Sashe 83
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
iyayensu suka aniya nufar cikin gidan Lokaci daya ya dakata ya tsare matan biyu da suka yi saura wa'inda ke dakuwa da junna ya ce" Kai,hala da nace na sake ku a tunaninki wasan yaa nake?, Ke delu dama saki daya ya rafe mana na cikashe maki shi, ke kuma sarai ai biyu na baki a jimulce dan haka ba sauran zama da ni da ku , ku kama gabanku jarabar ta isheni haka, inm lalatace ne ni da saka hannun matan nan, kun mayar da ni kamar dan dambe ni kunlum ina cakuwa da mutane ana abu kamar yam wiwi, ni ban ajiye ba ban ba wani ajiya ba, to ku sani na gaji iya gajiya, y'ayan oga kuma ku barmin su zan iya da fitinarsu, ke Bakuwa shigo mana na raka ki bangaren su Yar ogan" Da sauri Saudat ta daga kafa ta karasa ya ja hannunta ya turata ciki ya rufe kofar harda saka sakata kafin ya ja ashar da rantsuwar du shegen da ya bude shi da shi ne kafin ya tisa keyar Saudat da ta gama gane cewa lale Muneerath din yar ogan ce, sai kuma ogan ke iya mata A tsaitsaye suka same su a falon Mamansu Muneerath na tsaye tana kallon mahaifiyarta cike da mamakin yannayinta Oga ya yi dan gyaran murya yana dan wani abu kamar wanda yake tsoron shiga kai tsaye ya ce" To ki zauna mana wai tsayuwar ta mecece?" Muneerath ta juyo tana kallon Oga ta kuma kallon mamanta Mahaifiyarta ta dube shi a kausashe ta ce" Me kuma kake so Mutari?, Dan Allah ba sai ka shigo nan ba ka tafi kawai na ji da y'ata ta fada min a infa take! Ka koma ka barni da ita idan takamar y'ayanka ana masu taken sun gado rashin mutuncinka yau ta dake ni sai na san na hada jinni da shedan!" Da sauri Saudat ta juya zata fita a dakin Muneerath ta yi gagawar kamo hannunta ta janyota ciki A hankali Muneerath ta kalli Mamanta mahaifiya a gareta muryarta a sanyaye ta ce" Sai nake gannin kamar kin damu da son sannin daga inda nake, ko kuma kina son sani ne dan ki wulakantani?, Inace Sir ya shaida min an yi kira na nemi alfarmar a bani ke kin nuna ba sai kin amsa ba kawai na gaishe su?, Shin kin manta burina na son zama hostess da nake kwana da shi nake tashi wanda kika ce min ni mahaukaciya ce?, Ko kina son ce min a yanzu kin san darajata bayan na rayu da ke cikin rayuwa ta halin ko'in kula wace baki san darajar kowa ba sai oga?" Idannuwanta dake rintse tana sauraron datata mangangannun yarta ba taunawa ta bude rai bace ta dauke Muneerath da wani gigitacen marin da ya saka Oga yin tsuru tsuru har cikin zuciyarsa ya ji amsa kuwar marin kafin da sauri ya shigo gaba dayansa yana rike Muneerath din da ta buda idannuwanta da har suka fara yi mata ja tana kallon Maman nata Rai bace mahaifiyarta ta ce" Ki sada dubanki a cikin nawa kafin na saka yan yatsuna na kwakwale maki ido na zubar a wajen nan Muneerath !, Ki tausasa kalamanki a kaina tun kafin na koya maki yadda ake furuci wa mahaifiya!, A yau idanma karuwa ce ni, idan yar shaye shaye ce ni, idan mahaukaciya ce ni , nisawa na yi kika tsago jikina kika fito....kuma a haka da haukan nawa da iskancin nawa na shayar da ke na suturtar da ke!, Idanma kakan tsatson marar mutunci kika tsago kika fito ki kula ki tausasa muryarki a kaina in ba haka ba komai na iya faruwa ciki harda rasa harshenki domin ba zan maki baki ba ni, sai dai na ringa tsinguyar naman jikinki daya bayan daya har na karar maki da su!" Oga da idannuwansa ke rintse da bacin rai da abubuwan da matar tasa ke yi ya budi baki a sanyaye ya ce" Me zai hanna mu samu kebewa mu tatauna a nutse ta yadda kowa zai fahimci kowa ne?, Kina gani fa daga doguwar tafia take" Da dan daga murya, da bacin ran da take ciki ta juyo a hasale ta ce" Dillah ka rufe min baki azalumi, maci amana wanda ke raba y'aya da iyaye da kowa nasu dan cikar burinsa!" Wani marin ne ya sauka a jar fuskar mahaifiyar Muneerath wanda hakannua saka Saudat kaiwa kasa saman gwuiwowinta cike da tsoron al'amarin dake faruwa Shima yanzun cikin daga murya ya dubeta cikin ido ya ce" Ya isheki haka!, Na ce ya isheki haka kin ji? Na yi, na je na yin!, Me yasa a lokacin da na zo wajen ki da maganar soyaya dan kin ganni a kafa na yi aski irin na gayun zamanina kika tofa min yawu a fuska kika aibata ni kika nuna gidanku da irin motar da kike tukawa ta alfarma kika ce da ni aman mahaukaci ne ni kuma bani da magaya ko?, Kika aibata min iyaye kika aibata min dangi kika nunan ko akuyar gidanku ta fi karfin na yi zaman aure da ita bale ke yar gata mai gata gaba da baya?, A kan me da na zo baki yi min maganar kirki kika rabu da ni ta sigar da ta dace ba sai kika wulakantani mafi munin wulakanci harda watsa min ruwa dan na nemi soyayarki?, Ni bana tare da kuruciya ne ko bani da zuciya a cikin kirjina aka fada maki ?, Walahi walahi ban taba son mace kamar yadda na so ki ba, a kan dole dan na rayu da ke na kuma koya maki hankali na maki asirin da na raba ki da danginki da duniya baki daya ya kasance a duniya idan ba ni ba bakya gane yaren kowa, idan ba soyayata ba bakya fahimtar ta kowa, sai dai halayanki na yawo wajen biki wannan ba ni na dora maki ba, idan kika auna izina ce ta hau kanki Allah ya nuna maki shi ke shiryarwa, kin zageni da dan iska dan kawai na zo a shiri irin na yan gayun da basa jin magana, ke sai gashi da aurenki kike yafa dan gyale kina shagalinki duda na yarda cewa ba maza kike bi ba aman yawon ta zubar din da kike Allah ne ya nuna maki !, Ba zan iya ba, walahi ba zan lamuncewa kowa ya wulakanta yar oga ba, Halina kuma da kike zagi cewar mugun tsatso mugun hali na ji na dauka, ni dai bani da hali irin na izgili!, Idanma a yanzu kike son koyawa y'ata ladabi ki bita a sannu kar ki rikita min ita domin kaf cikin y'ayana zan iya rantse maki ita kadai nake iya shama kur'ani!" Yana gama fada ya juya har yana gannin duhu duhu a idannuwansa ya fito, nan fa ya ga y'ayan yan mata sun layu sunna saurare hakan ya saka shi tsayawa ya kare masu kallo gannin sun yi tsuru tsuru ya ce" Kowace ta fida mijin aure nan da sati biyu in ba haka ba in ban yi sadaka da ku ba ku ce min shege!" TABDIJANNNNNNNNNN 11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar: *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*