsaga gareta fa har kusa da cinya fa! Kai ita ba yar duniya bace walahi
Dan bakinta kawai ta turo tana kifta ido tana kallonta ta ki yin magana aman a kasan zuciyarta fadi take koma uban waye princ din nan ya yi ya gama ta koma ta maida barcinta
Hannunta madame ta kama da sauri ta yi cikin dakin da ita
Dakin ta bi da kallo, yana fitar da sansanyan kamshin da bata taba jin irinsa a duniyarta ba
Table ne madaidaici a ajiye a tsakiyan kujeru biyu lafiyayu da su, sai katon madubi da kuma wani abu dake fitar da amon murya waje sai kuma camera har hudu kusurwa kusurwa da wasu abubuwan da bata san ko na meye ba ita dai, sai mutumen nata watau sanyi karara da dakin yake yi
Wajen da zata zauna ta nuna mata ta tsaya a gabanta ta ce" Muneerah, ki saurara da kyau, mutumen da zai shigo yanzun ban san takamaiman me kika masa ba, domin idan lafia ne ganninsa na iya zamewa har ki koma ga mahalicinki baki samu gannin nasa ba in dai ba a jaridu ba ko a tv ba, abinda nake so da ke ki tsaya a nan ki hade hannayenki waje guda ki yi jira, kar ki saki ki zauna ko ki shiga wani abin daban , idan ya shigo kafin ya shigo sai an shigo am bincika dakin da ke kanki, kar ki yiwa masu bincikarki gardama dan abu kalilan na iya sakawa su sumar da ke a wajen nan, ki kula ki saurara da kyau ladabinki shi zai fitar da mu duda ban san tsakaninki da shi ba domin shi ya sa aka kawo ki nan, aman abinda na sani shine halayansa da kuma irin yadda yake da karfi da mulkim da zai zartar maki da hukinci a nan kuma kin kade har buzunki, ki sani kar ki sake ki zauna sai ya zauna bara na fita ki tsuaa a tsayen nan fa"
Tana gama fada ta fice ta bar Muneerath tsaye baki da hanci da ido a bude ta bita da kallo, wanda ya kawota? Wai tsaya hala sir abokinta? Kai aman kuwa dama shine zai zo bai fada mata ba ko menene? Kuma wai shine ake tsoro haka? Aman kuwa yau zasu sha mamaki idan ya zo yana wangale mata baki tana cin magani dan ba zata sakar masa fuska ba sakamakon zai zo bai fada mata ba walahi!
Tsayawar ta yi tana hamma tana tarewa da hannunta tana dan kale kale a kadan ta dauki minti goma sha biyar ba shi ba alamunsa hakan ya sa ta tabe bakinta ta nufi kujerar da ba ita aka nuna mata zata zauna ba watau kujerar da shine zai zauna a sama ta hau ta zauna tana lumshe idannuwanta sakamakon barcin dake cike a cikinsu ta dora hannayenta saman table din ta dora kanta a sama ta kwontar tana limahe idannuwanta wani dadadan barci ya zo ba sanya ya sureta irin mai tafe da dadadan mafarkin nan nasa ta lula duniyar gidansu bayan ta gama tsakin wai wani tsaya sai ya zauna ta zauna kamar shine OGA!
Wanda ke zaune a gaban computern ne ya gama kallon ikon Allah gannin ta zauna saman kujerar da Sir ne zai zauna a sama uwa uba ya ga ta kwonta abinta ta yi barci ya mike da niyarr zuwa kusa da abin maganar da zai yi dan ya tasheta ya tuna mata abinda Madame ta fada domin sun fita tarbo shi ne gaba dayansu, kawai sai gani ya yi an bude wajen, sojoji suka fara shigowa dafka dafka da su fuskar nan a hade sunna rike da bindigoginsu lokaci daya suka shiga bincikar wajen baki dayansa kafin oga kwata kwatan ya shigo shima cikin takunsa na kosashen ingarman namiji inda dukan manya manyan wajen ke tafe a bayansa sun yi shiru ba mai kwakwaran motsi
Kai tsaye shine ya fara zuwa kofar da aka saka Muneerath, sannan ya gama fadawa sojojin cewa yarinyar bincikensa ce ya dauki abin nan da ake karawa jikin mutun dan a ji idan da wani mugun abin a jikinsa abun ke yin kara ya shaida hakan ya rike a hannunsa na dama ya nufi kofar da aka bude masa inda wanda aka bari gaban computer ya ji wasu hawaye masu dumi na son zubo masa sakamakon tunanin yau sun cira bata nuna ba du sai sun fadawa yan garinsun da ya yi , sannan ya kalli madame da ido yake nuna mata cewar ba kanta fa idan har ya shiga a yanzu aman sam bata gane ba har sai da ya sa kai sanann aka basu damar su tsaya a gaban alon da zai nuna masu abinda yake faruwa a cikin ne
Cikinta ne ta ji ya mata wani irin kuka a lokacin da ta ga HANJA tsaye da mamaki yana kallon Muneerath kwonce tana sheka barci a saman kujerarsa kafin ta ji kafafuwanta sun gaza daukanta ta yi kasa tana zarar ido jiki a mace
Da mamaki yake kallonta na tsayin minti biyu ya gama yarda cewa da gaske barci ne take yi a saman kujerarsa, ta zauna kafin ya zauna harma ta yi barci, nan da nan zuciyarsa ta fara tafasar bacin rai ya gama yanke nata hukuncin shine zai saka jirgin da zai tafi africa ya dauketa a yau ya watsar da ita a duk inda ya ga dama idan ya so a cen ta nemi danginta bayan ya gama kurce baki daya al'umar kasar da ya daukota a kan list din wa' inda zasu ringa horar da Hostess dan ya kula basu san meye ma'anar hakan ba!
Rai bace ya juya zai bar office din , lokaci daya kuma ya ja ya tsaya sakamakon lalausar fuskar mamansa da ta bayana a cikin kirjinsa da kalamanta da tunanin irin nacin da ta nuna a kan yarinyar
Juyowa ya kuma yi ya kara ja ya tsaya ya kuma zuba mata ido, Bukekiyar banza bukekiyar wofi! Ya saba idan ya zo ma'aikata yan aikin wajen suka yi laifi ya hukunta uban gidansu, aman a yau yana tunanin ya zama wajibi hukuncin nan ya hau kan yarinyar nan kafin ya hade baki dayansu sauran daya bayan daya , kai ya zama wajibi ne yau yarinyar nan ta san menene iko! Ya zama dole ya bata tarbiya ya nusar da tsagerancinta domin ba zai manta irin yadda ta zo masa kai tsaye gabansa tana masa irge da wasu yatsunta ba tana fama da wani shegen tumbin tsiya wai ita Hostess ! Kai dolema ya kara hukunta wa'inda suka dauketa suka sakota a duniyar JIRGI!
A DAKE YA RINGA DAGA KAFARSA YANA KARRA TAKU KUSA DA TABLE DIN, WANDA DU TAKUNSA SAI GABAN MUTANEN DAKE GABAN ALON SUNNA KALLONSU YA RUGUZA YA DUGURGUZA YA FADI.....INDA DA YAWANSU SUN GAMA SAREWA CEWAR TASU TA KARE A YAU A GIDAN NAN, DADIN ABIN DAYA IDAN YA KOROKAN KO YA MAYAR DA KAI MAKARANTA KO YA BAKA WANI AIKIN BA ZAKA DAI YI ZAMAN BANZA BA
Lokaci daya ya ajiye hannayensa da abin cajetan a saman table din kafin ya dago hannunsa na dama ya daki table din da dan karfin da ya saka ta a firgice tana jan tsaki ta dago kanta a hankali ta saka idannuwanta masu dauke da launin abin barci a cikin nasa masu dauke da kakausan kallo da yannayin fushi a cikinsu
A tsorace ta zabura ta mike tsaye hakan ya sa yan dugwui dugwui din mamanta motsawa dan ba bra ta saka masu ba sanann dan kwalin da ta daurawa kanta ya kunce ya fadi saman dayan hannunsa dake saman table din kafin ta fito da sauri ta zagaye shi ta koma gefen kujerarta da aka ce tata ce ta zauna a rikice ta kuma mikewa tuna maganar Madame ta tsaya ta sada kanta hannayen nata a hade inda shi kuwa mai zai yi banda tsura mata ido mamakinta na neman halaka shi kafin ya mike tsayinsa gaba daya yana kara kare mata kallo dan idasa fitar da dukan abinda ya dace a hukuntata a kansa kafin ya kai hannunsa ya ciro yar Silent bindigar dake jikinsa ya direta a saman table din yana mai binta da idannuwan nan nasa tamkar zasu dauki mutun da kallo a dake ya ce"
More cmmnt......more pags
11/14/21, 12:48 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*