← Book details Dutse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 114

Sashe 11

Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ke Doguwa ta min baki ne da zan yarda mu koma soyaya da wancen makirar yarinyar? (DOGUWAR WATA ALJANARSU CE A CEN GARIN DOGON DUTSI), ni ai ba dan shegiya bane bale na yarda, ta je ta auri wanda take so lafia kalau, nima na samu tawa lafia kalau na aure abata mu yi zamanmu, ke ni nan da kika gan ni ba zan kuma yarda da farar mace ba, zan samo bak'ata mu je mu yi aurenmu dan na fahimvi fararan fatar nan tunaninsu halitar matan Aljanna aka zuba wajen hakitarsu shi yasa suke girman kai*) Dayan likitan namijin ne ya yi daria yana girgiza kai ya ce" Kai Moise to meye dan ta dawo? Kai ba musulunci bama ka zubar ka dauki Christanci ai bamu ce mun fasa zama da kai ba ko?" Zai bashi amsa nurse din dake gadi ta nemi izini ta shigo, cikin ladabi ta sanar masu an kawo wata da ta suma a wajen fadin sakamakon jarabawar da aka gama MOISE ne ya dubeta da kulawa kasancewar shine babansu ya ce" kya ji balaki bata samu ba ko?" Da ladabinta ta ce" Aa itacema premiere du centre, emotion din ne ya sumar da ita, a yanzu dai mun yi mata dukan abinda ya dace dan gannin ta farfado harma ta farfado din , kudin treatments ne muke son sannin a asusun gwamnati ko mu ba yayanta ordonance?" Kallon junna suka yi, haka kawai Moise ya ji yana son zuwa ya ga Premiere du centre din da ta sume dan tsabar jin dadi ko me? Yana son ya ga irin farin cikin da iyayenta suke yi a irin wannan lokacin, yana so ya ga irin nata farin cikin itama, dan haka ya mike yana gyara rigarsa ya ce da sauran yana zuwa sannan ya fito a office din suka raka shi da kallo Ajiyar zuciya Halimar ta sauke tana dan girgiza kanta Dayan abokin aikin nata ne ya dan rage muryarsa ya ce" Har yanzu sonsa kike ko?" Da sauri ta kale shi kafin ta dan girgiza kanta a sanyaye ta ce" Wani irin so kake so na yiwa mutumen da ya yi gagawar sakin adininsa dan kawai ya tsinci kansa a cikin hali na damuwa? Ka duba ka gani Musa daga fadawa halin kangin rayuwa mutanen nan suka ribance shi ya zama kirista shi kadai a familly dinsu, a da fa mahaifinsa baya amsa gaisuwarsa har ya dawo yake amsawa, shin baya tsoron mutuwa ta masa zuwan da bai shiryawa ba? Ko baya tunanin shiryuwa ? Ko har cen kasan zuciyar Musa ya gama zubar da adinin gaskiya adinin musulunci ya dauki na kafurci ne?" Shima ajiyar zuciyar ya sauke ya dauki byro ya shiga rubutu a baban kundunsu , tabas abin nan ya matukar girgiza su, basu taba tunanin wahala zata saka mutun ya bar adininsa ya fada wani ba a lokacin da yan wani adinin suka nuna masa idan ya shiga nasu adinin zai ji saukin wahalar dake damunsa, bale Musa nasu, Musan nan ba'adare ne gaba da baya, haifafen garin dogon dutsi ne, Musa akoy mutunci da faran faran shi yasa komawarsa dan yesu yake masu ciwo a zukatansu Tunda ya shigo ya ja ya tsaya yana kallonta A yanzu zumbulelen hijab din da ta zumbula baya jikinta yana ajiye saman gadon sai wata riga marar nauyi aman ba gajera ba a jikinta wace ta siyi abinta a gwonjo, rigar mai ruwan orange ce da dan baki baki kadan a jikinta, tana da kyau sosai rigar bata da dogon hannu gajeru ne aman kuma ba sirara ba A zaunen da take hawaye take wani na korar wani ta rike hannun dan uwanta gagam Cike da shashakar kukan ta ce" Ka gani kau? Inaga fa Aurena da Dogari zai tabata , ka ga na samu BAC yanzun sauran koyon girki, koyon ruwa, koyon allura da zama Hottest, daga nan Dogarina zai zo inda nake, ka ga ni ba mahaukaciya bace ko" Da mamaki yayan nata take kallonta kafin ya dan janye hannunsa ya ce" Ke tunda kin warware tashi mu je gida, ko in da hali ki ga likitan mahaukata kafin mu bar nan din, ke yanzu ina hadin samun Bac dinki da wani aljaninki wai shi dogari? Kai in ba dan ba da na ce Dogarin nan naki ya ci ......" Da sauri ta mike daga zaunen da take a saman gado ta kai hannunta ta rufe masa baki ranta ya soma baci , yannayi na tsiwar da ra watsar kwana da kwanaki ya dawo sabo fil a saman fuskarta ta ce" A sha weekend lafia 11/14/21, 12:43 PM - Allah Akbar: *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)* _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_ *[ T.M.N.A]* https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *DUTSE* RUBUTAWA: *SAJIDA* SADAUKARWA: *GA MASOYANA* LABARINA NA: *10*
Chapter 11 · 0% Book details