← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 114

Sashe 13

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
8
Muryarsa cen ciki ya ce" Mam, ba zan jima ba fa "
Kamar wata mai kannanun shekaru ta make kafadarta tana dan jujuya kanta zata yi magana daya daga cikin masu kula da gidan nasa ta zo ta ja ta tsaya kanta kasa cike da ladabi ta ce" Mai kula da Tigre ya ce ya fito da ita ne ko ya barta?"
Bai juyo inda take tsayen ba, gaba daya hankalinsa a kan datijuwar dake gabansa mai cike da annurin fuska, kamar ba zai yi magana ba cen kasa da yaren turancin ya ce" Ku bamu waje "
Yana fada mai aikin ta fara ficewa kafin kyakyawar budurwar nan ta mike tana kallon fuskarsa ta yi murmushi ta fice ta tsaya jikin kofar ta jingina tana lumshe idannuwanta
Ita dinma sai da ta ga du sun fice ta ringa dan matsa hannunsa ta shiga fadin" ALLAH shi ya haliceka, ya baka damar numfashi, ya ara maka daula dan ka sarafata ta hanyar da ta dace, Yarona baban tashin hankalin babu inda bawa zai shiga ya labe kida a tandun kwali ne bazai boyewa mahalicinsa abinda yake aikatawa a aikace da wanda yake cikin zuciyarsa ba, Khalb shin baka tsoron haduwarka da Allah?"
Idannuwansa ya lumshe a sanyaye ya dora gefen fuskarsa a hannunta, bayan hannunta, cen ciki ya ce" Ina jin kunyar mahalincina, ina jin tsoron haduwata da shi, Mam, ko ni dan wuta ne shi yasa na kasa rabuwa da aikata alfasha? Kin ga Jirgi zan hau na ja na tsayin awa bakwai ban san yaya zata kaya da ni ba a cikin tafiata , aman sai na zabi aikata zina kafin na shiga......na tsani wannan halaya nawa, kuma ina matukar jin tsoron kar a je ko dan wuta ne ni, ko Allah ba zai yafe min ba, ko ba zan shiryu ba?"
Da sauri take dan girgiza kanta a sanyaye ta ce" Abinda Allah baya so shine bawa na neman yafiya kuma yana kara dulmiya "
Idannuwansa da suke da launin ja ya dora a saman kanta ya ce" Shi yasa ai nake jin kunyar na kuma zuwa da kokon barata da neman yafiyata"
"Gaban wanda ya haliceka? HANJA wanda ya ce da kai rokeni ni kuwa zan baka? Shi din shi kadai ya isa ya shiryar da bawansa, HANJA ina so ka ringa kokarin hanna kanka aikata zinar na tabata zaka fasa zan wayi gari HANJA dina ya fasa wannan mumunan aikin? Da na fi kowa farin cikin haka domin zina bashi ce My Son" ta karasa fada cike da yannayi na rarashi tana kara fuskantarsa
Idannuwansa ya lumshe yana sauke ajiyar zuciya, dama ya san du saurinsa a kadan mamansa na daukan minti arba'in tana nasiha shi yasa yake gagawa dan kar ya shiga lokacinta kafin ya tafi, a nutse ya ce" Ta yaya? "
Bata gajiya ba ko yanzun , ba zata taba gajiyawa da maimaita masa ba hakan ya sa yanzunma ta bashi amsa cike da fatan samun nasara ta ce" Ta hanyar yin aure, ta hanyar kyamatar taba wata macen da ba taka ba, ta hanyar kwadaituwa da son samun ladan aikatawa idan da igiyar aure a kanka"
Murmushi ya yi ya tsurawa fuskarta ido, yakan ji baban muradin son budar bakinsa ya kaleta ya ce da ita' Ta yaya zan iya auren wace ta gama rabawa? Ba dan ina jin zan ji haushin hakan ba, a tunanina da tunanin samawa y'ayana uwa mai mutunci wace zata basu tarbiya, tabas a zamanin nan da ya kazamce ko a garin da musulmai suka fi yawa ana aikata alfasha, bale garin INGLA, bai san ta yaya zai kwatanta mata cewar a tsarin rayuwarsa bai tsara tara mace sama da daya tak ba, domin sunna da yawan tafiye tafiyen da suke yi da matayensu, baya son ya zamana yana yawo da wannan yau gobe da wancen, kai bama zai iya wai wani tsayawa shirmen mata ba, tsakani da Allah ko mace ya aura idan tana bashi ciwon kai zai saketa ya dauki wata dan ba zai iya wahala ba, babar damuwar ita ce shin wacece zata iya da shi?, wacece zata iya hakuri da lalurarsa? Shi ya san wannan abin lalura ce, wada sai wace ta jajirce, ta jure, ta zama jarababiya fiye da shi zata iya da shi, ba wai shi kadai ba haka yannayinsu ke dawowa koda kuwa halitarka yar karama ce'
Ajiyar zuciya ya kuma saukewa a sanyaye ya ce" Ki ci gaba da yi min adu'a, Allah ya bani wace zata iya zama da ni"
Murmushi ta yi har cikin ranta, ta tabata sannu sannu bata hanna zuwa, a da ba nasiha ba ko kuka ta masa zai fada mata kiri kiri cewar bai shiryawa hakan ba ba zai yi ba, yau har ya ce ta masa adu'a kuma ya nuna mata shima yana son dainawa? Ita kuwa zata yi ta yi masa da dukan karfinta da lokacinta zata fadawa danginsu su kama mata sosai a yi ta masa adu'a a saudiya
Mikewa ya yi da hannunta a cikin nasa suka nufi hanyar wajen da Zakanyarsa ke ajiye
Da sauri ta ja ta tsaya tana turo bakinta , shi kuwa ya yi murmushi ya shige ciki abinsa kasa kasa ya ce" Na sha fada maki ba zata iya yi maki ila ba, domin tana anfani da bugun zuciyata ne, ba zata iya ilata abinda yake saka zuciyata gudu ba komai kankantarsa"
Ita dai kin binsa ta yi daga tsayen da take tana kallonsa du irin motsin da zasu yi shi da zakanyar sai ta ji tsoro, irin yadda yake yiwa zakanyar murmushi kuwa sai abin ya birgeta sosai, idan ta dan daga bakinta hakoranta suka fito a kusa da kansa kuwa sai ta ji kamar gudun jinninta zai tsaya da sauri ta rintse ido da rufe baki, sai kuma ta ga sun kara gaisawa, a kadan ya dauki minti ashirin a wajen nan bayan ya gama gaisawa da ita ya kuma kara gargadin mai kula da ita kan tsaftar wajen kwonciyarta, abincinta, lafiyarta, ya shaida masa cewa ko yatsarta ke ciwo a sanar masa kafin ya fito
Rakiya suka yi masa har airport kamar wanda zai yi tafiar kwanaki masu yawa, a lokacin da ya fitar da ita daga babar motar ma'aikatar da ya sakata ya rakota har kusa da mitar masarautarsu bayan an bude ya kamata ta shiga ta zauna da kyau sannan ya shiga ya zauna yana mata murmushin da kowa ke son gannin yana yinsa ba dan komai ba sai dan shi din ba ma'abocin yin murmushi bane
Hannunta ya rike kamar yadda suka saba, a yanzun kuma bai kori yaringar ba ta kuma zuba maasu ido tana kallonsu
A sanyaye ta ce" Yau kwana goma sha daya baka je ka gaishe da mahaifinka ba, ba zaka daina yin fushi da shi ba ko?"
Kansa ya sada, bai bata amsar wannan maganar ba ya dago hannunta na dama ya dora saman kansa a hankali ya ce" Ki min adu'a"
Ajiyar zuciya ta sauke ta shiga jero masa adu'o'in tsari idannuwansa lumshe hakama nata, har sai da ata gama sannan ta dago habarsa tana kallonsa ta ce" *yarona DUTSE ne, DUTSE AJIYAR ALLAH KA FI KARFIN GARA, DUTSE A DAKA A BARI*, in sha Allahu rabih zaka je lafia ka dawo lafia, kar ka manta mutun bai haliceka ba ba abinda ya isa ya yi maka, aman Allahn da ya haliceka yana kallonka a dukan motsinka"
Murmushi ya yi ya manawa bayan hannunta kiss sannan ya fita
Yana nan tsaye har motocinsu suka wuce kafin ya saki ajiyar zuciya ya juya lokaci daya masu tsaronsa suka mara masa baya
Bai zame ko'ina ba sai tankamemen ofice dinsa, saman kujera ya zauna likitar dake sanye da shiga ta likitoci ta shiga auna shi , kama daga zafin jikinsa, matsalar ciwon ciki, matsalar ciwon kai, matsakar kafa ko hannaye, irin yannayin mood dinsa, komai da komai sai da suka tabatar normal ne kafin ya mike ya yi dakin da kayan aikinsu suke
Cikin nutsuwa ya dauki yar karamar bindiga bak'a ya kara dubata ya duba alburushinta da securit
dinta kafin ya soketa a jikinsa ta baya ya rufeta ta yarda idan ba sannin akoyta a jikinsa ka yi ba ba zaka taba tunanin akoyta ba, sauran galarsa da ba zai iya shiga gari da su ba ya ciro ya sakala ya dauki dan abin kunnen ya saka sannan ya fito
Yana fitowa ya ga HOTTEST din a laye kowace ta kama kanta ta nutsu irin nutsuwar da baka son a ga laifinka ko a kamata da wani laifin dake iya janyowa a koreka, HANJA mai gidansu ne, kuma duda kasancewarsa mutun mai harkar mata ba dai na wajen aikinsa ba, ya kasance mutunmen da ko magana bata hada shi da su idan har ba dile ta kama ba, sunna iya yin doguwar tafia sosai su dawo komai bai hada su ba ciki har gaisuwa domin ba amsawa zai yi ba
A yanzunma a tare suka gaishe shi cike da ladabi da biyaya ta yada ba zasu rasa aiyukansu a wannan baban kampanin da kaf fadin duniya suke son kasancewa ma'aikata a karkashinsa domin kampani ne mai biyan albashi mai tsoka ga mutunta ma'aikata
Bai amsa su ba daga tsayen da yake fuskarsa tamkar an ce da shi babarsa(
) ya kara gimtsewa sosai ya ce" A cikin tafiyarmu du wace ta yi wasa da oasinger a bakin aikinta, du wace ta ga abin fada irin ta ga alamun miyagun kwaya ta rufe ko ta amshi cin hanci da gangan sai na rufeta!, du wace ta yi prostitution a tafiarmu hukunci zai hau kanta domin HOTESTE ba karuwa bace!, ba yar amsar cin hanci bace!, ba kuma shagaltaciya! INA FATAN KUN FAHIMTA?" Ya karashe maganarsa sama sama kamar wanda yake bawa sojoji horo a filin daga,
Dama sun san hali hakan ya sa gaba dayansu suka amsa masa cike da nutsuwa
A haka ya amshi litafin da aka rubuta irin shirin da suka yi, irin turaran da zasu yi anfani da shi ba mai karfi ba dan kar su takurawa pasinger, irin tsaftar da ta dace da su har dawowarsu ya mikawa banasariar dake jira ta amsa da sauri ta ja gabansu du suka yi cen ciki suka shiga dogon coridor din nan ya kaisu wajen da zasu yi yar tafia kafin su isa inda jirgin da zai tashi nan da minti arba'in suka shiga
Shima ya gama daidaita komai sannan ya tafi ya shige wajensa ya rufe ya shiga kara duduba komai na jirgin cikin nutsuwa dan tafiar ta shi kadai ne, watau matukin shi kadai ne kasancewar tafiar ba mai daukan lokaci da yawa bace kuma idan an je sai an kwana za'a juyo zai huta iya hutun da yake so
....................MUNEERATH
11/14/21, 12:43 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*
Chapter 13 · 0% Book details