← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 114

Sashe 97

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 6 A hankali ta kuma dan kokarin kwace kanta tana rintse idannuwanta dan jin yadda gaba faya zuciyarta ke neman biyowa ta bakinta ta fito "Innalilahi" ta fada tana jin ta kasa wani kwakwaran motsi a rikon da ya mata A hankali cikin dan fada fada ta ce" Ka sakeni, ka wani rikeni kai dai kowace banza tana iya hawa kirjinka kau? Sakarni kar a shiga min zanen cikin yan iska" Mamakin dake neman kasarashi a kan yarinyar nan sai irin karfin da take da shi a tatare da shi Ya jima da wuce bangaren da daga ya kalli mace ya ji halitarsa ta motsa sai da ya farra ganninta A hankali ya fara tsorata da koda son rike hannunta ne bale kafeta da yake da ido shi kadai ya san me yake son karanta a tare da ita da ta fi sauran matan da yake mu'amala da su Ya yi tunanin ko kalar fatarta ke birge shi? Ya yi tunanin ko wannan bombom din nata ke haukata shi? A yanzu haka ba wai son sakintan bane baya yi, wollah abinda ya mike masa kamar sanda yake jin kunyar aminiyarta da Iman da sukai masa kurru gani Hakanma sabo ne a gare shi wai jin kunyar a ga yannayinsa A hankali ya rage muryarsa ya ce" Me yasa dan na rike wata a jikina yake baki haushi? Munarah kina jin haushin na taba wata ba ke ba , kuma ke na taba ki kina cewa iskanci ne, ni kam meye wai irin naku al'adun da ake yi da wa'inda ba'a yi" Ajiyar zuciya ta ringa saukewa sakamakon sajensa da kuma hucinsa dake sauka a kuncinta, sajensa kuma sai sosa mata lebe suke A hankali ta ce" Dan Allah sakeni fitsari nake ji" Sai da ya ji tamkar jinnin jikinsa zai tsaya, a hankali ya ringa dabarar sakatan dan shima ya fahimci idan ba sakatan ya yi ba komai na iya faruwa Yana cikata da sauri ya juya har yana jin kamar numfashinsa na gaf da tsayawa ya wuce su da wani irin sauri ya shige Lft ya sauka dan so yake ya yi bangarensa ya zauna ko zai samu nutsuwa Ido da ido suka kalli Junna da Iman, a hankali ta so cire dubanta a cikin na Iman din, sai dai hakan ta gagara sakamakon mugun kallon da ta kula Iman ta tsareta da shi Muryarta ba karfi ta ce" Ke kuwa me ya samu idannuwanki?, Na ga kamar hararena kike" Iman ra hadiye abinda take ji a ranta ta ce" Ba kama bace, ba kama bace Muneerath, na gaji, walahi na gaji, me kike so da ni ne dan Allah? Dukan abinda yake nawa kin karbe, harta kusancina da Mah kin amshe bayan kusancina fa Mah ya fi kusancinta da Hanja din kansa da kike ta budewa da isar naki ne, kin kuwa san irin lokacin da na dauka ina dama da soyayarsa? Kin san irin son da nake masa?" Muneerath dake kallonta a hankali ta ce" Ni yanzun ina hadina da maganar son da kike masa? Idan soyayarku kuke kin taba gannin na yi magana ne? In dan rike nin nan da ya yi ne ki yi hakuri, ni da kaina abin na damuna, sai ace shi musulmi ne, sai ace shi dan musulmai ne sai kuma ya ringa rike mutun a jikinsa bayan ni ba muharamarsa ba, kin ga soyayata da Mah kuma Allah ne ya hadata, ni dai ba danginta bace aman ta rikeni tamkar yar cikinta, wannan kuma ban san yaya zan yi na hanna ba, Iman me yasa kike nemana da fitina ne? Kin ga ni yanzun zazabi ne ya sauko min har rawa jikina yake, mai yiwuwa mutuwa cema zan yi dan zufa ta karyo min, zuciyata ta kusa fito min ta baki, koma menene ki yafe min Hanja kuma ki dafa ki cinye abinki" Iman ta ce" Abinki dai, gashi kiri kiri kina son min shigar sauri a wajensa? Abin takaicina kamar makauniya, kamar kurma, kamar mahaukaciya idan kina abu kamar innocent, maganar rungumewa kuma ai Hanja kakansu yake yi, a yau idan ya yi niya sai ya kwonta da mace biyu su kwana a jikinsa, maganar adini kuma ai inaga ba ke ba ya dame kaf ahalinki ya shanye a fannin harda!" Muneerath ta lumshe idannuwanta , jikinta ya karra mutuwa, shin me yasa Iman ba zata daina mata abubuwan da take yi mata ba? Me yasa kuma idan ta nuna mata tana cikin halin son kadaice kanta bata ganewa? Bata da lafia Bon sang!, Bata cikin mood da kowace irin magana a yanzu! Gaba daya ji take karshenta ne ya zo , tata ce ta kare, shine zata ringa fada mata maganar cewa Hanja na kwana da mata biyu? Dama haka yake? Dama haka ne halayensa? A dan kaushashe ta ce" Ban ga anfanin tarin sannin nasa da baya anfani da shi, Iman wani irin so kike ikirarin kinaiwa Hanja?, Koma wanene so din nan na tsine masa albarka, Iman , Hanja ba saurayina bane, hauka kike rabawa, shirme kike yi, kuma ina matukar tausaya maki, ke baki da zuciya ne? Namijin da kika san yana aikata irin haka da wasu matan ne har kike yiwa irin so din nan?, Ina zaki je da matsalarsa? Ina zaki je da fama da shi? Ko zaki rayu da shi a hakanma?...." Ta hadiyi yawu tana kallon yadda Saudat ta dawo ta rike hannunta fuskarta na nuna matsananciyar damuwa , a hankali ta ci gaba da fadin" Ko kema aikin da kike na facebook ba iya nan kika tsaya ba? , Ba'a taraya sai halaya ya zo daya, Iman kema aikinki kennan?, Iman ni da ban hada jinni da shi ba, ban hada soyaya da shi ba, wannan abin da kika fada yana kona min zuciyata fiye da tunaninki, Iman ji nake tamkar na yi ra kuka da dukan karfina har sai muryata ta daina fita, Iman ciwo nake ji jin haka yake, ya fara zama abokina, ya fara zama yayana, na fara fahimtar waye shi, sai ki saka min tsanarsa a raina?, Iman halayan nan nasa har ya kai a bayane kowa ya sani? Me mamansa ta dauka mataki? Me mahaifinsa ya dauka? Ko kallon da nake masu na iyaye masu matukar kaunar y'ayansu, masu matukar tsayawa a lamarin yaronsu soyayar bata kai zuci ba?, Iman.......Im......" Kuka ne ya ci karfin Muneerath, ur Muneerath mai karfin zuciya, Muneerath dinmu da bata san gabas ba, Muneerath dinmu da karamin abu ko nace abu mai tana zuciya baya gagawar taba tata, Muneerath dinmu da ko kukan da ta yi na faduwar Mah nan da nan ta saku da ta ganta a garin harma ta ga da sauki, itace ta fashe da kukan da bata san me yasa ba Tun karfi ta dora kanta a saman kirjin Saudat tana rusa kukan da dukan karfinta Muryarta a cen ciki take fadin" Dan Allah, dan Allah ku taimake ni, walahi na rasa gane kaina, dan Allah ku nisantani da kasar nan, ku kaini nesa, daga garinmu zan iya aikowa da Mah adu'a, daga inda nake zan iya yiwa Mah adu'ar samun lafia, Saudat dan Allah ki kirayi Freind a maida ni gida, ba zan iya ba, walahi zuciyata gaf take da bugawa ban san dalili ba, shi kuma ribar me yake ci da wannan abin? Saudat na tsane shi! Na tsane shi!" Subahannalah, wannan shine ba sabanba namiji da kwontace Tabas wannan bacin rai da ya rufe ma Muneerath ido tsabar tsagworon kishin da take fama da shi ne ya sakata irin furucin nan, ba sani ta yi ba, ba taba yi ta yi ba, lalle akoy ciwo ka ji wani da kake gannin darajarsa a irin wannan halin aman ta kasa gane cewar abinda ya sa abin nan ya taba zuciyarta har haka dan ta gama macewa a kogin son dan nasara ba tare da ta shiryawa hakan ba, kamar yadda ya gama haukacewa a sonta A yanzu matsalarta daya ce, kuma tana gannin idan hakan ya kasance gaba dayansu farin cikin hakan zasu shiga Taba so Na iya cenza mutun, mai mumunan hali ya dawo mai kyakyawa a lokacin da ba'ai tunanin hakan ba So take ta yi anfani da wannan damar ta samu ta yiwa Hanja dukan da so zai saka shi daina halayansa, duda tana tunanin da kamar wuya Aman zata kwatanta, tsoronta daya ne kar a je ya kasa zama waje daya ya kula da lafiyar mahaifiyarsa A hankali ta ringa janta har suka shige suka sauka Sunna saukowar bata hannata kukan da take yi ba wanda ya saka Pah mikewa da sauri domin falon yake bai jima da saukowa ba, masalaci ya fito shine ya zauna yana jan carbi yana gannin matarsa na masa gizo ta ko'ina a cikin gidan, yana fama da kewarta mai girman gaske "Subahannalah, me yake faruwa, bata da lafia ne?" Ya fada yana nufo su yana kallonsu da wani yannayi na tsoron jin abinda ya sajata kukan Da sauri Saudat ta ce" Ba komai fa Pah, kawai wani dan abu ne ya sakata kukan nan har take cewa zata mutu a kaita Niger". Ta fada da sauri dan kar ya yi tunanin kukan ko na matarsa ne shi mai majinyaciya a kwonce Muneerath ta dago tana jan hanci ta karra fashewa da kuka tana fadin" Wannan ne karamin? Ke yanzu dan Allah bakya jin kamar zaki mutu da kika ji maganar nan?" A hankali Saudat ta girgiza kai tana kawar da kan nata cike da son dane dariyar yannayin na Muneerath Muneerath ta ce" Baku shaku ba shi yasa, aman ni fa muka shaku dole na ji ciwo a raina, Pah wai Hanja, HANJA" Sai ta kasa karasawa dan tana tsoron kar a je bai sani ba ta fada masa juma a samu matsala Pah da kula ya ce" Daughter kukan nan ya isa haka , ki daina sshi ki fadan me Hanja din ya yi ne?" Hanci ta ja tana kallon Saudat ta ce" Fada masa " Saudat ta zarro ido tana kallonta, sai dai ba zata iya musawa baa domin a tsaye yake a kana kafafuwansa yana jiran jin dalilin kukan, sai dai
Chapter 97 · 0% Book details