← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 114

Sashe 111

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir-rahamanir-rahim_ 6 Kasa kasa ya ce" Kana ji Hanja, kar mu yi haka da kai, tun jiya na basu amanar eh ana iya komawa da ita, yaya zaka ce ba za'a maida masu yarinyarsu su shiryata kamar yadda suka saba ba, akoy gyaran amare da suke inaga sunna shirya yarensu ne dan zama da namiji, to me yasa zaka ce ba inda zata tafi?" Hanja ya dan yi tsai shima kasa kasan ya ce" Wai Pah kana nufin banda haka har wani shiri suke karama matan?" Pah ya dan yi murmushi kadan ya ce" Please son yanzu fa ka girma ka wuce a ringa rigima da gardama da kai, sun maka adalci da suka kawo maka ita a jiya, so plz ka shiryata zasu zo daukanta ne in ji mijin su" Dan murmushi ya yi yana girgiza kansa a hankali ya ce" Pah u see, bata yi barci ko dis ba duka daren nan, nd ba sabawa ta yi ba, bana tunanin zan iya barinta tafia ko ina ne, Pah ka ga sarautar nan da ka dora min a jiya ko? Na dauka ban ce komai ba idan ka takura a kan maganar MUNARAH gaskiya zan ce wani abu, ka duba ka gani plz" Pah ya shiga murza goshinsa yana kallon mai martaba dake sauraro yana murmushi Katse kiran ya yi bayan ya ce masa yana zuwa Ai kam yana kashewa Hanja ya shiga whatsup ya shige ccnt din Pah ya masa voice kamar haka" Pah ka duba mana, idan ta tafi kwana nawa zai shiga tsakanina da ita? Ba zata saba da wuri ba wahala ce zata yi ta sha, ni kuma ba zan iya ba" Pah ya rasa me zai cewa sarki domin dukan abinda Hanja ya fada ya ji domin shima yana jin turancin hakan ya sa kawai ya dan kura masa ido, inda Sarki kuwa yake murmushin kasaita yana dan kada kansa ya juyar da dubansa gefe ya dauki wayarsa yana fadin bara ya kirayi mahaifin yarinyar su ji yaya zasu yi da shi?, A lokacin OGA ya jima da farkawa sunna tsakar gidansa ana shawara, ko nace yana sanar masu abinda ya yanke wayarsa ta dauki tsuwa Sai da ya mula kai ya karra irin na sababin masu kudin nan ya ce" Nana karanta min waye ne?" Maman Muneerath dake zaune tana cikin farin cikin yannayin mijin nata da a yanzu al'amuransa ke sakata nishadi haka kuma yana birgeta a dukan abinda ya yi domin du tsiya baya takata haka kuma baya wulakantata, sannan du abinsa ya iya godiya ya iya yaba mata komai kankantar kyautata masa da zata yi kuwa baya yin kamar bai gani ba ta duba a bayane ta ce" Mai martaba ne Aban Muneerath" Ya kuwa sakin murmushi ya ce" Daga ki saka shi a amsa kuwa, dan uwana ne, tunda aka daura auren nan na tabata cewa ko ba dade ko ba jima sai na zama magajin kujerarsa, abin ai na Allah ne" Ita dai dagawar ta yi tana kallon yadda idannuwan kishiyarta suka kumbura suntum dan sakawa rai mugun abu a zuciya ta saka amsa kuwar ta ajiye A nutse ya yi salama, inda oga ya amsa cike da ladabi ya ringa gaishe da sarki da su tambayar ya iyali ya waye waye har sai da sarkin ya gaji da amsawa kafin ya ce" Dangane da maganar dawo da Gimbiya Muneerath ne" Sai da gaban Oga ya fadi da karfi ya ce" Ina? Na shiga uku me ta yi za'a dawo da ita tun yanzu? Kar dai ku ce min har ya saketa Innalilahi wa inna ilaihi raj'une" Sarki ya yi sakayau da wayar a hannunsa yana kallon Pah da bai san me Oga ke fadi ba aman gaba daya hankalinsa a kan wayar so yake ya fahimta sai dai ba hali shi dai kuwar muryar Oga kadai yake ji a kunnensa A nutse Sarki ya ce" Subahannalah, me ya kawo saki ana abin farin ciki?, Al'adun sarautar garinmu ne idan aka daurawa sarki mace sai ya kwontata sannan a maidata gidan iyayenta a mata gyara da kitso da kunshi, dalilin da ya saka aka daukota a jiyan nan kennan, yanzun maganar dawo da itan ne ake" Oga ya shiga kifta ido a sanyaye ya ce" walahi gaba daya sai da na ji zan haukace, to yanzu Allah taimaki mai martaba idan aka dawo da yar Oga na mata me?, Dan Allah ka rufan asiri ku gyarata a cen ina al'adun na niger ne ba na ingila ba, ni yanzun haka maganar da nake maka gidan nawa ne na saka a kasuwa ake ta ciniki ana karawa domin ginanan nan na anguwar plateau ne na taya harma na biya kudin so nake kowace na siya mata motar hawa sai su ringa jana muna zuwa anguwa, to abindama ya dan kawo tangarda ita abokiyar zaman nata ne ta ce ina ita ina jan mota tsoro take ji, wai saboda haka ba za'a siyawa uwar Allah ja da ranta ba, ta manta ita ta nakudo abinta ta haifo, to mafanar ce ake yi ana karawa ka san mai kudi ba son hayaniya yake yi ba shine kaina ya fara ciwo, walahi ina son fitowa fadarma abin ya gagara sai nana ta yarda tukunnan, to yanzu mu da muke cikin wannan harlallar kar ku hada mu da Allah ja fa ranta dan Allah na roke ka Mai martaba" Tunda ya kama zubar sarki yake karra mamaki da lamarin bawan Allahn har ya dasa aya kafin ya samu kansa da yin murmushi yana girgiza kai cike da mangarin rayuwar oga, watau shi bai biyo ta hanyar damuwa ba, idanma ka damun kanka Gashi dai cikin ruwan sanyi sun samu mafita, sai dai duda haka sai ya ce" To ita mahaifiyar yarinyar ta yarda da hakan ne?" Oga ya ce" Ai abinda na ce shine Allah kara maka lafia, ama bara mu ji ta bakinta ai tana jinmu a amsa kuwa muke....," Ya kuwa karkata ya ce" Nanata wai a kawo maki yar gidan oga gidan nan? Ai gwara su gyarata idan zasu tafi ma je mu ganta kin san yanzu fa ba koda yaushe ake iya bari a ga Allah ja da ranta ba" Murmushi ta yi ta mike ta yi ciki dan walahi kasheta yake son yi da ranta, wai yanzun Muneerath din ce da yake lukawa ashar idan ta ki masa biyaya a wani abin ya maida Allah ja fa ranta? Shima yar dariya ya yi yana talabe habarsa da fadin" Mace mai kunya duniya ce, kai jama'a" Shi dai sarki gannin abin na Oga ba mai karewa bane sai ya masa salama sannan ya fuskanci Pah ya shaida masa ba za'a fitar da ita ba, aman dole su basu dama su mata gyara a nan koda na kwana biyu ne kafin su tafi da ita A kan Dole Pah ya aminta da hakan shi ya shiga kokarin juyawa ya je ya yi sharar fage a gyara komai kafin Hanja din ya dawo domin ya kula ba fa zai bishi ba, dan haka ya daga masa kafa ya tabata Abinda bai taba samu bane ya samu Da kyar ya iya ganar da Hanja cewar ya basu dama su gyaratan, saboda haka ya nemi alfarmar Sarki ya basu damar su ringa fita wajen gonakinsa da sauransu dan ya ga garin su matarsa da al'adunsu na yau da kulun a boye ba tare da an san fitarsa ba Ai kam hakan ce ta faru, kusan karfe goma ya fita tare da su Sir Attahir dan tafia gannin gari da shiga lungu lungu sako sako na garin dan ya ga menene kasar Niger da al'adunsu Sunna tafia babar matar sarki tare da masu gyara suka dira dakin Muneerath, tare da Saudat da matar uncle dinta Da saudat aka fara barinta dan zuwa kai zannun gadonta baban daki, SANNAN a zo da dukan abubuwan shirinta , inda ta riki hannun saudat tana hawaye ta ce" Saudat yada kika san zan bar duniya" Saudat ta ringa bubuga bayanta ta ce" Haba Muneerath ban sanki da ragwonci ba fa, dan Allah ki yi hakuri ba komai kin ji?, Babu abinda zai faru ki yi hakuri kin ji?" Muneerath ta ce" Dole ki bani hakuri, dole ki bani tunda da saninki cewa dan gidan Mah bashi da wayau kika kyaleni baki fada min zuwarma mutun na daidai da kashe mutun ne" Da sauri Saudat ta ce" Kar ki bayana sirrin mijinki, kin fa je islamiya kin san ba kyau, ki kiyaye furucinki a kan wannan lamarin, ki rike harshenki, kin ga ban taba yin aure ba , kuma Allah yana ganni ban taba sannin meye abin ba, ni dai a karatuna an fayace mana komai, sannan a makaranta an hanemu da bayana irin haka idan ta same mu da mazajen aurenmu, so dan Allah kar ki ringa fadin haka kin ji?" Rai bace ta dago da kanta ta ce" To a maida ni gidanmu mana, na tabata Oga ya kasa barci dan bana kusa, ke ai kin san irin son da yake min" Saudat kam dariya ce ta kubce mata, sai dai bata ce mata ga dalilin dariyarta ba cewar Oga ya hanna a kaita gidan, sai ce mata ta yi" Baki san Oga yana so ki zauna a dakinki ba?, Ai farin cikinsa ne ace kina dakinki kina kula da mijinki, dan Allah kar ki saka damuwa a ranki kin ji? Haba jarumar Mama" Muneerath ta ringa gyada kai tana tunanin kawai Saudat dan bata ji abinda ta ji bane take mata wannan maganar, aman ba komai zata mata adu'ar itama ta ji idan ya so sai su jajantawa junna, aman ita kam ba ita ba d'a namiji ko a lahira ta yafe! A lokacin da suka dawo dole Saudat ta koma falo aka bar masu gyara da Muneerath Ai kam ta ga gyara, ta ji gyara, ta kuma tabata gyara Dirzar fatarta ake kamar ba gobe Ruwan dumin da aka sakata kuma ko na mai jego albarka Tun tana dan jin zafin abinda ta dandana har ya bace bat ta dawo murmushi da jin yannayinta ya koma da sauki sosai A haka suka zuba hade hadensu
Chapter 111 · 0% Book details