Sashe 78
Dutse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_
*[ T.M.N.A]*
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir-rahamanir-rahim_
5
Da matukar farin ciki ta dirko ta karasa kusa da su sosai ta ce" Lah Mah da ranki, dama na san zaki tashi ciwon ba wani bane dan jikinki ai ba zafi, Pah yaushe a gari?"
Pah dake murmushin yar shiriritar yar dake nan haukata masa yaro ya dan kama kuncinta ya ce" Ke da kike jinya ce kika yi barci?"
Muneerath ta yi murmushi tana dan jin kunyar an taba mata kunci ta ce" Pah, gwara ni, ka ga Walahi Hanja kuka ya yi ta shekawa da kyar na lalaba shi ya tashi a nan"
Ido ya kwalalo daga inda yake yana mai karra kallonta, da kallon yadda iyayensa ke dariar abinda ta fada
A ba zata, a yannayi na rashin tsamani wani sansanyan murmushi ya wadaci saman lebensa, wanda ya sauka a kan fuskar Mah dake satar kallonsa tana mai jin dadin irin yadda du yada ya so kin kallonta abin ya gagare shi
A hankali ya kuma juyar da kansa yana shafa sajensa kadan kadan kafin ya taka ya karasa har kusa da su sosai
Muryarsa a rage sosai ya ce" Hutu, likita ya ce hutu take da b
ukata"
Pah ya gyada kansa ya mike yana fadin" Ba zata huta a nan ba sa a turakar mijinta"
Muneerath ta fito daga labewar da ta yi a bayan Pah tunda ta ga ya nufo wajen tana dan murmushi gannin bai kulata ba ta sake abinta ta karasa kusa da gadon ta yayo bargon ta cuimuimuye ta dora a kanta ta yi gaba tana fadin" Sai kun zo Mah bara na je na gyara maki gadon tunda an sake mu"
Gaba dayansu da kallo suka bita cike da sha'awar lamarin yainyar, ko dan a gabansu basu san mutun mai hali irin haka ba?, Irin rayuwarta na matukar saka su nishadi na debe masu kewa na saka su a shauki a koda yaushe, bata da wata damuwa ita sam a rayuwarta, tabas zaku yi mamaki idan har kuka fahimci rayuwa irin ta Muneerath ta zamo abin mangari a wajen sarki na ingila da matarsa, rayuwarta bata fa kowa a saman kanta, bata da kowa a cikin zuciyarta ita din lafiyarta kalau ras take haka take lamarinta ba tare da ta jira wani ba
Tun kafin ta kulewa ganninsu suka cire dubansu a kanta suka dora kan HANJA
Gaba daya hankalinsa da nutsuwarsa sun rakata da kallo ne
Kallo ne mai shige da kamar baya so ta tafi a wajen
Kallo ne kamar wanda zai dawo da ita kar ta yi masa nisa
Yannayin da fuskarsa ta nuna kamar Hanja na son ya dakatar da ita ne
Ba shi ya san halin da yake ciki ba har sai da ta bacewa ganninsa kafin a hankali ya ankara da halin da yake ciki, sai ya samu kansa da kasa juyowa kai tsaye domin bai san yaya iyayen nasa suke ciki ba duba da sun yi shiru ya tabata hankalinsu a kansa ko kuma Pah na taimakawa Mah ta mike
Sai da ya rintse ido yana mai tambayar kansa menene dan Allah ya saka shi bin yarinyar nan da kallo? Me hakan yake nufi? Salon ya janyowa kansa ko?
A hankali ya juyo sai kuwa suka yi ido hudu da Mah wace sunna hada idon ta sakar masa lalausan murmushinta mai sanyaya zukatansu
Sai dai ga mamakinta nan da nan sai ya hade rai yana mai cire kansa ya karasa ya kama dayan hannunta Pah na dayan hannun suka taimaka mata ta idasa mikewa tsaye kamar yadda suke mata kafin su kamo hanya a hankali su nufi kofa fuskar nan tasa a hade shi a dole kar a masa maganar bin yarinyar nan da kallo, koda yake a shiryema yake da basu amsa daidai da tambayarsu, zai fada masu ne haukan yarinyar nan na karra girmama duba fa ta dauki bargo ko me zata yi da shi?
A hankali suke tafia har suka karasa bangaren Mah din
Kasancewar ta ce tana son zuwa ta dauki sako a cen wanda ba wani sako dan dai ta salami yan matanta ne dan ta tabata sunna cen din duba da Muneerath ta dauki bargo ta ce zata je ta gyara mata gado
Ai kam sunna nan din, kuma su suka gyara dakin da kansu wanda Iman da kyar ta iya wani kokari a guaran tana kallon yadda Muneerath ke mika injin shara kasan bed tana son sharo dati bayan ba wani dati ko daya yau dinma abinda ya hanna masu gyarawar dan mai wajen bata nan, idan bata nan kuwa ba shiga suke yi ba
Murmushi Mah ta saki a lokacin da Muneerath ta matso tana mata murmushin itama ta ce" Mah me zamu dafa maki?"
A kasan zuciyarsa sai kawai ya samu kansa da mamakin furucinta, wai me za'a dafa , yar dake kona shayi? Ta kona wainar kwai ta ce ta fi vitamine?,
A hankali Mah ta zauna bakin Bed tana mai godiya wa abubuwan kaunarta watau Pah da kuma Hanja
Pah ya ce" Bara na je falona na dawo dan na saka a kimtsa maki komai"
Yana tafia ya yi sauran su hudu a dakin,
Mah na murmushi tana shaa kan Iman dake gefenta tana jikinta sosai tana sauke ajiyar zuciya, Muneerath kuwa tana tsaye a gabanta tana kallonta, Hanja kuma yana cen kusa da mirror dinta yana duduba turarukan dake ajiye kamar wanda hankalinsa na kan hakan bayan gaba daya hankalinsa ba a wajen yake ba a kan su Mah yake
A sanyaye Mah ta ce" My Munee, wannan kayan na fita ne?, Kin ga yadda wandon nan ya maki a jiki kuwa? Ba hula a kanki fa?"
Muneerath da sauri ta bi jikinta da kallo, lokaci daya ta zarro ido tana fadin" La hauli, tashin hankali da a haka naie yawo ko hula babu? Allahnma da ya sa a gaban Hanja ne da Pah, wollah Mah ni du rikicewa na yi da aka ce baki da lafia kuma ina zuwa na tarda shi yana kuka sai ya karra rikitani"
Wannan karron sai ya kasa rikewa, ya juyo ya karaso wajen yana hararanta a dake ya ce" Ke a ina na yi kuka da zaki ringa yadawa cewar ina kuka?"
Iman dake jikin Mah a hankali ta dago dubanta tana kallonsa tare da mamakinsa da ya ki ya daina kokarin kasheta, wai me yarinyar nan ta fita ne da har ta fita samun alfarmomin nan a game da mutumen da ta rayu da sin gannin sakin fuskarsa a gabanta?
Muneerath ta kama baki ta ce" Lah, Ka rantse da Allah ba sai da na rarasheka ba ka daina kukan, ji fa dan ka ga ta tashi ne zaka karyata ni?"
Wata daria ce ta kubcewa Mah lokaci daya tana dafe cikinta tare da dafe kafadar Iman
Da sauri suka nufeta, lokaci daya suka rufun mata a tare suka kai hannayensu gefen kafadarta da nufin rikota dan talaf mata duba da dan tarin da ta dan fara sakamakon dariyar ba zatan da ta sarketa
A hankali idannuwanta suka sauka a kan fari kal din hannunsa dake saman bayan hannunta mai duhun haske wanda ta ji tamkar an dora mata gashin mage ne mai laushi a bayan hannun nata sannan a hankali aka dan murza bayan hannun hakan ya sa gaba daya ta ji gabanta ya fadi
A hankali ta cire duban nata daga kan hannayen nasu ta dan fara kokarin zarewa cikin dabara tare da dago duban nata ta sauke a kansa dan gannin idan tunaninta na baima san ya taba mata hannu ba haka ne
Ido hudun da suka yi, da idannuwansa masu launin ja wa'inda tun tashin hankalin rashin lafiyar na Mah da suka dauki launin har yanzun bai hadu da abinda zai saka su cenza kala ba suka shiga cikin nata masu hasken gaske da kwayar cikinsu masu kala daban da ta mutane sai ta tsinci kanta da bugawar zuciya a karro na biyu wanda shima abinda ya ziyarce shi kennan harma ya shagala da kallonta har sai da ta cire hannun nata da sauri tana kallon yadda Iman ke mikowa Mah ruwa tana mata sannu ita kuwa tana nuna ba komai fa
Gaba data rasa me zata yi ta yi,baki daya daburcewa ta yi ta rikice hakan ya sa da sauri ta juya tana fadin " Mah bara na dauko hijab "
Hannunsa na hagu ke rike da Mah dinsa, ya rintse idannuwansa yana jin yadda yake fitar da numfashi tamkar mai ciwon huka
A hankali ya bude duban nasa ya kurawa hannunsa ido, wannan tabawa da ya mata itace tabawa ta farko da ya yi mata ba da niyar fada ba
A gaskiya bai san me yake damunsa ba, abinda ya fi ajiyewa a kasan zuciyarsa shine Bashi da lafia
Gaba daya jikinsa sai ya mutu Iman kuwa Muneerath na tafia itama ta bar wajen, dama karfin zamanta dan ta ga Muneerath din ne a yanzu da bata nan bata isa ta yi dogon zama a wajen da yake zaune ba, shi kuwa bai bar wajen ba har sai da Pah ya dawo ya dauki matarsa ya yi bangarensa da abinsa yana ta riritata tamkwar kwai
11/14/21, 12:52 PM - Allah Akbar:
*DUTSE*
RUBUTAWA: *SAJIDA*
SADAUKARWA: *GA MASOYANA*
LABARINA NA: *10*